Da walakin...

PAGE 1

by @sadiyaabdulrazak954

Tamkar wacce za ta je gasar kyau haka ta caɓa kwalliya da ado, ta shafe ilahirin jikinta da shu'umar humra, wacce take ɗaya daga cikin manyan makamanta dake yi mata jagora wajen tashin kan namiji cikin ƙanƙanin lokaci. A hankali ta fito tana taku cikin yanayin da ke nuna tana fargabar wani ya ganta. Da alama haƙanta bai cim ma ruwa ba, domi kuwa tana ƙarasawa falon ta tarar da matar da take yi wa kallon dodo hakimce a kujera tana latsa waya, kallo ɗaya ta yi mata gabanta ya faɗi, ta ji irin yanayin da takan ji a duk sanda suka haɗa ido, daidai sanda ta zo dab da ita matar ta ce"A shiga a fito dai, don mijina ya fi ƙarfin haɗa jiki da ke wallahi". Ko juyowa ba ta yi ba, don idan da sabo ta saba da jin maganganu makamantan wannan, daga bakin kishiyar tata, kuma sam ba ta iya tanka mata, saboda haka ta wuce, ta tunkari turakar mai gidan nata kai tsaye cike da fargaba da fatan Allah Ya sa yau ɗin ya bawa marar ɗa kunya, ko za ta samu sauƙin ƙasƙancin dake tsakaninta da kishiya.

A hankali ta tura ƙofar ɗakin ta shiga da sallama, Alhaji Shamsu dake kwance ya tashi zaune da sauri, jin wannan kalar bala'in da yakan shiga a duk sanda amaryar tasa ta tunkaro shi ya ziyarce shi, "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!" Ya furta a hankali yana jin gabaɗaya kanshi ya fara juyawa. Salatinsa da yanayin da ta ga ya shiga bai sa ta sare ba, ta yi jarumtar ƙarasawa, ta ajiye mayafinta ta zauna a bakin gadon da yake, ya sauke gwauron numfashi kafin ya ce"Hajara".

Ta amsa da"Na'am Alhaji".

Ya ce"Don Allah ki koma ɗakinki, yanzu ina son hutu ne, saboda kaina yana ciwo sosai".

A raunace ta ce"Allah Ya ba ka lafiya, amma kwanana a ɗakinka ba zai ƙara maka ciwo ba, kamar yadda fitata ba za ta sauke maka ba".

Ya ce"Hakane, to bari na fita na siyo magani na sha". Ya fice da sauri yana waiwayenta cikin kallon da ya yi mata kama da na ƙyama, wanda hakan ya sa ta bi jikinta da kallo, sam ba ta ga wani naƙasu a tare da ita ba, musamman ma yadda ta yi mugun yarda da shu'umar humrar da ta yi wankanta. Duk iya ƙoƙarin da take wurin kau da tunanin mijinta ba gudunta zai fara yi ba, a yau zuciyarta ta gaza, dole ta yarda akwai matsalar da ta shiga tsakaninsu, domin kuwa tun da ya fita bai dawo ba, tun tana ƙirgen mintuna har ta fara na awanni, firgigit ta farka daga baccin da ya sure ta, tana kallon agogo ta ga ƙarfe ɗaya da rabi, har lokacin bai dawo ba, saboda haka ta sakko tsam daga gadon ta fito falo.

Jiki a sanyaye ta zauna a ƙasan kujerar da yake kwance yana bacci a takure tamkar mara gata, ta kai hannu ta tattaɓa ƙafarsa tana cewa"Alhajina".

Ya farka, yana yamutse fuska, sai dai ganinta da kuma warin da ya turnuƙe shi yake shigarsa tun daga ƙofofin hanci har cikinsa ya sa shi wartsakewa, ya tashi zaune da alamun fushi ya ce"Hajara don girman Allah ki rufa min asiri ki tafi ɗakinki ki kwanta, wai ba dai kina zuwar mini ba ne saboda ki ba ni haƙƙina ba? To ni na yafe, ba sai kin zo ba, duk lokacin da na buƙata zan neme ki". Ya miƙe tsaye nesa da ita yana haɗe fuska sosai.

Da rawar murya ta ce"Na ji, amma kar ka manta ni ma ina da haƙƙina a kanka, zan iya neman ka ba ni haƙƙina ko da kai ba ka da muradi, me yasa ku maza kuka ɗauki wannan fannin a matsayin haƙƙinku ku kaɗai? Buƙatarku ita ce buƙata, za ku yi a lokacin da kuke so ko da mace ba ta so, amma idan ba kwa ra'ayi ita ta so sai ƙasƙanci ya biyo baya".

Ya ce"Hajara magana kike yi a kan mace fa, mace ai tana iya saka namiji ya yi abin da bai yi niyya ba ma, amma wacce take da tsafta kuma ta san kanta ciki da waje".

"Kana nufin ni ƙazama ce?" Ta yi masa tambayar tana kallon jikinta, wanda ba ya taɓa rabuwa da ƙamshi.

Ya ce"A haka dai ga ki nan kamar ɗawisu, sai dai kin zame mini tamkar ɓaure, kin ɗauka ado da kwalliya ne kaɗai tsafta? Wallahi idan kika tunkaro ni gabaɗaya nake fita hayyacina, kina cutar da ni".

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Alhaji me kake so ka faɗa mini ne? Ka aure ni ne saboda ka tozarta ni?" Ta yi maganar tare da sakkowar hawayen da ta kasa riƙewa.

Tsaki kawai ya shige ɗakinsa ya banko ƙofa, wacce ta ji kamar a ƙirjinta ya bugata, saboda yadda ta ji ƙirjinta yana barazanar fashewa, jaɓar ta zauna a kujerar ta riƙe baki, zuciyarta tana ɗarsa mata tunani daban-daban. Gabaɗaya sati huɗu kenan da auren nata, sati biyu na farko a gidan ta yi shi da mijinta cikin aminci da nuna ƙauna tare da tsantsar kulawa, amma sai ga shi cikin sati biyu komai ya canza, wanda ta nemi dalilin canjin ta rasa, a da har zumuɗin ranar kwananta yake yi, ko bai faɗa ba ta ga alamar hakan a ayyukansa da idanunsa, amma rana ɗaya ta lura kamar ba ya ma son ganinta. A yadda take ƙishin rayuwar aure dole za ta shawo kan matsalarta, don zaman gidansu ba abu ba ne mai sauƙi, saboda haka ta yanke za ta fito masa a mutum ta nuna masa ita ma tana da ƴancin rayuwa mai inganci tamkar yadda matarsa take yi, da wannan saƙa da warwarar ta kwana, baccinta na ranar dai rabi da rabi ya kasance.

Washegari da sassafe ta shiga kitchen ta fara hada-hadar ɗora girki, ta kusa kammalawa Suwaiba ta shigo tare da yaranta ƴan'mata biyu, kowaccensu ta bi Hajara da wulaƙantaccen kallo, yayinda ita kuma ta sunkuyar da kai, suka shiga aiki tare da mahaifiyarsu, sum-sum ta fice da kayan abincinta ta nufi ɗakin Alhaji.

Fitowar shi daga wanka kenan yana shiryawa, ta shiga da sallama, "Innalilillahi wa inna ilaihi raji'un!" Furucinsa ya datse gaisuwar da ta kwaso, zuciyarta na kumbura ta ajiye kula da plas ɗin shayin, kafin ta yi magana ya ce"Hajara tsakaninki da Allah jiya ya muka yi da ke? Ba na shata miki layi akan shigo mini ɗaki ba?"

"Ka yi haƙuri abinci na kawo maka shiyasa..."

"Hauka nake da zan sake cin abincinki!?" Ya katse ta kamar zai kai mata duka.

Ta lura kullum abun ƙara gaba yake yi, tun da ko jiya ai ya ci abincin, don haka cikin fusata ta ce"Wai Alhaji me na yi maka!? Meyasa kake son kai ni bango? Me na yi maka!?"

Shi ma a fusacen ya ce"Ke jakar ina ce? Ba kya jin irin warin da yake surnanowa daga jikinki? Wannan wace irin ƙazanta ce haka? Na kasa tantance wanka ne ba kya yi ko tsarki ne ba kya yi? Gaskiya ba zan ɓoye miki ba, duk iya jarumtata na yi, na ji ba zan iya zaman mintuna a kusa da ke ba, ba zan iya cin wani abu da kika taɓa ba, Hajara wari kike yi sosai, irin wanda zai iya kumburawa mutum ciki ko ma ya saka masa wata cutar".

Kallon shi kawai take yi, hawaye suna wanke mata fuska, tana buɗe baki za ta yi magana ya ce"Fita! Ki fice na ce! Idan na sake ganinki a ɗakina zan iya yi miki wulaƙanci, wannan ai masifa ce!".

Ta fita da sauri ba tare da ta ɗauke abincin ba, a falo ta tarar da Suwaiba zaune, ta yi mata makirin murmushi tana toshe hanci, wanda hakan ya ɗarsa mata zarginta a zuciyarta.

Ɗakinta ta shiga, ta zauna kuka ya ƙwace mata, tana tunawa da abubuwa da dama, ashe haka wulaƙanci daga wurin miji yake da zafi? Ashe haka makircin kishiya yake da zafi?

"Ya zama dole na nemi mafita, don ba na sha'awar sake wani zawarcin!" Ta faɗawa kanta hakan, tana share hawaye.

Sai wajen ƙarfe goma ta ɗauki wayarta, ta kira shi bai ɗauka ba, ta tura masa saƙon tana so ta je asibiti, ya dawo mata da amsar sai ta dawo. Ta yi wanka ta fito, sai ta ga abincin da ta kai masa a ƙofar ɗakin a ajiye, ta ɗauka ta wuce ta mayar da shi kitchen ɗin, ta fice daga gidan.

Ba asibitin ta nufa ba, domin ta san larurarta ba ta can ba ce, gidan ƙawarta Hafsa ta je, bayan sun gaisa ta ce da ita"Amarya lafiya kuwa na ganki duk a sanyaye?"

Hajara ta ce"Hafsa don Allah da ga shigowata ɗakin nan zuwa yanzu wane kalar ƙamshi kike ji a jikina?"

Hafsa ta ce"Ƙamshin humra kike ta bazawa mana, ke da ƙamshi ai kowa ya san tif da taya kuke, amma me yasa kika tambaye ni?"

Hajara ta ce"Ko kaɗan ba ki ji wari ba?"

Hafsa ta canza fuska zuwa ta mamaki ta ce"Kamar ya? Me yake faruwa ne?"

Hawaye suka sakkowa Hajara ta ce"Hafsa ina cikin matsala! Alhaji wari yake ji a tare da ni, ya kalle ni ya faɗa mini wari nake yi, yanzu ko kusa da shi ba ya so na zo fa, ki duba ki ga fa sati huɗu kacal da auren, zuciyata ciwo take yi sosai".

Hafsa ta yi murmushi tamkar wacce aka bawa labarin farinciki kafin ta ce"Lallai Suwaiba, ashe dai ba a zaune take ba, shiyasa ko tada hankali ba ta yi ba a auren nan, yanzu ya kike so a yi?"

Hajara ta ce"Hafsa ba na so aurena ya mutu wallahi, ban ji daɗin zaman gida ba sam, shekaruna sun fara ja, ya kamata a ce ina zaune a ɗakin mijina duk da a ƙaddarata babu haihuwa, amma auren ma kaɗai ai ni'ima ne".

Hafsa ta ce"Wannan gaskiya ne, amma kin san muddin za ki ɗaura ɗamarar zama da mace irin Suwaiba sai kin dawo layina ko?"

Ta girgiza mata kai da sauri ta ce"A'a, sam ba zan je wurin kowane boka ba in sha Allah! Da na yi wannan kuskuren gara na dawwama a hakan, zan iya jure wannan zaman muddin dai ba zai sake ni ba".

Hafsa ta yi dariya ta ce"Wannan ai zance ne, hauka ake da zai zauna da ke yana cutuwa? Kawai dai ki ce kin shirya sabon zawarci, kuma za ki ta maimaita shi, don idan ma kin fita wani gidan ma za ki tarar da irin matsalar ko ma wacce ta fi ta wannan".

Hajara ta miƙe tsaye ta ce"Hafsa ban zo gidanki saboda ki ci mutuncina ba fa! Allah zai dube ni ya yi mini maganin matsalata, idan har biye-biye kika ɗauka a matsayin makami tabbas rayuwarki tana cikin baƙin duhu".

Daga haka ta fice, tana jin zuciyarta na cunkushewa sakamakon tuno wasu daga cikin abubuwan da suka shuɗe a bahaguwar rayuwarta ta baya. Gidan dai ta koma, saboda ba ta ga inda za ta kai kukanta ba, gani take duk wanda ya ji halin da take ciki dariya zai yi mata, a maimakon tausayawa. Ta yi sallama a ƙofar falon, babu kowa a ciki, sai kayan kitchen ɗinta da ta hango a ƙofar ɗakinta, da mamaki ta ƙarasa tana kallonsu, ta juya ta kalli kitchen ɗin daidai sanda Suwaiba ta fito, duk da tana jin shakkarta amma ta dake ta ce"Wane isasshen ne ya fito min da kayana?"

Ta ƙaraso dab da ita ta ce"Ni isasshiyar ce, bisa umarnin isasshe, wanda ya kwaso ki ya kawo gidan!".Ta yi mata mugun kallo ta shige ɗakinta.

Hajara ta ciro wayarta a jaka ta kira Alhaji hannunta har yana karkarwa saboda ranta ya ɓaci, yana ɗagawa ta ce"Alhaji kai ne ka sa a fitar mini da kayan kitchen?"

Ya ce"E ni ne, saboda ba na son kina taɓa duk wani abu da zan ci, don Allah Hajara ki yi nesa da ni har zuwa lokacin da za ki gyara jikinki!"

Ƙit ya kashe wayar, bai jira cewarta ba. Ta haɗe gira tana auna maganarsa, ta yi nesa da shi? Yana nufin ta bar gidan kenan ko kuma dai ta daina shiga harkar shi? Ta ja ƙafa ta shiga ɗaki, a bakin gadonta ta zauna zuciyarta na zafi, ta na tunanin mafita.

*** [9/5, 9:19 AM] Sadiya Abdulrazak:

WANI KISHIN

*FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION* (Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation.)

Wani Auren Iya Ruwa Matar shige Alhakin So Mukullin Nadama Mataccen buri. Duka za ki same su complete.