Da walakin...

PAGE 6

by @sadiyaabdulrazak954

*BOJUWA HERBAL'S & SCENTS* *Suna kawo Saiwowin sanyi da suke dagargaza sanyin mara da na jijiya.* *Haka nan akwai dafaffen maganin ga wanda tafi son ready made.* *Haka nan suna kawo Saiwowi daban daban daga Chad da Sudan, kuma marasa illah* *Saiwowin tsumi* *Saiwowin dahuwar kaza/tattabaru* *Saiwowin matsi gangariya* *Original gadalin mata* *Ƴaƴan gadali na asali* *Original gumba* *Tsumin Saiwowi* *Tsumin kwakwa da Dabino* *Igiyar alkairi* *Zumar goran tula* *Hakkin daka na musamman na asali* *Bayan haka suna dafa kazar amare da masu jego da ma uwayen gida*. *Akwai bridal package* *Mai jego package* *Ƴar gata package*. *Dukkan kayan kuma available ne for pickup or immediate delivery.* *A Kano nake amma kuma nationwide delivery ne* *Ku tuntubi Surayya Halin yau a wannan lambar dan samun naku cikin musulmin farashi* ***** *Serious buyers pls* *Iyah Basiru na gaisuwa*😅

Da daddare Alhaji yana dawowa Suwaiba ta shiga ɗakinsa, ta aro damuwa ta yafawa fuskarta, wanda hakan ya sa Alhaji tattara hankalinsa a kanta, ya ce"Uwar gida saurautar mata! Lafiya dai na ga yanayinki babu daɗi?" Don a yanzu ita ce ta gaban goshinsa, har lallaɓata yake yi, tun da ita ke ba shi wurin fakewa, kuma mace ce mai rowa a shimfiɗa ta yi ta fankama ko ta fake da hakan ta dinga shigo da buƙatunta na kuɗi marasa dalili, wannan yana ɗaya daga cikin dalilan da ya saka shi ƙara aure, sai kuma ga shi bai yi dacen samun lafiyayyiya ba, shiyasa dole dai ya dawo ɓangaren Suwaibar.

Da alamun damuwa ta ce"Alhaji wani abu na gani yau wanda ya firgita ni, wallahi na so barin maganar a cikina sai na ga yin hakan tamkar cin amanarka ne, ba zan so a ce da saka hannuna a cutar da wani ba ballantana kuma mijina, bango abun jinginata na ji sanyi ni da iyalina".

Alhaji Shamsu ya ce"Tafi kai tsaye Madam, me kike so ki ce ne?"

Ta sauke ajiyar zuciya tana gyara, sannan ta ce"Alhaji ba na son shiga tsakaninka da matarka, ka ga dai sam ƙarin aurenka bai dame ni ba, tun da ban ga ta inda ka tauye mini haƙƙi ba, saboda haka ban ga dalilin da zai saka amaryarka ta tsone mini ido ba".

Cikin ƙaguwa ya ce"Ai duk na san wannan, na yarda da kyakkyawar zuciyarki".

Ta ce"To Alhaji dama cikin kwana biyun nan ne na lura kullum sai Hajara ta ci kwalliya ta fita, ni na yi zaton ma ko biki suke yi a danginsu, sai kuma na lura duk ranar kwananta sai ta jiƙa zobo ta a kofi ta shiga da shi ɗakinta, ban kawo komai ba don a zatona sha take, yau ta fita tun safe, lokacin na aiki Saudat, da ta dawo take ce mini ta ga Anti Hajara ta shiga motar wani a bakin titi sun tafi".

"Motar wani!?" Alhaji ya tambaya a zabure.

Suwaiba ta ce"Kai kuwa Alhaji ina ba ka kana roƙo, to ai ba wannan ba ne abun mamaki, bayan ta dawo da yamma ina kitchen, ita kuma ta zo shiga na lura ba ta san ina ciki ba, sai na ji tana cewa wallahi kullum da zoɓon nake amfani, kuma har yanzu bai gane ba, shi da jikina ai sun yi sallama, to na ga da ta shigo ta ganni ta firgita".

Alhaji ya ja numfashi ya fesar da huci mai zafi.

Suwaiba ta ce"Sai duk jikina ya yi sanyi, tun da ta zo gidan nan nake ta ƙoƙarin janta a jiki amma ganin ba ta sake da ni ba sai ma kallon raini da take yi min, sai na jingine ta gefe, tun da ka ga ba sa'ata ba ce, kar raini ya shigo ciki".

Ya ce"Hakane".

Ta ce"To sai na yi nufin na je na ba ta shawara mu kashe mu binne kar wanda ya ji ko ya gani, na so na ce mata ta bar wannan hanyar ko mace ba ta da aure wannan ba mutuncinta ba ne,na yi sallama a ƙofar ɗakinta shiru ba ta amsa ba, na tura na ji ƙofar a rufe, amma sai na ji tana ta kiran sunanka, na yi zaton ko waya take yi da kai, na kira ka na ji ta shiga ka ɗauka".

Ya ce"Shi ne kiran da kika yi mini kenan ɗazu kika ce mistake kika yi?" Ta gyaɗa kai alamar haka ne.

Sannan ta ɗora,"To zuciyata sai ta kasa nutsuwa, shiyasa na zagaya ta baya na leƙa don na ga abin da take yi". Ta fara matsar ƙwalla ta ce"Hajara na gani baje a tsakar ɗakinta da wata roba a gabanta da ruwa a ciki, ga wasu ganyayyaki da wasu duwatsu, kana yi musu kallo ɗaya dai za ka gane kayan sihiri ne, babban abun tsoron ta kafa kai a ruwan tana ta kiran sunanka, Alhaji ina tsoron ta kassara mini kai, yau idan ta mallake ka ragamar gidan nan ta koma hannunta ai na san shan ruwana a gidan ya ƙare, ta kaɗa ni waje ta mayar da ƴaƴana marayun ƙarfin da yaji" Tana kai wa nan ta fashe da kuka.

Sosai hankalin Alhaji ya tashi, ga wani tsoro da ya shige shi, ya tashi da sauri zai fita, Suwaiba ta ruƙo hannun shi, ta ce"Ina za ka je?"

Ya ce"Zuwa zan yi na sawaƙe mata mana, wannan ai babbar annoba ce a gidan nan!".

Suwaiba ta girgiza kai ta ce"A'a idan ka sake ta a yanzu ba ka da hujjar furtawa ballantana nunawa, idan ka ce ta wurina ka san wannan babu wanda zai yarda, tun da ni kishiyarta ce, kuma kai ne kawai kake da tabbaci a kan zuciyata ban da sauran mutanen gari, saboda haka ina ba ka shawarar ka tsaya ka kamata da hujja dumu-dumu kafin ka zartar".

Ya ce"To wace hujja zan jira!? Ai ba zan iya bari yau yarinyar nan ta kwana a gidan nan ba".

Suwaiba ta ce"A'a Alhaji, mu bi komai a sannu, gaggawa aikin shaiɗan ne, ka yi haƙuri gobe ka dawo a sace, idan ta kwashi kayan aikinta ta shiga sai mu je ka ritsa ta".

A fusace ya jawo lokar gadonsa ya ɗakko biro da littafi ya yagi takarda ya yi rubutu, Suwaiba kamar za ta yi kuka ta ce"Yanzu Alhaji ba za ka dubi hanzarina ba? Ashe ban kai na ba ka shawara ka ɗauka ba?"

Ya ce"Ai na ɗauka, na dai rubuta ne kawai, saboda goben ba sai na ɓata lokaci ba!". Ya saka takardar a lokar, har ya yi hanyar fita sai kuma ya dawo ya zauna yana huci.

Suwaiba ta fita ta kawo masa abinci, tana yin komai a sanyaye, sai tausarsa take yi, cike da makirci.

Yayin da Hajara ta kwana ranta fess don ba ta taɓa zaton akwai wata matsala da take shirin tunkararta ba, haka ma Suwaiba ta kwana da farincikin sanin gobe warhaka sunan Hajara sakakkiya, tana gidansu ta fara lissafin iddarta, ta shiga sabuwar rayuwar ƙunci, shi kuwa Alhaji a nashi ɓangaren bacci rabi da rabi ya yi, har ya ƙagauta goben ta yi, don ya ga zahiri, sosai yake nadamar ƙara aure, sam bai taɓa zaton haka Hajara take ba, sosai ya yi mamakin wai ashe duk jinin da take faɗa har ma da nuna tana cikin damuwa ƙarya take yi, har ta san ta jiƙa zoɓo saboda ta nuna masa shaida ko da ya nuna bai yarda ba, duk iya tunaninsa ya kasa gano me ya yi mata da ta yi masa haka, me take nema a wurin mazan waje, kuma sannan ta san ba ta son shi me yasa ta amince ta aure shi?

Washegarin ma ji ya yi kamar kar ya tafi kasuwa, sai da Suwaiba ta lallaɓa shi ya tafi, suka tsaya a kan sha biyu tana yi zai dawo. Hakan kuwa aka yi, sha biyu da mintuna ya dawo gidan, ya shiga ɗakinsa a sace ba tare da Hajara ta sani ba, Suwaiba da ke hakimce a falo tun safe ta kafa ta tsare ko sallar azhar ba ta tashi ta yi ba, har ƙarfe huɗu da rabi ta yi, sai a lokacin Hajara ta fito, don ta yi amfani da maganinta, ta yi wa Suwaiba kallo ɗaya ta shiga kitchen ta ɗakko robar da take amfani da ita, da kofi ta koma ɗakin.

Alhaji dake zaune cikin zullumi sai gani ya yi Suwaiba ta shigo ta kama hannun shi, suka zagaya bayan ɗakin Hajara, tar suke kallonta ta windo, suna kallon lokacin da ta ɗakko Qur'ani, haka ma ganyen magaryar da ta ɗakko Alhaji ya gane shi, sai ya tuna shekarun baya da mahaifin shi Malam yake raye, duk ranar juma'a sai ya zaunar da su ya yi musu makamancin wannan abun da take shirin yi, da sunan rigakafin karya sihiri, kuma ya fara gasgatawa a sanda ya ji tana karanto irin ayoyin da har yau bai manta da su ba, sam bai ji ta ambaci sunan shi ba, har ta gama ta fara shafawa a jikinta.

Jiki a sanyaye ya ja Suwaiba gefe ya ce"Wannan ai rigakafin karya sihiri take yi".

"Ko dai yin sihirin ba!" Suwaiba ta faɗa tana yi masa wani kallo.

Ya ce"Mu je zan yi bincike tukunna". Ta yi gaba yayin da shi kuma ya tsaya yana amsa kira, kamar kububuwa haka ta shiga ɗakinsa ta buɗe lokar ta ɗakko takardar jiya ta nufi ɗakin Hajara cikin sauri. Yadda ta banko ƙofar ya saka Hajara ɗagowa a zabure, Suwaiba ta jefa mata takardar ta ce"To matsiyaciya yau ne ƙarshen shan ruwanki a gidan nan! Sai ki fara lissafin kwanakin iddarki, ki fara yi wa kanki tanadin yadda za ki sarrafa sabuwar rayuwarki ta ƙunci".

Da sauri Hajara ta buɗe takardar ƙirjinta yana bugawa, _Ni Alhaji Shamsu na saki matata Hajara saki uku_ Abin da ta gani kenan a takardar, ta tashi tsaye zuciyarta kamar za ta faso ƙirjinta, ta kasa furta ko da kalma ɗaya, daidai nan Alhaji ya shigo ɗakin yana yi wa Suwaiba kallon tuhuma.

*FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATION* (Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation.)

WANI AUREN IYA RUWA MATAR SHIGE ALHAKIN SO MATACCEN BURI MUKULLIN NADAMA DUKA ZA KU SAME SU COMPLETE ***