Page 19
Washegari tun safe nake kiran ta ba ta d'auka, jikina ya yi sanyi, tsoro da fargaba suka cika zuciyata, haka na yi wunin ranar duk a sanyaye, sai da daddare ta kira ni, na dauka gabana yana faduwa, bayan mun gaisa na ce"Khairi don Allah kar wannan ya zama silar rabuwar mu, wallahi ina son ki, idan kika aure ni za ki iya canza ni, ki mai da ni duk yadda kike so na kasance, son ki ne ya nakasa ni, rashin ki ne ya haddasa mini masifar, kuma auren ki ne kawai zai iya wanke komai, ki yi jahadi ki aure ni, ko da kin tsane ni, wallahi zan jure k'iyayyar ki, da horon ki matuk'ar dai kina gidana matsayin matata, komai zan fada miki yanzu ba lallai ki yarda ba, tun da tsohon mijinki ya dasa miki wani miki, amma da za ki ba ni aron dama, ta hanyar manta ko ni wane, da bak'ar halayyata, ki aure ni a hakan, da zan ba ki mamaki, za mu zauna lafiya, mu yi rayuwa mai inganci, wallahi zan gyaru!".
Ta ce"gaskiya ina tsoron namiji mai neman mata, saboda dole matar shi tana cikin had'ari, sannan ba za ta tab'a ganin komai daidai daga wurin shi ba...".
Da narkakkiyar murya kamar zan yi kuka, na ce"wallahi da gaske zan daina Khairi, daga wunin yau ni Saifullahi na yi rantsuwar na daina bin mata, har abada! Ko da kuwa ba ki amince kin aure ni ba".
Ta ce"hmmm! Rantsuwar mane mini mata, kamar ta 'yan siyasa nake kallon ta, tun da na karanta littafin ZAI GYARU!".
Na sauke numfashi na ce"don Allah Khairi ki yarda, ni ban san ma me zan ce miki ba, sai an yi auren za ki gane kawai!".
Ta ce"Yau da asuba Baba ya yi mini zancen, ya ce idan na amince zan aure ka shi ba shi da matsala,ina son ka, don haka na yarda zan aure ka, da sharad'in duk ranar da na gano ba ka daina ba, wallahi ba zan sake kwana a gidanka ba! Don haka ya ce za ka iya turowa ko cikin satin nan ne".
Wani sanyi ya fara kewaya zuciyata, na lumshe ido, ina jin kamar har an d'aura auren, ina murmushi na ce"na gode sosai Khairi, kuma in sha Allah ba zan ba ki kunya ba, wallahi na daina wannan halayyar har abada! Dama rashin ki ne, idan na same ki, babu wata mace da za ta burge ni".
Ta yi 'yar dariya, ta ce"Allah ya tabbatar".
Muka yi fira, kafin mu yi sallama. Da daddare na je na samu iyayena da zancen, suka amince, duk da Ummi ban ga alamar ta yi farinciki ba, Abba ya ce cikin satin za su je nema mini aure, na baro gidan ina jin nishad'i a zuciyata.
Tun a daren na sanarwa Nabila, don kar ma ta ji zancen a waje, kuma ba ta nuna wani kishi ba, ta ce Allah ya sanya alkhairi, sai jikina ya yi sanyi, don da gadarata na sanar mata, gudun kar ta kawo mini raini, ashe ita babu kishin ma a ranta.
Cikin satin aka saka ranar aurenmu da Khairi, watanni biyu, wanda na dinga k'irgen su, ina jin su kamar shekaru biyu. Muka samu wata irin shak'uwa da ita, ta yadda har nake jin idan babu ita ba zan iya rayuwa ba, Khairi ta canza mini, ta saki jikina da ni, muna sharb'ar soyayyar mu yadda ya kamata, wata irin rayuwa muka yi a wata biyun nan, mai tsayawa a rai, tarihi mai wuyar mantawa, na gyaru, na bar kula kowace mace, sai matata da take fama da cikin da ba na bi ta kan shi ma, bare na binciki lafiyar shi, soyayyar Khairi kawai na saka a gaba, ba na gane kowane yare sai nata, ba na jin kowane motsi sai nata.
Da k'yar na jure zuwan wata biyun nan, da nake yawan fada mata, shekara biyu ne fa, ba wata biyu ba. Alhamdulillah burina ya cika, lokaci ya yi, aka d'aura aurena da muradin raina, mafarkina ya tabbata, bayan gwagwaryar rayuwa da na yiz wajan ganin na dawo da ran Mataccen burina, a ranar jin zuciyata na yi kamar ana wanke ta da ruwan k'ank'ara, da daddare aka lullub'o kyakkyawar amaryata aka kawo ta gidana ina ganin komai kamar a irin mafarkan da na saba yi.
Sai da na je gidan Nabila na yi mata sallama, don ba a gida d'aya za su zauna da Khairi ba, hakan na tsara, don a ganina ta haka ne kawai zan iya gudanar da adalci, saboda kar Nabila ta yi ta ganin abin da zai dame ta, ko kuma wata rana Khairi ta ga abin da za ta ji kishi, ko ta ji na yi mata laifi. Kwance ma take ba ta da lafiya, jikinta zafi rau, kuma ta ce min ta fi sati tana yi, nan na ce ta tabbatar ta sha magani, ban ma san akwai magani a gidan ko babu ba, ni dai na hanzarta na bar ta, don kar Khairi ta yi fushi da ni.
Da sallama na shiga d'akin da take, tana zaune fuskarta lullub'e da mayafi, k'afata har rawa take yi, hannuna yana karkarwa na k'arasa inda take, na bud'e fuskarta da wani murmushi a fuskata mai wuyar misaltawa, sai ta saka hannayenta ta rufe fuskar, tana murmushi, na bi zanen jan lallen hannunta da kallo, ina murmushi, na janyo ta jikina, har lokacin ban yarda ba mafarkina nake yi ba, ganin mun jima a hakan, ba ni da niyyar farkawa, sai na tabbatar yau fa da gaske Khairin ce tare da ni, ba ta cikin mafarki ba.
"Alhamdulillah!" Na furta, ina sauke ajiyar zuciya.
Ta sake lafewa a jikina, har na yi zaton bacci ta fara yi, na d'ago fuskarta ina kallo, kamar ranar na fara ganinta, na ce"ki ce wani abu mana, ki fad'a mini yau ba mafarki nake yi ba, Khairi ina cikin fari cikin da ya fi k'arfin baki ya furta shi".
"Zan so ka furta na ji". Ta fad'a tana sake rik'e ni.
Na ce"ki kalli k'wayar idona, ita za ta sanar miki komai, sannan ki auna farin cikin da kike ji a zuciyarki, sai ki rib'anya shi sau dubu, to irin farin cikin da nake ciki kenan!".
Sai ta yi 'yar siririyar dariyarta, mai saka ni a shauki.
Da na umarce ta, ta tashi mu yi sallar godiya ga Allah, sai ta sanar mini yau d'in ba ta da tsarki, haka na yi tawa, na godewa Allah, tare da neman yafiyar shi bisa zunubai na, na baya, ina kudurce na tuba har abada, Allah gafurur-rahim ne, tun da ya cika mini burina, duk da sab'a masa da na yi a baya, haka muka kwana cikin farin ciki, ni kam baccin nawa rabi da rabi ne, idan na ya fara d'aukata, sai na tuna Khairi ce fa a jikina yau, ba cikin mafarki ba, sai zuciyata ta fara azalzala, na sake k'ank'ameta har sai ta farka, cikin shagwab'ar ta sai ta ce mini bacci take ji, ko ta ce don Allah na bari, a haka har aka kira sallar asuba a kunnena.
Wannan daren ya shiga k'arshen kundin tarihin rayuwata, wanda sai mutuwa kad'ai ce za ta mantar da ni shi, duk da idan na tuna shi, ba k'aramin mawuyacin hali nake shiga ba.
Na wayi gari cikin wani irin shaukin da na jima ban ji ba, wani wasai nake jin raina, kamar ba ni da sauran damuwa a raina. Kana taka Allah na ta shi, ta Allah ita ce gaskiya, ban taba zaton wannan ranar za ta zama ranar k'arshe ta farin cikin rayuwata ba, a tunanina ita ce ranar da zan manta da duk wani k'uncin rayuwa, ashe ita za ta zama, ranar da zan fara sanin ainahin wane ne ni, a ranar zan gane duk wani k'unci da na shiga a baya na rashin Khairi, sharar fage ne, yanzu ne zan fara karatun.
Da safe Nabila ta kira ni, ta ce za ta koma asibiti wurin awo, dama ko zuwan farkon ba ni na kai ta ba, don haka na ce mata ta dawo lafiya.
Ina nan lik'e da Khairi har shad'aya na rana, don fir na k'i fita daga gidan, na ce sai idan bak'i ne suka zo. Ina ta yi mata fira, da tsara mata yadda rayuwarmu za ta kasance, ita kuma tana dariyarta mai burge ni, wani abun kuma idan na fad'a ta rufe fuska, ko da za ta ba ni amsa, kwatsam! Sai ga kiran Nabila, sai da gabana ya fad'i, saboda ba na son Khairi ta ji kishi, na kalle ta na ce"kin ga 'yar'uwarki Nabila tana kira na, dama ta ce mini za ta je asibiti, bari na amsa kiran".
"Ina gaishe ta" Ta fad'a da murmushi.
Ni ma na yi mata murmushin, na fita harabar gidan.
"Ya aka yi?" Na tambaye ta, bayan na d'aga kiran.
Ta ce"wai sun ce ka zo!".
Na ce"kamar ya na zo? Su wa kenan?"
Ta ce"a asibitin".
Na ce"wata matsalar ce da cikin, me ya faru?"
Ta ce"ina jin, to ka zo d'in mana!".
Ta fada mini asibitin da take, ba don raina ya so ba, na yi wa Khairi sallama, na tafi ina ra k'unk'uni, ni kad'ai. Ina zuwa wata nurse ta raka mu ofishin wani likita, nan ya fara yi mini tambayar watan mu nawa da aure, mun tab'a rashin lafiyar da ta hadar da zazzab'i mai tsanani, ko ciwon mak'oshi, gyambo, k'uraje a fata, gudawa mai muni, yawan ciwon kai, yawon kasala ba tare da dalili ba, gumi musamman da daddare, ko da ba lokacin zafi ba...
Bai gama lissafin ba na katse shi, saboda na gaji, na matsu ya fad'a mini dalilin kiran nawa.
"Sorry doctor! Sauri nake yi, don Allah mene ne yake damun ta?" Na fad'a ina nuna masa Nabila.
Ya cire glass ya ajiye, ya ce"abun ba na sauri ba ne! Don haka ka gyara zama, wancen zuwan da matarka ta yi, bayan mun d'auki jininta mun yi gwaji, bisa k'a'ida, kamar yadda ake yi wa kowa, sai muka tarar tana d'auke da cuta mai karya garkuwar jiki, wato H I V, to na tambaye ta ko tana da wani ciwon ne na musamman ta ce babu, don haka na ce a zo da kai, don mu gwada ka, sai mu gano inda matsalar take".
Wani irin bugu k'irjina ya dinga yi, kamar zai fashe, zuciyata ta fito, na kalli Nabila, na ga ita ma ba ta cikin hayyacinta, sai zazzare ido take yi, ta dafe k'irji.
Na yi k'arfin halin furta"doctor! Ka tabbata ba ku yi mistake wurin gwajin ba?"
Ya ce"harkar gwaji muna takatsantsan sosai! Amma don kauda kokonto, idan kun shirya za a sake yin wani, har kai ma sai a gwada ka".
"A gwada!" Na fad'a jikina yana karkarwa.
Nabila kuma ta fara kuka, na yi mata wani kallo bayan mun d'auki hanyar da za ta sada mu da inda za a d'auki jinin, na ce"Nabila tsakanin ki da Allah wannan Abdul din shi kad'ai kika bawa kanki?"
Sai ta yi mini wani kallo mai kama da harara, ba ta ce komai ba.
Tsakanin d'aukar jinin, da fitowar sakamakon Allah kad'ai ya san kalar gumurzun yak'in da aka zabga, a zuciyata, jin komai nake yi kamar a mafarki, na saka wannan, na warware, a haka har aka sake kiran mu ofishin likitan, ban san cewar a baya ban san me ake nufi da tashin hankali ba, har sai da aka tabbatar mini, sakamakona da na Nabila duka positive, ma'ana dai muna d'auke da cutar mu duka, ina kallon lokacin da Nabila ta sulale, ta zube a wurin, to ba ni da kuzarin motsawa bare na tare ta, a ranar na gane wani abun ya fi gaban kwatance, don ban san ainahin abin da zan ce ina ji ba, Allah ne kad'ai ya sani, sai dai idona a bushe yake ba, don kuka ma ya san tsarar sa.
Gado suka bawa Nabila, don haka dole na daure na kira Ummi a waya, na sanar mata muna asibiti, babu jimawa kuwa ta zo, hankalinta ya tashi ganin yanayi na, musamman da na kasa furta mata ko kalma d'aya, zuciyata sai zugi take yi mini, kamar ana dandak'ata, sai likitan ne ya yi mata bayanin halin da muke ciki.
Ita ma kad'an ya rage ta fad'i, ta yi zaman dab'aro tana dafe k'irjinta, sai a lokacin na yi jarumtar hadiye wani kasu daga bak'in cikin da yake neman zautar da ni, na k'arasa kusa da ita, kamar na ce mata ga ni ki kashe ni, sai ta shiga wanka mini mari, babu k'akkautawa, ina dai jin saukar hannunta a fuskata, don tsananin da nake ciki, ba zai bari na ji zafin marin ba, sai da aka zo aka janye ni sannan Ummi ta dawo cikin hayyacin ta, sai kuma ta fara zagina, tana fad'in, na cuci Nabila, sai Allah ya saka mata, kuma na rubutu mata takardarta yanzun nan, kafin ta farka.
So nake na ba ta hakuri, amma na kasa bud'e baki, saboda nauyin da ya yi mini, kamar an saka mini dutse, haka na sulale na baje a k'asa, ina fitar da wani zazzafan numfashi, don hawayen sun k'i ba ni hadin kai, wai su zuba, ko zan ji sassauci a zuciyata.
Ina cikin wannan halin ne kuma wayata ta yi k'ara, na ciro ta a hankali, sai na ga Khairi ce mai kiran, nan tashin hankalin ya lunku, da na tuna bai zama lallai ta zauna da ni ba, duk irin son da take yi mini, na kasa d'aga kiran, wata nadama ta rufe ni, sai na dinga fatan ina ma mutuwa ta d'auke ni a daren jiya. [12/21, 1:31 PM] Sadiya Abdulrazak: *MATACCEN BURI!*
BY *SADIYA ABDULRAZAK*
*FIRST CLASS WRITER'S*
MARUBUCIYAR; Matar Shige Alhakin So Zai Gyaru
*Sadaukarwa ga Mrs Sadauki*💕