PAGE 1
Zaune yake dirshan a gaban iyayensa, zuciyarsa fal ƙunci, Allah ne kaɗai ya san yanayin da yake ciki a daidai wannan lokacin, a sanyaye ya ce"Don Allah Mama ki taimaka mini mu tafi ɗin, wallahi ba na so na tafi na bar Aisha ita kaɗai, ga ciki a jikinta".
Mama da take a fusace ta kalli mahaifin Abba wanda ya kasance makaho ta ce"Oh! Ashe rashin ido ma rahama ne, wallahi mara ido ya huta da ganin wani takaicin".
Baba ya zabura yana cewa"Kamar ya? Wannan wace irin magana ce haka Saratu?"
Ta ce"To Malam idan ban ce haka ba me zan ce? Ka ga fa Abba ya yi zaman dirshan a gabana ya ƙi tashi yana neman butulce mana ya ƙi bin umarninmu saboda mace, wannan wace irin baƙar rana ce?"
Baba ya ce"To ke ma Saratu ki sallama shi mana ki rabu da shi su tafi..."
Da sauri ta katse shi da faɗin"Au haka ma za ka ce!? To su tafi, Abba tashi ku tafi, kai idan sun tafin wane ne a ruwa? Duka fa saboda kai nake yin wannan yaƙin, wallahi bari ka ji na faɗa maka, idan yaron nan ya ɗauki wannan yarinyar mai suffar munafukai suka bar garin nan abincin da za mu saka a bakin salati ma sai ya gagare mu, kai dai na tabbata sai dai ka koma bara a danja".
"Subhanallah! Wannan wane irin nemawa kai alkaba'ir ne? Ni ɗin ne zan yi bara?" Baba ya faɗa a fusace.
Mama ta ce"Idan ka ji bara ɗaya kenan, to a tunaninka idan ya saka ƙafa ya bar garin nan zai ci gaba da ciyar da mu ne?"
Abba ya sako musu baki da faɗin"Wallahi Mama babu wani abu da zan rage cikin abin da nake yi muku, wannan tafiyar ba za ta rage komai ba, sai dai ma ƙarin wasu alkairan in sha Allah!".
Baba da tun da ya ji batun bara hankalinsa ya tashi, ya fara laluben sandarsa ya ce"Ina Abba? Ina kake?"
Ba tare da ya kalle shi ba murya a cushe ya ce"Ga ni".
Sai ji ya yi ral, Baba ya rafka masa sandar a kafaɗa, ya ɗaga zai ƙara masa ya yi saurin matsawa gefe, zuciyarsa na ƙuna kamar ya yi kuka.
Baba ya ce"Kana ina? Kana hauka ne da za ka ɗauki matarka ka tafi da ita can uwa duniya? Kenan sai ka manta da mu ta zama ita ce uwarka ita ce ubanka".
Mama ta ce"Kuma wallahi Malam gabaɗaya sai ta ɗaiɗaita shi ta kashe masa zuciya, ya za a yi ya ɗauki yarinya ya tafi da ita wajen aiki? Kai da za ka yi aiki ka nemi halak ina ruwanka da mace? Salon duk abin da ka samu ta handime?"
Baba ya ƙara da faɗin"Haba Abbati, me zai haɗa ka da mace kai da za ka tafi wajen aiki? To wallahi ni dai da na yi bara a danja har gara ma a ce na san ba ka raye, idan har sai ka tafi da yarinyar nan to kuwa sai dai ka fasa tafiyar".
Maganarsa ta ƙarshe ta fusata Mama, ta yi masa wani shashashan kallo ta ce"Kamar ya ya zauna?"
Abba ya ce"E Mama ni kawai na haƙura da tafiyar nan, ya za mu yi ta kwan gaba kwan baya? Da kin haƙura mu tafi yanzu kuma kin mayar da bara bana, gaskiya ni na fasa, zan zauna na ci gaba da sana'ata a nan, tun da ban rasa komai ba, ai dai arziƙi na Allah ne".
Mama ta ce"Lallai wuyanka ya isa yanka, yau ni kake sa'insa da ni saboda mace? Macen ma wacce ba sonka take yi ba dole aka yi mata take zaune da kai? To shinkenan, ni ba zan zauna ina ja inja da kai ba, zan ba ka zaɓi guda biyu, ko dai ka ɗauko Aisha a yau da tsummokaranta ta shiga ɗakin can ta zauna, ko kuma ka sake ta!".
Kalmar saki ta daki zuciyarsa, ya ɗago da sauri ya kalli Mama, ta jinjina masa kai ta ce"Wallahi da gaske nake yi, kuma ka sani tafiyarka babu fashi! Don haka muddin ka ce ba za ta zauna a gidan nan ba, sai dai ka sake ta!".
Ya ce"Don Allah ku yi haƙuri, shikenan za ta dawo nan ɗin, Allah Ya sa hakan shi ya fi alkhairi". Ya tashi ya fita saboda kar ma a tsawaita zancen sakin, zuciyarsa babu daɗi ya kama hanyar komawa gidan shi kamar mara laka.
Aisha tana cikin kitchen, tana ta kai da kawowa cike da karsashi tana yin aiki, ta ɗauki wannan ta ajiye wannan, halayyar Aisha ce wannan indai aka ce gobe za ta yi balaguro to ba ta taɓa samun kanta, ta yi ta zumuɗi kenan da shirye-shiye, musamman wannan tafiyar da ta zame mata ta musamman wacce za ta yi ta tare da mijinta, don haka yau ranta fess.
Sallamar shi ce ta saka ta sakin murmushi tana amsawa da ɗan ɗaga murya don ta fahimtar da shi inda take, kuma ta san ya fahimta, amma ga mamakinta sai ta ga bai shigo kitchen ɗin ba, ya wuce ɗaki, ta tsame cincin ɗin da take soyawa daga cikin mai, ta zuba a faranti ta ɗauki ruwa ta nufi ɗakin fuskarta ɗauke da murmushi ta shiga da sallama, sai dai ganin shi a kwance da kuma yanayin fuskarsa ya karantar da ita ba lafiya lau ba, a ajiye kayan hannunta ta zauna gefen gadon tana cewa"Sannu da zuwa, shi ne ka zo ka shige ni ko?"
Shirun da ya yi mata ne ya ƙara tabbatar mata da hasashenta, nan take jikinta ya yi sanyi ta ce"Abba ba ka da lafiya ne?"
Ya sauke numfashi ya ce"Lafiyata ƙalau".
Ta ce"Na ganka duk a sanyaye".
Ya ce"Ba komai je ki ci gaba da aikinki".
Ta ce"To, ga cincin ka ci ka ji yadda ya yi".
Ta yi maganar tana miƙa masa farantin, ya karɓa ba tare da ya ci ba, ita kuma ta fita ta koma kitchen ɗin, wajen sha biyu na safe ta kammala komai ta dawo ɗaki, ta fara ciro kayansu tana sakawa a cikin akwati, jiki a sanyaye yake kallonta yana tunanin ta inda zai fara faɗa mata mahaifiyarsa ta haramta tafiyar nan tare da ita. Tashi ya yi zaune ya ce"Amm...Aisha ina ga ki dakata da haɗa kayan nan haka fa, ki saka iya nawa".
Gabanta ya ba da rass, ta juyo a sanyaye ta ce"Me yasa? Na yi zaton kun gama magana da Mama".
Ya ce"Da saura, da dai an gama to yau da na je gaishe ta, ta ce mini kar ma ki haɗa kayanki, anjima za ta zo gidan".
Wani yawu mai tauri ta haɗiya har ƙwalla ta cika idonta, ta saki rigar hannunta ta fice daga ɗakin cikin sauri, ɗakin kujeru ta shiga ta zauna ta saki kukan da ta yi ƙoƙarin riƙewa a gaban shi, ta rasa me yasa wasu iyayen mijin ba sa yi wa matan ƴaƴan su adalci, mene ne aibu don ya tafi da ita garin da yake yin aiki? Mama ta kasa ba da hujja ɗaya mai ƙarfi wacce za a saka a mizanin hankali a dogara da ita har a yarda ya tafi ya bar matarsa a gida shi ne maslaha a rayuwar aurensu.
A na shi ɓangaren shi ma tunanin da yake yi kenan, duk da ya san dama mahaifiyarsa ba son Aisha take yi ba, amma bai yi zaton za ta hana shi tafiya da ita inda yake aiki ba. Mama irin surukan nan ne masu kishi da matan ƴaƴansu, sam ba ta ƙaunar ta ga ɗanta yana kyautatawa matarsa, tunaninta ɗaya kawai ta mallake shi ta mayar mata da ɗa bawa, gani take yi kamar ɗanta ya zaɓi matarsa akanta ne, shiyasa gabaɗaya surukanta uku babu wacce take jin daɗin rayuwar auren.
Wajen minti biyar da fitarta ya tashi ya bita, tana zaune a kan kujera ta kifa kanta, ta tsaya da kukan tunani kawai take yi mai cike da takaici, da tunanin mafita, domin ta saka a ranta ba za ta taɓa bin maganar da Maman ta tsara ba, wai shi ya tafi aikinsa ita kuma ta tattaro kayanta ta koma gidan Maman ta zauna, idan ya samu lokaci ya zo hutu sai ta koma gidanta, sam Mama ba surukar da za ku zauna a waje ɗaya ba ce, kuna nesa ma ba ta barka ka huta ba ballantana ka je gidanta da zama?
Zama ya yi a gefen kujerar yana kiran sunanta, ba ta ɗago ba kuma ba ta amsa ba, ya ce"Aisha ki yi haƙuri..."
Ta ce"Na haƙura, na ji Abba ka tafi, amma wallahi ba zan zauna a gidanku ba, muddin ba a gidan nan zan zauna ba to sai dai a yi ɗaya cikin biyu, ko dai ka tafi da ni dole ko kuma a yi uwar watsi kowa ya kama gabansa".
Ta faɗa, ba don maganar ta kai har zuciyarta ba, domin ta san mutuwar aurenta a wannan ƙadamin ba ƙaramin tonon asiri ba ne a gare ta, ta kashe aurenta ta je ina? Ta tauna tsakuwa ne kawai don aya ta ji tsoro, tun da ta san babu kalmar da ta fi saurin saka mijinta shiga taitayinsa kamar ta rabuwarsu. Ta yi nasara, domin kuwa alamun firgici ne ya bayyana ƙarara a yanayinsa duk da ya sani dama can ba shi ne zaɓinta ba, amma ya yi mamakin jin kalmar rabuwar a daidai wannan lokacin, saboda a ƴan watannin nan ta sauke kwandon ƙiyayyarsa da ta ɗorawa kanta, zamansu ya daidaita, har ma ya fara tunanin ta manta da komai, za ta zauna da shi har abada.
"Aisha ni kike faɗawa haka? Haka za ki ce mini? Ki tausaya mini mana da wanne zan ji? Kenan ba zan samu sanyi ta wajenki ba?" Ya ƙarasa maganar a sanyaye.
Ta ce"Ai ba ka nemi sanyin ba, ta ya zan fara rayuwa a gidanku? To idan ma ba za ta bari ka tafi da ni ba, sai a bar ni a gidana".
Ya ce"A gaskiya ni ma ba na son zamanki a gidan nan ke kaɗai, saboda yanayin tsaro, sannan ko ba wannan ba zuciyata ba za ta iya jure a ce matata tana zaune ita kaɗai a gida ba, gaskiya ba zan samu nutsuwa ba".
Ta ce"Saboda kana zargina ko?"
Ya ce"Ni ban zarge ki ba, amma kin san sharrin shaiɗan, shiyasa maganin kar a yi kar a fara".
Ta ce"To Abba ka sake ni mana..."
Ya ɗaga mata hannu da sauri, cikin ɓacin rai ya ce"Kar ki sake faɗar kalmar nan, saboda ba zan sake ki ba har abada!".
Daga haka ya tashi ya fice daga gidan, ita kuma ta fara kuka, tana gwada sa'arta ne kawai saboda ya ƙyale ta ta zauna a gidan aurenta, domin ta san idan ya sake ta ɗin tana cikin garari, da aurenta ya mutu har gara ta yi zaman gidan Maman.
GIDAN SHAMSU
Tun daga ƙofar gida za ka iya jiyo hayaniya da sautin kiɗan da yake tashi a cikin wani madaidaicin gida. Ƴan mata ne manya da ƙanana da ƙananun zawarawa suka kunna waƙar suke raƙashewa da sunan training ɗin rawar da za a yi a ranar bikin ɗaya daga cikinsu, wanda ya rage sati ɗaya rak.
Ummi ita ce matar gidan, wato uwar daba, tana zaune a kujerar tsakar gida riƙe da rediyon da suke jin sauti, tana kallon su tana ɓaɓɓaka dariya ranta fari ƙal, ƙaramar yarinya ce wacce ba za ta wuce shekara ashirin da biyu ba, wasu daga cikin jama'ar tata duk sun girme ta. Ummi irin yaran nan ne wanda tun tasowarsu ba sa jin magana, tana da rawar kai sosai, ga kule-kulen maza, sanda ta zama buduruwa sai ta so ta fara shashanci da biyewa samari ƴan nanaye, ita ce bin maza shoppin ita ce yawan zuwa paty, samarinta babu adadi yara da manya, saboda baiwar kyau da Allah Ya ba ta, tana da kyaun da yake fizgar maza cikin ƙanƙanin lokaci, ga zaƙin murya kamar gyare, uwa-uba kuma rawar kai da rashin kamun kai, idan ka ganta ta fito ta ci kwalliya sai ka ce buduruwa ce, musamman idan ta shiga cikin marasa auren kusan ta fi kowa zaƙewa da nuna ita ce wayayyiya.
Daidai gwagwado iyayenta sun yi ƙoƙari a kan tarbiyyarta, amma abun nata kullum ƙara ta'azzara yake yi, don haka suka ga gara kawai su yi mata aure su huta, tana ajin kusa da ƙarshe a sakandiri aka cire ta aka yi mata auren dole, Shamsu ɗan'uwanta ne, da mahaifinsa da mahaifiyarta wa da ƙanwa ne, tun tana ƙarama ya nuna yana sonta, har ta girma bai fasa binta ba, duk kuwa da halayenta na rawar kai, da rashin mutunci a gare shi, don babu tudu da gangaren da ba su hau ba, amma ya ce ya ji ya gani, zai zauna da ita a duk yadda take matuƙar dai za ta zauna a gidan auren, ai da ƙuruciya a lamarinta, watarana sai labari.
To da aka yi auren ma haka ya ci gaba da jurewa, ya ji ya ƙi ji, ya gani ya ƙi gani, duk don ta haƙura ta zauna, yana ganin idan ta fara haihuwa za ta yi hankalin da ake ta fata. Tun farkon auren take shige-shigen maƙota, dayake unguwar da aka kaita tsohuwar unguwa ce mai cike da ƴan mata da ƙananun zawarawa, kuma sun lura da amarya ƴar sharholiya ce sai suka mayar da gidan dandali, tun suna cewa gidan amarya har ta canzawa gidanta suna ya zama dabar mata.
Yawanci yaran da suke shiga su ma irinta ne marasa kamun kai, da farko Shamsu ya so taka mata burki amma ganin za ta botsare masa sai ya ƙyale ta, yana dai saka ido a kan shige da ficenta.
Adaidaita sahu yake ja, shi ne sana'arsa, amma a ransa ba shi da burin da ya wuce aikin soja, sau biyu yana yin traning ba ya yin nasara, yanzu kuma bayan auren ya samu wani a cikin danginsa ya yi masa hanyar da ake kyautata zaton zai samu aikin, ya gama shiryawa don tafiya garin da za su yi training ɗin, amma a ransa yana jin wasu-wasin tafiya ya bar Ummi ita kaɗai a gida.
Don haka yau ya zaunar da ita ya ce"Ummi yanzu kina ganin za ki iya kwana ke kaɗai a gidan nan babu ni".
Ta ce"To me zai hana? Ba sai na nemi ƴan tayin kwana ba?"
Ya ce"Ni dai a ganina gara kawai ki koma gida, ko gidanmu ko naku duk ɗaya ne, idan ya so cikin ƙannena sai na samu wanda zai zo ya dinga kwana a gidan, ya jire mana kafin na dawo ko?"
Nan take ta murtuke fuska, ta fara tunanin wannan ma ai rainin hankali ne, ta ya ita da take murnar samun ƴancin damar cin karenta babu babbaka sanadin aure, kuma a ce ta koma gida ta zauna har lokacin da ba ta ma san tsayinsa ba?
Ta ce"Gaskiya ni dai Shamsu ban yarda da wannan maganar ba, ta ya zan koma gida da aurena? Maza nawa ne suke yin tafiya su bar matansu a gida? Wasu ma ba ƙasar amma matan suna nan a ɗakunansu, sai dai kawai su dinga aiko musu da kuɗin abinci, ballantana kai da za ka je traning ɗin da ba a da tabbacin ma za ka haye?" Ta ƙasara tana turo baki, tare da kai da kai.
Ya ce"Yanzu Ummi ba za ki yi mini fata na gari ba, sai ki ce babu tabbacin hayewata?"
Ta ce"Wannan bai dame ni ba, ni dai babu inda zan je gaskiya".
Ya ce"To shikenan, dama ni na yi tunanin ba za ki iya zama ke kaɗai ba, tun da dai za ki iya shikenan".
Ta ce"To me zai hana ni zama? Kai dai kawai ka tabbatar ka ajiye mini kayan buƙatar da za su ishe ni har ka dawo".
Ya ce"Zan ƙoƙarta in sha Allah!".
GIDAN HABIBU
Mata da miji ne zaune a ɗaki, shi ya kalli gabas ita ta kalli arewa, kowannensu fuska babu annuri, kallo ɗaya za ka gane ba abu mai daɗi suke tattaunawa ba, cikin jaddadawa Halima ta ce"Baban Islam da ma ka daina ɓata bakinka, don ni wallahi ba zan kwashi ƴaƴana mata na bi ka kudu ba, yadda tarbiyya ta zama sai addu'a yara suna gida ma Arewa cikin yare da addininsu sun lalace ballantana an kwashe su an kai su inda babu tarbiyya? Duk inda za ka tafi neman kuɗinka ka je, Allah Ya ba da arziƙi mai amfani, amma wallahi da na kwashi yarana mata na bi ka tarbiyyarsu ta lalace a bar ni da sallallami har gara ma auren ya mutu, na koma gidanmu na kama sana'a na dinga kula da su".
Habibu ya haɗiyi wani yawu mai ɗaci, tun sanda ya kawo maganar tafiyar nan tasu rashin lafiya ya yi ƙaura a gidan, shi a ganinsa ya saka iyalinsa a gaba su tafi duk inda zai je shi ne mafi alkhairi, musamman da ya kasance shi mutum ne mai yawan buƙatuwa, sam ba ya jure nisa da matarsa, shiyasa ya fi so a ce sun tafi taren.
Cikin tausasa murya ya ce"Halima kin kasa fahimtata..."
Ta katse shi da faɗin"Ni fa ba zan fahimce ka ba, saboda haka ka adana kalamanka".
Daga haka ta nemi waje ta kwanta tana ci gaba da mita"Haka kawai ina bacci ka tashe ni da zance mata toshe".
Habibu ya kalli jakar kayansa wacce ya haɗa ta, sai jiran tafiya gobe da asuba in sha Allah, amma yanzu jikinsa ya yi sanyi har yana jin gwiwarsa ta sare da tafiyar.
*** ***
*RANAR KUKA!*
BY
*SADIYA ABDULRAZAƘ*
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR Sandar dukanuwargida Zuciyar mace Miji goma... Iya ruwa... Wani auren Matar shige... Da walakin Wutar ƙaiƙayi Alhakin so ***