PAGE 2
GIDAN ABBA
Ta daɗe cikin wani yanayi, kafin ta ɗakko wayarta ta kira lambar mahaifiyarta, tun suna gaisawa uwar ta fahimci ƴar tata ba lafiya take ba, a sanyaye ta ce"Aisha lafiya? Na ji muryarki kamar kina kuka".
Aisha ta ja hanci wani sabon hawayen yana sakko mata sannan ta zayyanewa mahaifiyarta komai da ya faru.
Ta ɗora da faɗin"Gaskiya Umma ba zan iya zaman gidan mahaifiyarsa ba, saboda ba sona take ba".
Umma ta ce"To idan ba ki zauna ba ya za ki yi? Ko so kike ki yi silar kashe aurenki a samu abun faɗa a gari? Tukunna ma idan kika bari aurenki ya mutu Aisha ina za ki je ki zauna? Mahaifinki dai kin ga ba aure ne da shi ba, yana zaune shi kaɗai a gida, zargin da ake yi ma..."
Sai ta yi shiru ta kasa ƙarasawa, a ƙoƙarinta na son ganin ba ta yi furucin da zai zubar da ƙimar uba a idon ƴarsa ba, sai dai ta makara, domin Aishan ta san komai game da halayyar mahaifinta, abun duniya ba ya ɓuya, yau ko haƙa rami ka yi ka binne abu akwai ranar da wani zai iya tono shi ko da kuwa bayan ranka ne kuwa, tun da mahaifinta ya saki mahaifiyarta shikenan bai yi wani auren ba, kuma yake kawai matan banza gidan, har ma da yara ƴan talla, a yanzu haka har abin da yake aikatawa ya fara baza gari, musamman da ya kasance tsohuwar unguwa ce mai cike da jama'a, kuma ko ba haka ba ta san ko an bar batun addini a al'adance ma ta yi ƙanƙantar zama a gida daga ita sai mahaifinta, a dai wannan zamanin mai cike da ruɗu da abubuwan al'ajabi na ban mamaki.
A ɓangaren mahaifiyarta ita ma tunaninta kenan, sannan ta san ba bai yiwuwa ba ne a ce ta ɗakko bazawarar ƴarta ta kawo gidan da ta yi sabon aure, domin ba gidan daɗi ba ne, ta yi auren ne kawai don kar ta zauna haka, ta rasa abin da za ta saka a cikinta ma, shiyasa ta auri wani mutumi mai mata biyu, ɗaki ɗaya ne da ita a cikin gidan ɗan ƙarami, sannan abinci ma ba wani wadata ya yi ba, kuma sam ba ta ga alamar zai iya riƙe mata ƴarta ba, ba za ma ta fara ba, tun da tana kallon yadda suke tataɓurza da matansa a kan sauke haƙƙin ƴaƴansu, ballantana kuma wanda ba shi ya haifa ba a gola, ga shi matansa sun ɗauki kishi da ita sun ɗorawa kansu, saboda ita yanzu take amarya suna ganin ita ce tauraruwa a zuciyar miji, to ina ƴarta bazawara wacce ta wuce zaman gida za ta samu wajen zama?
Cikin damuwa ta ce"Komai ya yi farko zai yi ƙarshe Aisha, ki daure don Allah ki riƙe aurenki, ki yi zamanki a ɗakinki, duk yadda mahaifiyarsa ta tsara ki daure ki bi, babu abin da yake dawwama sai ikon Allah".
Aisha ta share hawaye ta ce"To shikenan Umma, zan koma ɗin".
Ta ce"Allah Ya miki albarka, Ya ba ki ikon jurewa, zan taya ki da addu'a".
Daga haka suka yi sallama, sai ta ɗan ji dama-dama a ranta, ta yi alwala ta yi sallah, ta daɗe a sallayar tana roƙon Allah Ya kawo mata mafita, ya ba su zaman lafiya a zaman da za ta yi da surukar tata, shi kuma mijinta Allah Ya kai shi lafiya, ya ba shi abin da yake nema, sannan ta tashi ta zuba abinci ta ci, ta gama ta koma ɗaki ta mayar da kayanta cikin sif ɗin ta ci gaba da harkokinta.
Bayan la'asar sai ga Mama ta zo gidan, Aisha tana ganinta gabanta ya faɗi, ta daure ta gaishe ta da guntun murmushin da za a kira shi da yaƙe, Mama ta amsa tana haɗe fuska Aisha ta ce"Mama ki shiga mana".
Mama ta ce"Ni ba sai na shiga ba, daga nan ma ya isa, na ce yaron nan ya faɗa miki ba za a yi tafiyar nan da ke ba?"
Ta ce"E ya faɗa mini".
Ta ce"Au ai na ɗauka bai sanar da ke ba, to dama zuwa na yi na jaddada miki, wannan tafiyar ba za ta yiwu da ke ba gaskiya, saboda wasu dalilai".
Aisha ta ce"Babu komai Mama, Allah Ya sa hakan ya zama alkhairi".
Ta ce"Alkhairi ne ma, sai ki haɗa kayanki, anjima zai rako ki".
Daga haka ta fice daga gidan tana jin sauƙi a zuciyarta, don ta kasa sukuni a kan wannan tafiyar da yake so ya yi da matarsa.
Bai dawo gidan ba sai dare, saboda ya bari zuciyarta ta yi sanyi, musamman da ya ji Mama ta je gidan, yana fargabar abin da ta je ta faɗa mata, sanda ya shigo tana zaune a falo, ya zauna ta yi masa sannu, ya ce"Aisha ya garin?"
Ta ce"Hmm! Kai za a tambaya".
Ya ce"Yanzu shikenan gobe iyansu ina can cikin kaɗaici?"
Ta ce"To ya za a yi? Sai dai ka jure".
Ya ce"A gaskiya zan yi kewarki sosai, sai nake ji a jikina kamar zan shiga wani tashin hankali sosai, saboda..."
Ta katse shi da faɗin"Don Allah ya isa, kar ka ƙarasa, me yasa za ka yi wannan mugun fatan? Kai da za ka yi tafiyar mota? Idan ba za ka faɗi alkairi ba ka yi shiru kawai".
Kafin ya yi magana wayarsa ta fara riging, ya duba ya ga Mama ce, kawai sai zuciya ta raya masa ina ma yana ɗagawa ya ji ta ce ta janye ta haƙura su tafi taren, amma yana ɗagawa sai ya sare saboda jin maganar Maman tana cewa"Wai Abba me kake nufi ne? Na ji shiru ba ka kawo ta ba".
Ya ce"Sallama muke yi, sai goben sai ta taho".
Ta ce"Sallama? Tun yaushe kuka san da tafiyar da ba ku yi sallamar ba sai yanzu? Ka san dai da asuba motarku za ta tashi ko?"
Ya ce"Na sani, kuma ma ai ba dole sai na rako ta ba, ko bayan na tafi za ta taho ita kaɗai".
Ƙwalla ta cika idon Aisha, sai kawai ta tashi ta bar ɗakin.
Sanda ya gama wayar ma ya ɗan jima kafin ya bi ta, ya same ta kwance a kan gado, ya maze kamar bai san halin da take ciki ba ya ce"Yau abincin ma sai na tambaya? Na ga dai na ƙarshe ne, a daure a ba ni, daga gobe sai ki yi ta hutawa".
Ta sakko ta fita kitchen ɗin ba tare sa ta yi magana ba, ta ɗakki abincin ta kawo masa, za ta koma gadon ta riƙe ta ya ce"Ki zo mu ci".
Ta fizge tana cewa"Ni na ƙoshi".
Ya ce"Don Allah za ki ci ba don ni ba".
Ta ɗauke ƙwallar da ta sakko mata tana cewa"Na ƙoshi".
A raunane ya ce"Aisha wallahi ba ki fi ni shiga ƙunci da damuwa ba, kawai ina daurewa ne saboda na ƙarfafa miki gwiwa kar na ƙara miki damuwa, amma wallahi a yadda nake ji yau da a ce ni kaɗai ne a cikin gidan nan babu ke da babu abin da zai hana ni ɗora hannu a kai na yi ta zabga ihu, ko zan samu sassauci a zuciyata, Aisha ta wajenki fa ya kamata a ce na samu sanyi a daidai wannan lokacin, tafiya ba mutuwa ba ce, in sha Allah zan je lafiya na dawo na same ki lafiya, ba fa ƙasar zan bari ba".
Ba ta ce komai ba, sai gudun hawayenta da ya ƙaru, ya ce"Ina ta tunanin yadda zan yi idan na ji kewarki, duk da dai ga waya zan kira ki, za mu yi chart, amma wata kulawar ba ta yiwuwa ta waya".
Ya yi huci mai zafi ya ce"Zan yi iya ƙoƙarina don ganin ba daure na riƙe mutuncina, in sha Allah babu wata mace da zan gani a duniyar nan na yi sha'awarta bayan ke, zan riƙe kaina in sha Allah, zan dinga haɗawa sa azumi. Ina da tabbas a kanki, na san kina da mutunci kuma ke ma za ki iya jurewa ki riƙe mini mutuncinki, gangar jikinmu ce kawai za ta yi nisa da juna, amma zuciyoyinmu suna kusa da juna in sha Allah".
Ya nisa ya ce"Na gaji da wannan shirun naki, don Allah ki yi magana ko yaya ne, ki ƙarfafa ni, sai sare ni kike yi".
Ta share hawaye ta ce"Allah Ya kai ka lafiya, kuma in sha Allah ni ma zan jure zan riƙe mutuncina, Allah Ya ba mu ikon jurewa bakiɗaya".
Ya amsa da amin, sai ta saki jikinta suka ci abinci, suka yi wanka, suna fira tana ƙarasa gyara masa kayansa a jaka, ta saka masa cincin ɗin da ta yi, suka kwanta suna jin shaukin juna kamar ba su taɓa kasancewa da juna ba sai a yau ɗin, a wajen Abba wannan daren har ya fiye masa daren farkonsu.
Washe gari da asuba kiran sallar farko abokan tafiyarsa suka fara kiran wayarsa domin yi masa tuni, bai wani samu bacci ba sai dab da asubar amma haka ya tashi ya yi wanka ya shirya, Aisha ma ta tashi ta zauna tana binsa da kallo jiki a sanyaye kamar ta ga sabuwar halitta, ya tafi masallaci, ya yi sallah, kafin ya dawo kiran Mama biyar, Aishan tana kallo ta ƙi ɗauka, yana dawowa suka ƙara sallama a gurguje ya ɗauki kuɗi ya ba ta, yana ƙara ba ta haƙurin zama da Mama, sannan ya tafi da ƙyar, yana waiwayenta, yana fita ta kwanta ta fashe da kuka sosai.
GIDAN SHAMSU
Sam zuciyarsa ba ta nutsu da ya tafi ya bar Ummi ita kaɗai a gidan ba, amma babu yadda zai yi, haka ya haƙura saboda a zauna lafiya, ana gobe zai tafi ya ce ta shirya su je gida, gidan iyayenta suka fara zuwa, ya sanar da su gobe ne tafiyarsa, mahaifiyarta ta ce"Ashe abun ya zo, to ai ni na yi zaton yarinyar nan gidan nan za ta dawo ta zauna ko can gidan naku kafin ka dawo".
Ummi ta ce"Mama kin san yadda ake sata a unguwar nan kuwa? Ai ba zai yiwu a bar gidan haka babu kowa ba, kuma ma kin ga ai ni ta mutane ce, ga yara nan duk suna shigowa".
Shamsu ta kasa jurewa ya ce"Yawwa don Allah Mama ki yi mata magana a kan shigowar ƴan'matan nan, abun yana yin yawa, sai su taru a gida su yi ta rawa kamar wajen paty, ko kuma na dawo na ga suna zance a ƙofar gida, ko ita ma ta fito su jeru a ƙofar gida ana zaman majalisa sai ta gan ni ta shiga gidan".
Yana direwa Ummi ta ce"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Yanzu sharrin da za ka yi mini kenan?"
Mama ta kai mata duka, ra kauce, cikin ƙufula ta ce"Mijin naji ne yake yi miki sharri? Ashe ba ki da kirki! Oh ni dai zan ga ranar da za ki yi hankali".
Ta turo baki tana cewa"Allah Mama ya yi ƙarin gishiri, na san dai suna shigowa, kuma mutum ai rahama ne, ni fa su ne ma suke ƙarfafa mini gwiwa a zaman auren nan, ba zai yiwu na zauna rufe a gida ni kaɗai kamar mayya ba gaskiya".
Mama ta ce"Idan mijinki ya ce haka ai dole ki bi!".
Shamsu ya ce"Shi kenan Mama su ci gaba da shigowar, amma dai ni fargabata kar wataran rigima ta ɓarke a tsakaninsu, a zo ana cewa a gidana ne, kin san sha'anin mata".
Mama ta ce"Gaskiya ne".
Sannan ta kalli Ummi ta ce"Ummi ki nutsu fa ki san kin girma, gaskiya dole ki rage tara yara a gidanki, wannan sam bai dace ba, ke ba kya ma tsoron wata ta ƙwace miki miji a cikinsu? Yaran yanzu da suke jin kamar su lashe namiji".
A ransa ya ce'Musamman yadda take wasarairai da ni'.
Ummi ta yi wata guntuwar dariya ta rainin hankali ta na kallon shi ta ce"Wannan za a ƙwace? Lallai" Sai ta ƙara yin dariya, don ita a ganinta babu wani abun so a tare da shi wanda zai ruɗi mace har ta ce za ta yi ƙwacensa.
Nan dai Mama ta yi mata nasiha, shi ma ta yi masa sosai, ta yi masa fatan nasara sannan suka yi sallama suka tafi.
Suna tafe a hanya ya kalle ta, tana ta shan agwalumar da ta ɗakko a gidan Mama ko a jikinta, da takaici, ya ma kasa ce mata komai.
Ita kuwa da ba ta ma lura ba jin sai tafiya suke kamar tumaki babu wata fira yasa ta sakin dariya, sannan ta ce"Wallahi ɗazun nan ba ƙaramar dariya Mama ta ba ni ba, wai sai wata ta ƙwace ka, to ta kai ka ina?"
Ya ce"Yanzu Ummi ko ba ki da aure ya dace a ce kina tafe kina shan abu a titi?"
Ta mayar da ita hijjabinta ta ce"Sorry matsuwa na yi na sha, kai ni da dama rannan Hafsa take cewa kamar ciki ne da ni, wai ta ga sai sheƙi nake yi".
Bai ce komai ba.
Ta ce"Allah kuwa, kuma dama shekaran jiya ne ko jiya? Na ji zuciyata ta tashi kamar zan yi amai, amma dai ban yi ba".
Ya ce"To Allah Ya tabbatar da alkhairi".
Daga haka ta ci gaba da zantukanta, wani ya kula ta wani ta share ta, yana ta kallonta, sosai yake jin sonta a zuciyarsa, babban abin da ya ja hankalinsa ga aurenta shi ne kyaunta, kuma Allah Ya cika masa burinsa shi yasa yake gode masa a kullum, sannan yana kishin wannan kyaun nata sosai, ya ce"Ummi anya ba za ki fara saka niƙab ba kuwa?"
Ta zaro ido ta ce"Niƙab!? Allah Ya kiyaye, sai ka ce wata matar liman? Wallahi kar ma ka fara, ni ba zan iya rayuwa da niƙab ba, masu sakawa ma ina sara musu".
Ya ce"To fase maks fa? Wallahi sai na ga kamar kyaunki kullum ƙaruwa yake yi, kin ga fa duk inda muka wuce kallonki ake yi, ji nake kamar na zagi mutum wallahi, wai don ma an ganmu tare".
Ta ce"Yaya Shamsu kenan, to kuma Allah Ya ba ni kyau sai na butulce masa na dinga ɓoye fuskata?"
Ya yi guntun tsaki a daidai sanda suka ƙarasa gidan iyayensa ya ce"Ke dai ba za ki girma ba".
Da sallama suka shiga, Umma ta tare su da fara'arta tana yi musu sannu da zuwa, sosai take shiga farinciki idan ta ga ɗanta a kusa da Ummi, saboda ta fi kowa sanin yadda yake son yarinyar, ta gane cewa Ummi ce nutsuwarsa, ita kuwa tana son farincikinta ɗanta, saboda shi ne nutsuwarta ita ma, shi ne yake ɗukar rabin nauyin gidan nasu, kuma shi ne ɗa namiji tilo da Allah Ya ba ta, ga shi mai hankali sa biyayya.
Bayan sun zauna sun gaisa ya ce"Ga ta nan, faɗa na kawo ta ki yi mata".
Ummi ta ce"Faɗa kuma? Me na yi maka wanda ba ka faɗa mini ba tun a gida, sannan muka baro gidan Mama ba ka faɗa ba sai yanzu da aka zo gaban Umma za ka nuna kai ne kaɗai ɗanta".
Umma ta ce"A'a nasiha ake cewa, idan ka ce faɗa kenan wani laifin ta aikata, kuma Ummi ai ke ce ƴata ba shi ba".
Ya yi dariya ya ce"To nasiha".
Sun jima a gidan, har aka kira sallar magriba ya tafi masallaci, ita kuma ta tashi ta yi alwala, a nan suka ci abincin dare sannan suka tafi.
Suna zaune yana saka kayansa a jaka yake cewa"Ke na ga fa ranki fes yake".
Ta ce"To me aka yi mini da zan yi ƙunci?"
Ya ce"Kenan ba za ki yi kewata ba ko?"
Ta ce"Ni fa waje ɗaya nake tausayawa maka a traning ɗin nan, an ce akwai wani hawan igiya da kuke yi, kuma wai kuna yi ana dukanku, zan so na ga yadda za ta kaya da kai" Ta kwashe da dariya.
Ya yi murmushi ya ce"Wallahi wannan shashancin da kike yi ya girmi shekarunki, ko ƴar sha shida ai sai haka, ni fa zancen kewata nake yi miki".
Ta ce"To da ni kaɗai zan zauna a gidan ne ai zan ji kewarka".
Ya tsaya yana kallonta na ƴan sakanni, kafin ya ce"Ni da ƙawayenki ɗaya ne? Kenan Ummi ba za ki yi kewar kwanan da muke yi a gado ɗaya ba?"
Sarai ta gane manufarsa, amma ta yi dariya ta ce"To ai da Safna za mu dinga kwana a gadon".
Nan take ransa ya ɓaci ya ce"Kar ki sake! Kar ki sake ki kawo mini wata yarinya makwancina, idan ba za ta kwana a falo ba, to kuwa sai dai ki kwana ke kaɗai, ko ki bi ta falon ku kwana, wai ke sam ba kya kishina ne?"
Ta ce"To ji ka yi na ce mu kwana mu uku da kai a gadon?"
Ya ce"Ko kwanciya ta yi a makwancina ko ta ɗora a kai a fulona ai ya kamata ki yi kishi".
Ta taɓe baki ta ce"Sai ka ce masifa?"
Haka dai suka yi ta maganganu kafin su kwanta.
Washegari ƙarfe tara na safe ya tafi, bayan sun yi sallama ya ajiye mata komai na buƙata kuma ya ba ta kuɗin cefane.
GIDAN HABIBU
Washegari Halima tana ta zuba idon ta ga ta inda zai fara shirin tafiya, ta ga ba shi da alama, sam ba son tafiyar tashi take yi ba, don dai ya zama dole ne kawai, rayuwar ta yi tsada, ƴar buga-bugar da yake yi a samu a rufawa kai asiri yanzu abin da ake samu ba ya isa a yi komai a wadace, saboda komai ya ninka kuɗinsa, ta san sarai Habibu yana da yawan buƙata, amma ganin yana da kamewa da mutunci shiyasa hakan bai wani dame ta ba, a cewarta idan ya matsu sai ya dawo, hatta mahaifiyarta sai da ta jaddada mata kar ta sake ta kwashi yaranta ta kai su kudu, tarbiyyarsu ta ɓalɓalce, don haka ta yi tsayuwar gwamen jaki a kan ƙin bin shi.
Ganin har ƙarfe tara yana kwance, yara sun tafi makaranta sai ta zo ɗakin ta ce"Baban Islam kar fa abincinka ya sandare a kula, wai ni ka fasa tafiyar ne?"
Ya ce"Tafiya kam ba za ta fasu ba, tun da zaman garin ta ƙi, amma Halima don Allah ki ƙara tunani kafin na tafin, ita ba tarbiyya ta Allah ce, wallahi mu iyaye gwadawa kawai muke yi, a ko'ina akwai na gari akwai akasin haka, yaran nan za mu iya ɗora su a kan tafarkin daga makaranta sai gida, kuma a can ma akwai islamiyya, Hausawa nawa ne suke rayuwa a can? Abokaina nawa ne a can da matansu da ƴaƴansu? Kin ga sai yaran su ƙulla ƙawance da su, babu abin da zai faru in sha Allah".
Halima ta ce"Hmm! Ni fa ba zan fahimta ba, gara ma ka hutar da bakinka, ka gan ni nan, babu abin da na tsana kamar auren nesa, shi yasa tun farko na ƙi auren wanda ba ɗan garin nan ba, sai yanzu kuma na tara yara na kwashe su har su biyar na bi ka? Ai su ma an tauye su ta fannin karatunsu, su yi gantalin canjin makaranta".
Ya ce"To shikenan, tun da dai na ga ba za ki fahimta ba Halima na haƙura zan tafi, sai dai ki sani idan Allah Ya hore mini zan yi wani auren na auri wacce za mu tafi can ɗin".
Takaici ya kama ta saboda maganar ƙarin aure, ta yi murmushin da ya fi kuka ciwo ta ce"A haf! Ai dama maza duka haka halinku yake, wannan har wani abun mamaki ne? Ai mata mun saba ganin wannan, mace ta zauna da ku tsayin shekaru tana bauta muku, ba ku da komai sai wahala, mace ta jeme ta mokaɗe tare da ku, amma idan kuka samu buɗi sai ku ce kun wuce ajinta, ku je ku auro wacce ba a sha wuya da ita ba, ƙarshe sai ta fi ta gidan jin daɗi".
Ta ɗora da faɗin"Ba aure ba? Don Allah a ɗaura shi a yau ku tafi tare da ita, ni kam zama daram, wallahi ba zan bi ka ko tasha ba!".
Ta ƙarasa tana ficewa daga ɗakin. Ya sakko daga gadon ya yi wanka ya shirya, a da ya bari sai gobe zai tafi, amma maganganunta sun tunzura shi, ya yanke gara ya tafi yau ɗin kawai, ko karyawar bai yi ba, ya ɗauki jakar kayansa ya zo ya same ta a falo, kuɗi ya miƙa mata yana cewa"To Allah Ya ƙaddara saduwarmu, ga wannan sai ki riƙe kafin a ga abin da hali zai yi".
Ta karɓa ta ƙirga kuɗin, dubu biyar ne, sheƙeƙe take yi masa kallon mamaki, ta yi wa kuɗin ruƙon sakainar kashi.
*** ***
*RANAR KUKA!*
BY
*SADIYA ABDULRAZAƘ*
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR Sandar dukan uwargida Zuciyar mace Miji goma... Iya ruwa... Wani auren Matar shige... Da walakin Wutar ƙaiƙayi Alhakin so ***