Page 20
Abba ya zo, da iyayen Nabila, a lokacin ta farka, tana ta gurzar kuka ana rarrashin ta, ni kam ina daga gefe, zuciyata da gangar jikina kamar ba nawa ba, ganin har azhar ta yi, muna nan, kuma babu mai kallo na sai kawai na koma gida.
Ina shiga na tarar da Khairi ta sha adon da ya kara tsorata ni, na fara jin ba zan bari ta rabu da ni ba, duk abin da zai faru. Ta tare ni tana tambayata ya jikin Nabila, na saka ta a jikina ina jin ina ma mutuwa ta dauke ni a wannan yanayin, na huta ganin rayuwar kuncin da take tunkaro ni.
Muryata na rawa na ce"Khairi! Don Allah kar ki bar ni, ki yi mini alk'awarin zama da ni har abada, ni kuma na yi miki alk'awarin farin ciki, zan ba ki gatan da babu wata mace da taba samu daga wurin mijinta, ba zan taba fushi da ke ba, ko da za ki dinga yankar naman jikina, har na mutu, kar ki bar ni don Allah!"
Ta ce"wannan alk'awarin ai na yi maka shi tun tuni, mijina na san kai mai so na ne, kuma ko ba ka furta ba na san za ka kyautata mini daidai gwargwado, don haka ka daina tunanin Khairinka za ta bar ka, har abada!".
"Wancen alk'awarin ya ruguje Khairi! Babu shi, wani sabo za ki yi mini, hakan ne kawai zai tabbatar mini da son da kike yi mini". Sai kukan da nake ta fata tun d'azu ya kufce mini, na rik'e ta sosai ina jin kamar ba ni da wani sauran gata a duniya sai nata.
Ta dago tana kallo na, ta ce"me kuma ya faru? Kawai ka fad'a mini".
Na runtse ido, ina jin kamar kar na sanar mata mu ci gaba da zaman mu, sai na nisanta da ita, amma ganin kamar ba zai boyu ba sai na yanke fada mata din, da yakinin za ta tausaya mini ta zauna da ni a yadda nake. Na tsagaita da kukan na ce"Khairi daga asibiti nake, wurin awo ciki jinin Nabila ya nuna tana d'auke da H I V, shi ne kiran da suka yi mini, don tabbatarwa, to ni ma ana gwada nawan ya nuna ina da cutar..."
Yadda ta firfito da ido waje da alamun tashin hankali ne, ya tsorata ni, har na kasa karasawa.
"Da gaske kake!" Ta tambaye ni muryarta tana rawa.
Na ruk'o hannunta na ce"a da na yi zaton rasa ki ne k'addarata, ashe zan same Ki, kaddarar kuma tana nan tafe, sai dai Khairi ba na fatan wannan k'addarar ta raba mu, rayuwata idan babu ke akwai matsala, don Allah kar hakan ya sa ki guje ni, zan zauna da ke, sai mu dinga nisa da juna ta wannan fannin".
"Don Allah ki yi mini wannan alfarmar!" Na fad'a hawaye wani na hankado wani.
Sai ta fara kuka sosai, ni ma gudun hawayen suka k'aru. Ta ce"me ya sa ka yi wa rayuwarka irin wannan illar? Me ya sa ba ka d'auki k'addarar rashi na ba, tun farko? Me yasa ba ka yi addu'a ba, ka jira lokacin da Allah zai dube mu? Wace irin rayuwar aure kake so mu yi, idan ban rabu da kai ba? Zaman mu ya k'are"
Sai ta rushe da kuka.
Na ruk'o ta, ni ma kukan nawa ya tsananta, na ce"A'a Khairi! Za mu iya zama a hakan, akwai wasu dabarun kariya, kuma wallahi da ace ke ce kika gamu da wannan k'addarar da zan iya sadaukarwa na aure ki, ki yi tunani, zama da mai son ka, ya fi zama da mai baka".
Sai ta fizge, ta tashi ta shige d'aki, ta kulle, bayan na gama cin kukana da jinyar zuciyata sai na tashi na je d'akin na dinga bugawa ta k'i budewa, haka na ja kafa na shiga d'akina, da la'asar ina ji ta yi bak'i, ta fito, bayan sun tafi sai ta shigo d'akina, ta ce na fito na ci abinci, na kalli idanunta da suka kumbura suka yi ja, alamar ta ci kuka, na ce"Khairi a haka kika bari bak'i suka gan ki? Zo nan!".
Ba ta kula ni ba, ta fice daga d'akin, ni ma ban fito ba har aka kira sallar magriba, na tashi na gabatar, na koma na kwanta, babu jimawa kuma sai ga kiran Abba, ya ce mini yana kofar gida.
Na taso na bud'e, gabana yayi mummunar faduwa, ganin tare da mahaifin Khairi suke, da kuma mahaifin Nabila, kunyar duniya ta rufe ni, na ji kamar babu wanda ya kai ni muzanta a duniya, na ba su hanya suka wuce, bayan sun zauna, na gaishe su, sannan na d'aga waya na kira Khairi, ta fito tana share hawaye, ta tsugunna kusa da ni.
Abba ne ya yi jawabi, ya maimaita duk yadda aka yi a asibiti, sannan ya tambaye ni, ko akwai abin da ya shiga tsakanina da Khairi daren jiya? Ina hawaye na ce babu komai, bai yarda ba, sai da ya tambaye ta, ta tabbatar da hakan, mahaifinta jinjina kai kawai yake yi, da alama ya kad'u da jin lamarina, Abba ya ciro biro da takarda a aljihun shi ya mik'o mini, ya ce"Saifullahi, ka raba takardar nan gida biyu, d'aya ka rubuta takardar sallama ga matarka Nabila, d'ayar kuma ka rubuta ta ga Khairi".
Na fara hawaye, gabana yana faduwa, na kasa karb'ar takardar, sai girgiza masa kai da na fara.
Ya wurgo mini, tare da daka mini tsawa, ya ce"mun yanke wannan hukuncin ne, don yi maka sassauci! Ba dan Nabila 'yar'uwarka ba ce, kuma iyayenta sun d'auki k'addara da yau a station za ka kwana, har kotu sai an shiga! Don haka ka sake su su duka, sai ka je ka auri duniya ka zauna da ita, zama na har abada!".
Cikin kuka na ce"Abba cikin su babu wacce zan iya saki, na yi nadama, Nabila ta riga ta shiga k'addarata, rabuwar mu ba mafita ba ce, ga shi har Allah ya kawo rabo a tsakaninmu, ba ni da bakin ba ku hak'uri, Nabila tana so na, zan ba ta hak'uri mu zauna mu rufawa juna asiri. Khairi kuma muna kan tattaunawa, ku ba mu lokaci".
Kaina a k'asa yake, don haka ban san lokacin da Abba ya k'araso inda nake ba, sai saukar wani zazzafan mari na ji a fuskata, ya sake sauke mini wani.
Mahaifin Nabila ya taso ya rik'e shi, ya zaunar, sannan ya kalle ni ya ce"Saifullahi! Ba ka kyautawa rayuwarka ba, ba ka kyautawa k'anwarka ba, Nabila tana cikin wani hali, kuma ta ce ba za ta ci gaba da zama da kai ba, har abada, a yanzu rarrashi take buk'ata, don haka dole mu ni yadda take so, saboda haka ya zama wajibi yanzu na koma da takardarta, idan ya so daga baya, idan ta huce sai ku sasanta a junanku, tun da har rabo ya shiga tsakani".
Hannuna yana rawa, na d'auki biro da takarda, na rubuta saki d'aya ga Nabila, na linke takardar na mika wa mahaifinta, sai Abba ya riga shi karb'a, ya yago inda babu rubutun ya mik'o mini, ya ce"Saura na Ummul-khairi, ka sake ta su koma da mahaifinta yanzun nan!".
Ai kamar ya ce mini saura sakan d'aya Khairi ta mutu, na fashe da kuka, ina girgiza kai na ce"Abba ku yafe mini, don Allah kar ku yi mana haka, muna son junan mu, ko Khairi?"
Na k'arashe maganar ina kallonta, ita ma sai kukanta ya tsananta har tana shid'ewa.
Na karasa na kama k'afar mahaifin Khairi cikin kukan fitar hayyaci na ce"don girman Allah Baba ka saka baki, kar ku yi mini haka, ku je ku yi tambaya, zamu iya rayuwa da Khairi ba tare da ta shafa ba, Wallahi ba zan iya sakin ta ba, mutuwa zan yi".
Na koma wurin Abba na ce"Abba ka manta ni ne? Ni ne fa Saifullahin ka, d'a mafi soyuwa a gare ka, ashe ka shirya rasa ni? Wallahi mutuwa zan yi, ba zan iya sakin Khairi ba". A maimakon ya mini magana, sai ya wanke ni da mari
Na koma wurin ta, na rike hannunta na ce"Khairi kin ji wai raba mu za su yi? Ke za ki yarda ki bar ni? Ni dai mutuwa zan yi, gara kawai su kashe ni, ba zan sake ki ba!"
Abba ya d'akko takardar ya ajiye a gabana, ya ce"Saifullahi kafin na k'irga uku ka saki yarinyar nan, kana b'ata mana lokaci, kuma ka san babu abokin wasan ka a nan wurin!"
Ya koma ya zauna, ya ce"d'aya!"
Na k'ank'ame ta ina jin yadda numfashina yake fita da mugun karfi, kamar tare da raina zai fita.
Mahaifinta ya ce"wannan yaron yana cikin wani hali, Alhaji mu bari ya samu nutsuwa daga baya sai ya sallame ta".
Mahaifin Nabila ya ce"gaskiya ne, ni ma bun ya tsorata ni".
Abba ya ce"ko mutuwa zai yi yau zai sake ta".
"Saifullahi ka saki yarinyar nan! Biyu!" Na tsinci furucin shi sama-sama.
Nan kuma na ji wani abu a k'irjina, kamar zuciyata ce ta dawo mak'oshina, take shirin fitowa ta bakina, sai na kasa jan numfashi, kaina ya fara juyawa, daga nan kuma ban sake sanin abin da yake faruwa ba, sai farkawa na yi gan ni, hancina d'auke da oxygen, nan kuma komai da ya faru ya dawo kaina, zuciyata ta fara bugu, na tashi zaune, na cire oxygen din, ina kiciniyar cire ruwan na ji k'ara ana tab'a band'aki.
Khairi ce ta fito da alama alwala ta yi, don ina jiyi kiran sallar asuba, ta k'araso sai ta fara kuka ba ta ce mini komai ba.
"Me ya kawo ki wurina?" Na tambaye ta.
Ta ce"likita ya ce ni ya kamata na yi jinyar ka, wai ka fara gani na idan ka farka".
Na girgiza mata kai, na ce"Khairi ba ke ya kamata ki yi jinyata ba, ke kashe ni za ki yi, tun da kika zab'i rabuwa da ni, to gara ma ki yi nesa da ni, idan na daina ganin ki zan fi yin jinyar a nutse, kar na yi mutuwar fuj'a".
Ta ce"ba haka ba ne Saifullahi, idan ka duba ka gani babu aure a tsakaninmu, Allah ya ga zuciyata ina son ka, kuma na so rayuwa da kai, wallahi ba dan iyayena sun ji zancen nan ba, da zan iya sadaukarwa na yi rayuwa da kai a yadda kake, to yanzu ba za su yarda ba".
"Ok!" Kawai na furta na kau da kai, ina fitar da huci mai zafi.
Sati d'aya Khairi tana jinya ta, Ummi ba ta tab'a zuwa ba, sai dai k'annaina su kawo mana abin da muke buk'ata, Abba kullum yana zuwa, kuma bai sake yi mini zancen sakin Khairi ba, ita kuma idan na yi mata zancen sai ta fara kuka, don haka na daina, na zubawa sarautar Allah ido, har likitoci suka ce na samu lafiya, aka sallame ni, muka koma gida, sai dai a gidan muka tarar da wasu Malamai, wai mu suke jira ni da Khairi, nan muka zauna suka dinga yi mini wa'azi da nasiha, zantukan hikima, da muhimmancin yarda da k'addara, har na gamsu da jawaban su, ni da Khairi kuka, kamar ranmu zai fita, haka na furta mata saki d'aya, don da na so rubutawa ma, takardar jik'ewa ta yi da hawaye, ina ji ina gani, 'yan'uwanta suka janye ta suka fita da ita, kamar za ta fad'i, duk yadda na so daurewa sai na kasa, na sulale a wurin ina wani irin kuka na fitar hayyaci.
Abba ya so a mai da ni asibiti, sai d'aya daga cikin Malaman ya ce, a bari ya tafi da ni gidan shi, abun nawa addu'a yake buk'ata ba asibiti ba, satina uku a gidan shi, yana kwantar mini da hankali, har da rubutun dangana nake sha, ga addu'o'in da yake koya mini, ina yi babu dare babu rana, Alhamdulillah na samu nutsuwa daidai gwargwado, amma wannan mikin na rashin Khairi ba zai bar zuciyata ba har abada.
Bisa shawarwarin Malamin na fara fafutukar bikon Nabila, a ranar da na je gidansu, sai na ga duk ta canza, ta yi muguwar rama, duk da cikin jikinta, kuma na yarda Nabila masoyiyata ce ta hak'ik'a, don ta tarbe ni babu yabo banu fallasa, ta sanar mini cikin watan shi bakwai, tausayi da kunyarta suka kama ni, na duk'a har k'asa na nemi yafiyarta.
Tana kuka ta ce"Yaya Saifullahi, na yafe maka! Ina son ka, amma idan na ce ban ji ciwon wannan abin da ya faru ba, na yi k'arya, sannan a lokacin da na yi furucin ba zan zauna da kai ba, ba na cikin hayyacin na, Allah ya zab'awa kowannen mu abin da ya fi zama alkhairi ga rayuwar shi".
"Ka daina kuka!" Ban san ma kukan nake yi ba, sai da ta fada
Na kalle ta sai na ga ita ma kukan take yi, na kai hannu na share mata hawayen, na ce"Nabila a da na yi zaton halinki rashin zuciya ne, ashe ba haka ba ne, wata kyakkyawar zuciya ce Allah ya ba ki, wacce duk namijin da ya same ki, ya yi saken da ya rasa ki, ya yi asara, wannan k'addarar mu ce, kuma da ace na san zan saka ki a wannan halin da na rabu da ke, tun tuni, to mutum ba ya tara sani da Allah".
Ta share hawaye, ba ta ce komai ba.
"Nabila!" Na kira sunanta a sanyaye.
Ta kalle ni, ba tare da ta amsa ba.
Na ce"za ki iya yi mini alfarma, ki ba ni dama ta biyu, ta hanyar yarda na maida ki d'akinki? Na yi miki alk'awarin zan gyara kuskurena, zan tattaro so da kulawar duniyar nan na ba ki, za mu yi kalar rayuwar da na so mu yi da Khairi, Nabila ba zan tab'a sab'a miki ba, zan kyautata miki fiye da yadda na yi niyyar kyautata Khairi, tun da na yarda ke ce wacce Allah ya zab'a mini, kuma ni a yanzu zabin da Allah ya yi mini, shi zan karb'a komai d'acin sa".
"Don Allah ki ba ni wannan damar k'anwata!" Na fada jin ta yi shiru.
"Ni na yafe maka, sai dai ka rok'i iyayena!" Ta fad'a muryarta tana rawa.
A ranar na samu Abba da zancen na mai da Nabila, suka je gidan su, tare da amincewarta aka mai da aurenmu, cikin satin ta dawo, sai muka zauna a gidan da na tanada don Khairi, don tuni an kwashe kayanta, a ganina zaman kwana d'aya da muka yi da Khairi a gidan, zai sa na dinga ganin Nabila kamar Khairin.
Na yi iya k'ok'arina, na faranta mata, na koyawa zuciyata mantawa da Khairi, idan muna tare da Nabila, haka rayuwar mu ta fara tafiya a nutse, ina kau da duk wani tunanin Khairi, tun da na san ta yi mini nisa, na dogara da addu'a, da nasihar iyaye da ta 'yan'uwa, na koma kasuwa, ina gudanar da sabuwar rayuwata sannu a hankali, don na lura duk wanda d'auki duniya da zafi shi take k'onawa.
Cikin haka Nabila ta haifi yaranta, 'yan biyu mace da namiji, ba tare da shawarar kowa ba narad'awa macen suna Ummul-khairi, namijin kuma Abdul'aziz, wato sunan tsohon saurayin Nabila wanda ya rasu, sosai nake taya ta kula da yaran muna farin cikin mu daidai damu.
Sai da Khairi da Abdul suka yi shekara d'aya, sannan na samu labarin auren Khairi, na yi mata fatan alkhairi, ina hana zuciyata tada mini da mikin da nake fatan ya zama tarihi.
Yarana suka taso cikin wata irin k'auna ta iyaye, ba ga ni ba, ba ga Nabila ba, don tsakaninmu ba a gane wanda ya fi wani son yaran, rayuwarmu ta ci gaba da gudana, lafiya lau da iyalina, muka rik'i maganin cutar mu, babu ma mai ganin mu ya ce ba mu da lafiya, sai wanda ya sani.
TAMMAT BI HAMDULLAHI!
Nan na kawo k'arshen wannan labarin, inda na yi kuskure Allah ya yafe mini. Kina ganin akwai wata shawarar da ya kamata ki ba ni game da rubutuna? Ko kin gano wani kuskure a cikin labarin? Kofa a bud'e take, za ki iya yi mini magana kai tsaye.
***