Ranar kuka

PAGE 3

by @sadiyaabdulrazak954

Ta ce"Habibu! Mene ne wannan? Za ka yi tafiyar da ba a san ranar dawowa ba shi ne za ka ɗauki dubu biyar ka ba ni? Alhalin ka san ko ƙwayar shinkafa babu a gidan nan, wanda za mu ci da rana ma sai an auna!".

Ya ce"To wannan ɗin ma arowa na yi jiya, kuma da zan yi tafiyar ai ban ce miki sai ranar da na dawo zan ba ku wani abu ba, zan dinga turo muku daidai gwargwadon samu".

Ta ce"Yanzu yaushe za ka fara turowa? Gobe ko jibi?"

Ya ce"Ba maganar gobe ko jibi ba ce, ai ya danganta da yadda na samu kaina a can, idan komai ya didaita ba fara aiki ba zan yi jikinri ba, ai na san haƙƙina ne, sai ki taya ni da addu'ar Allah Ya ba ni ikon saukewa".

Ta sauke numfashi ta ce"To amin, Allah Ya tsare hanya".

Ya tafi yana jin kewar iyalinsa na ratsa zuciya da gangar jikinsa.

GIDAN ABBA

Sai azhar Aisha ta tashi ta fara zuba kayanta a akwati, ba ta yi nisa ba ta ji sallamar ƴaƴan ƙanwar Abba, suka shigo suka gaisa ɗaya ta ce"Mama ce ta ce mu zo mu taya ki haɗa kaya".

Aisha ta ce"Ba komai a na haɗa ma".

Ta ce"To ga Ashiru nan a ƙofar gida, da kura zai kwashi kayan".

Aisha ta ce"Kura kuma? Kin ga fa iya akwatunana ne guda biyu, ba sai da kura ba ma".

Suka ɗaukar mata akwatunan ta shiga kitchen ta kwaso sauran kayan abincinsu duka ta tafi da su, Ashiru ya riga su ƙarasawa gidan, ya faɗawa Mama ta ce babu wasu kaya da za a saka a kura, don haka Mama ta yi tsaye a tsakar gidan tana jiran shigowarta ta ji me ta taka da za ta ƙi kwaso duka kayanta?

Suna shigowa ko sallama ba ta amsa ba ta ce"Aisha ya na ga haka? Ina sauran kayan?"

Ta ce"Mama gani na yi tun da ba garin zan bari ba, muna kusa da gidan ai ba sai na kwaso duka ba, idan ina buƙatar wani abun sai na je na ɗauka, tun da dama duk sati zan dinga zuwa ina share gidan".

Mama ta ce"Too! Haka kika tsara? Amma tun da Ashiru zai dinga kwana a can har sai kin je kin share? Shara ai ta mai kwana a gida ce".

Ba ta ce mata komai ba, ta ja ta tsaya, tana jiran ta ga ɗakin da aka ba ta.

Mama ta ce"Ga ɗakin can, ku ƙarasa da kayan".

Aisha ta ƙarasa ɗakin Umman ta gaishe da Baba, ya amsa yana cewa"Ashe kin ƙaraso, to Allah Ya ba mu haƙurin zama da juna".

Ta amsa da "Amin".

Ya ce"E, ai haka shi ne daidai, babu amfanin ya kwashe ki ku tafi, ku je ku kaɗai a yi ta ƙuruciya babu idon wani babba a kusa".

Ba ta ce komai ba ta tashi ta fice, shi kuwa da ba gani yake ba, bai san ta fita ba ya ci gaba da faɗin"Ai da nan ɗin da can duk ɗaya ne, tun da dai zai dinga yo aike babu abin da zai gagara in sha Allah, za a dafa ki ci ki sha to me kuma ya yi saura?"

Mama da ta shigo ta tsaya tana kallonsa tare da son gano da wanda yake magana haka a tsanake, ta riƙe haɓa ta ce"Ikon Allah! Malam kuma yau gamo ka yi, ka fara magana da aljanu?"

Ya gyara zama ya ce"Kamar ya aljanu? Ni kaɗai kika gani a ɗakin da za ka ce haka? Da Aisha nake".

Mama ta ce"Wace Aishar? To babu kowa a ɗakin nan sai kai ɗaya".

Ya ce"Kenan ficewa ta yi ta bar ni, saboda raini nake yi ni kaɗai".

Mama ta ce"Hmm, kaɗan ma ka gani indai wannan sumumu kasau ɗin ce".

Aisha ta shiga ɗakin ta zauna, wata tsoguwar rabarma ce ta tarar a ciki ta fara tunanin inda za ta kwana, ta ce da ɗaya daga cikin yaran"Suwaiba ashe ba katifa, ai da na san haka ne da na kwaso kayan shimfiɗa".

Ta ce"Ai sai mu koma mu ɗakko".

Yarinyar ta fita tana cewa"Mama ashe ba katifa..."

Tun kafin ta ƙarasa ta ce"Katifa!? To ai Abban bai siyo ya saka ba, idan kuma tawa za ki kai mata ga ki ga ta".

Suwaiba ta ce"A'a ai da ita ma sai ta ɗakko tata".

Mama ta ce"Shi kuma ɗan jiron gidan ya dinga kwana a ina?"

Ran Aisha ya ɓaci ta fara tunanin kenan ma ana nufin a kan gadonta Ashiru zai dinga kwana, ta kasa jurewa ta fito ta ce"Amma Mama ai na yi zaton a falo zai dinga kwana, ya yi shimfiɗa".

Mama ta ce"Au haka kika tsara? To ai shi kenan, ke da gidanki ai sai yadda kika ce".

Ta san sarai da gatse Mama ta yi maganar, amma ta maze ba ta ce komai ba, saboda gaskiya ita ba za ta so ma a ce wai yana buɗe mata ɗakin gadonta ba, wannan ba dacewa ba ce, ta shiga ɗaki ta ɗakko mara kayan abincin ta ajiye ta ce"Bari na koma na kwaso bargo da fulo".

Mama ta ce"Au kin fasa ɗakko katifar?"

Aisha tana ficewa ta ce"Ni da dama ban ce zan ɗakko katifa ba".

Yaran ne suka ƙara rakata ta ɗakko kayan shimfiɗar, tana dawowa Mama ta ce"To ai sai ki kawo mukullin gidan ko?"

Ta miƙa mata, ta shiga ɗakin da ya zama nata, ta zauna ta yi shiru tana tunanin yadda zaman zai kasance, har ta fara jin kewar gidanta da mijinta tun yanzu.

Can bayan la'asar tana jin Mama ta ɗora girki, ta fito ta karɓa shinkafa da wake ne da miya, ta gama ta kwashe a kula ta kai mata ɗaki. Ba ta san abin da Maman ta tsara ba sai bayan magriba da ta ga Muhibba ƴar ƙanwar Abba ta zo gidan da fagon kayanta, ta doshi ɗakinta, Mama ta kalle ta kalli Aisha ta wutsiyar ido ta ce"Ga ƴar zaman ɗaki nan kin samu".

Aisha ta ce"To na gode".

Muhibba yarinya ce ƴar shekara bakwai, irin yaran nan masu ɗan banzan surutu da kwasar zance, tun da ta ji Anti Amarya za ta koma gidan Mama ta ce ita ma za ta koma can ɗin ta zauna a wajenta. Aisha ta zuba ido ta ga ta inda za a fara ba ta abincin daren da ta dafa ta ji shiru, ba a ce mata ga abinci ba, har sallar isha'i shiru, sai ta tashi ta shiga ɗakinta, ta ɗakko cincin ta zauna ta fara ci, tana cikin ci Muhibba ta shigo ta zauna tana zare ido, Aisha tana sane ta hana ta cincin ɗin saboda ta tsani ta ga yaro mai kwaɗayi a gabanta ta cinye wanda ta ɗebo ta sha ruwa ta nemi waje ta kwanta.

Yarinyar ta fice sum-sum, ta je kusa da Mama ta rakuɓe kamar mara lafiya, Mama ta ce"Uwata, lafiya? Ba ki kwanta ba?"

Ta ce"Mama ni ma zan ci cincin ɗin".

Mama ta ce"Wane irin cincin kuma? Gani kika yi ina ci? Ba na son kwaɗayi fa".

Ta ce"Anti Amarya ce take ci".

Mama ta taɓe baki ta ce"To ina ruwanki? Ke da shegen kwaɗayi ita da matsiyaciyar rowa, kuma a gabanki take ci ba ta ba ki ba?"

Ta ce"E ina kallonta ta cinye".

Mama ta ce"Tafi ki kwanta, ni ban iya roƙo ba ballantana na roƙar miki".

Ta ce"Wuce ki je ki kwanta".

Muhibba ta koma ta kwanta, Aisha ba ta san an yi wannan ba, da safe ma da ta tashi da yunwa ta ɗakko cincin ɗinta tana ci, ta yi zaton ma yarinyar bacci take yi, ba ta san tana kallonta ba.

Bakwai na safe Abba ya kira ta a waya, suka gaisa ya ce ya sauka lafiya, dare ya yi jiyan shiyasa bai kira ta ba, ya ce"Kina can gidan Maman ko?"

Ta ce"Ina can".

Ya ce"Komai dai normal ai".

Ta ce"E, ga ni dai a ɗakin da aka ba ni".

Ya ce"To don Allah ki ƙara haƙuri, kin san irin wannan zaman sai ka yi haƙuri, Allah Ya rufa asiri".

Ta ce"Babu komai, zan yi haƙuri in sha Allah, amma kuma ni fa akwai tsarin da bai yi mini ba".

Ya ce"To me ya faru?"

Ta ce"Bai kamata a ce Ashiru zai dinga kwana a gadonmu ba, kamata ya yi ya kwana a falo, a ce iya nan zai dinga shiga".

Ya ce"To dama wane ne ya ce zai kwana a ɗakin gado? Ai ba zai yiwu ba".

Ta taɓe baki ta ce"Haka Maman ta tsara".

Ya ce"Bari na kira ta za mu yi magana".

Tana ajiye wayar Muhibba ta tashi ta fita, ta samu Mama tana dama koko, tana waigen bayanta kamar sabuwar munafuka ta ce"Mama ashe cincin ɗin bai ƙare ba, yanzu ma ta ci".

Mama ta ce"Ke dalla ba na son gulma!".

Ta ce"Kuma yanzu suka yi waya da Uncle Abba, na ji har tana ce masa Uncle Ashiru kar ya kwana a gadonta".

Nan take ran Mama ya ɓaci ta haɗe fuska ta ce"Da gaske? Kenan ya sauka shi ne ita zai fara kira ba ni da nake uwarsa ba, kuma da take kai ƙarata wajenshi dukana zai yi?" Ta yi ƙwafa ta ci gaba da abin da take yi.

Ko minti biyu ba a yi ba wayar Mama ta fara ringing, Muhibba ta ɗakko mata ta ɗaga, tana jin muryar Abba ta ce"Waye?"

Ya ce"A! Yau kuma muryata ce ta ɓace miki Mama?"

Mama ta ce"Idan ta ɓace mini ma ai ba komai ba ne, tun da ni ma tun daga yanzu matsayina a wajenka ya fara ɓacewa".

Ya ce"Subhanallah! Mama me ya kawo wannan maganar?"

Ta ce"Ashe Abba mahaifiya ba ta cancanci ta zama farkon wacce za ka fara kira ka sanar da ita ka sauka lafiya ba? Sai dai mu ji a bakin matarka ko? Ai shikenan, dama surukan yanzu sun mayar da uwar miji ƴar niƙa su karɓe garin".

Ya ce"Haba Mama yanzu duk me ya kawo wannan zancen? Ni fa ban yi haka da wata manufa ba, sani na yi sai a yi ta kiranki ma ki ƙi ɗauka, kin fita kin bar wayar a gida, yanzu ko kiran Aisha na yi na ce ta ba ku wayar ashe sai ya zama laifi? Kuma ita ma ai amana ce a wajena, ya dace na damu da sanin ya ta kwana".

Yana direwa Mama ta ce"Baba ka gama? Na ce ka gama yi mini faɗa ko da saura? Yanzu Abba ni ka zauna kake tsarawa maganganun nan saboda mace? Ai shikenan, sai ka dawo ka ga ya ta kwana, ka ga ina da ina na gutsura a jikinta na cinye".

Ya ce"Kai Mama, don girman Allah ki yi haƙuri maganar nan ta wuce haka na sauka lafiya fa kin ganmu nan a masauki, za mu yi bacci kafin a kaimu wajen aikin".

Ta ce"To Allah Ya taimaka Ya dafa muku".

Ya ce"Amin Mama na gode, sai na sake kira".

Daga haka suka yi sallama.

Mama ta gama haɗa abun karyawa, ta zubawa kowa nashi ta bawa Muhibba ta kai wa Aisha kokonta da ƙosai na ɗari da hamsin, Aisha tana buɗe kokon zuciyarta ta fara tashi, ba ta shan koko tun can ma, tada mata da zuciya yake yi, ballantana yanzu da take da ciki mai tsirar abubuwa kala-kala, ba za ta cuci kanta ta sha abin da ranta ba ya so ba, sai dai kuma ba ta son mayarwa da Mama abunta kar ta ce ta raina, sai ta rasa yadda za ta yi, har Muhibba ta gama shiryawa ta tafi makaranta, ta cinye ƙosan dai, can dai ta fito da shi, ta samu Mama tana wanke-wanke, ta ƙarasa tana cewa"Haba Mama ai kin san zan fito na yi, ya za a yi ina gidan ki yi wanke-wanke?"

Mama ta taɓe baki ta ce"To ni zan zauna da ƙazanta ne kina can kina soyayya a waya?"

Aisha ta ce"Mama ni fa ba na shan koko, ga shi na dai ci ƙosan".

Mama ta ce"Au Allah? Ashe fa ku sai shayi mai kauri da wainar ƙwai, to kin ga dai mu yadda muke rayuwarmu, ga shi bai fara turo kuɗin ba ballantana ki ce za ki yi zaɓi".

Aisha ta ce"Ba haka ba ne, ni da ma can ba na shan koko, tashin zuciya yake saka ni, ba wai rainawa na yi ba".

Mama ta ce"Hmm! To Allah Ya kyauta, dama ai kin karya da cincin".

Ta tashi ta karɓi kokon ta shiga ɗaki, ita kuma ta zauna ta ci gaba da wanke-wanken.

Mama ta shiga ɗaki ta ajiye kokon tana cewa"Malam anjima idan za ka ƙara koko ga shi nan ko ba na nan ka laluba gefen gadon nan".

Ya ce"To, yau da yawa kika dama kenan".

Ta ce"Ina fa! Wannan yarinyar ce matar Abba ta ce ita ba za ta sha koko ba".

Da mamaki ya ce"Ba za ta sha koko ba?"

Mama ta taɓe baki ta ce"To wannan har wani abun mamaki ne? Ka san me da me yake jibge mata a gidan tana ci? Ta saba ta karya da shayi mai kauri da wainar ƙwai, ka ga kuwa ina ita ina koko?"

Ya ce"Lallai wannan yarinya ta samu waje".

Mama ta ce"Tukunna ma! Ai ka zuba ido za ka ga ikon Allah...".

Ya katse ta da faɗin"Da wane idon zan gani? Sai dai ko na ji".

Mama ta ce"To ai kuwa za ka ji, don ina mai tabbatar maka yarinyar nan gaba ma cewa za ta yi ba ta son kalar abincin da muke ci".

Ya ce"Danƙari!".

Ta ce"To ai shi ne abin da nake ta nuna maka ka kasa ganewa, yanzu inda ya kwashe ta sun tafi wa ya san me zai ba ta ta ci?"

Baba ya jinjina kai ya ce"Sai Allah!".

Aisha ta gama wanke-wanken ta share gidan ta gyara ko'ina ta koma ɗakinta ta gyara ta kwanta, yunwa take ji rabonta da abinci tun na jiya da rana da ta ci a gidanta, sai cincin ɗin da take ta ci, a matsayinta na me ciki ya kamata a ce ta ci wani abu mai nauyi, Abba ya ba ta kuɗi kafin ya tafi, amma tana fargabar ta fita ta siyo wani abun Mama ta yi mata wata fassarar, don haka ta yanke za ta haƙura ta jira na rana.

Tun wajen ƙarfe goma Mama ta tafi, ta dai cewa Aisha za ta fita, amma ba ta san inda ta tafi ba, shiru har sha biyu ta yi, yunwa ta addabi Aisha ga shi kuma Maman ba ta bar mata sallahun ta yi girki ba, don haka ta fito tana leƙen ƙofar gida, a zaune a ƙofar gidan ta ga Baba shi kaɗai da carbi a hannunsa, ta yi shiru ba ta kula shi ba, saboda ba ta son ma ya san ta fito ƙofar gidan, tana ta kalle-kallenta ta ga wata yarinya ta zo wucewa da bokitin alala, ta yafito ta da hannu, ta zo, suka shiga cikin gidan, ta siya ta ba ta kuɗin, ta zauna ta ci ta sha ruwa, ta kwanta, sai ga kiran Abba, sun daɗe suna waya kafin su yi sallama, sai bacci ta ɗauke ta.

Dawowar Muhibba daga makaranta ne ya tashw ta, lokacin ƙarfe ɗaya da rabi, ta fito don yin sallah, ta ga Mama tana ta fifita wuta, Aisha ta ce"Mama ashe kin dawo, sannu da zuwa".

Mama ta taɓe baki ta ce"Ni ai na fi awa ɗaya da dawowa, kina bacci ina za ki san na dawo? Lallai idan ka samu dama sai ka dama".

A yadda Aisha ta lura da maganarta kenan baccin da ta yi ma ya zama laifi, bacci fa mai ciki kuwa ai ba komai ba ne, kuma ma idan ba ta yi baccin ma me za ta yi?"

Ta ɗauki buta ta wuce banɗaki, tana idar da sallah ta fito, lokacin Mama tana daka yaji, ta karɓa tana daka mata, ita kuma ta ɗakko fulawa ta juye a roba ta fara kwaɓa ɗan wake, Aisha sai ta shiga damuwa, saboda ba ta cin ɗan wake sai dole, sam bai dame ta ba, da safe ta ƙi shan koko yanzu idan ba ta ci ɗan waken ba wane kallo za su yi mata? Don haka da aka gama ta daure ta ci kaɗan.

Mama tana ganin wanda ta dawo da shi ta ce"Ikon Allah! Wai ni Aisha ko dai raba girki za mu yi? Tun sa kin rainawa bamu babu ɗan ƙashin da zau sa ki ji ya yi miki daɗi, sai ki kwaso kayan kitchen ɗinki kawai ki dinga girki".

Aisha ta ce"Wallahi Mama ba haka ba ne, ɗan waken ne bai dame ni ba, kuma ai na ci".

Mama ta taɓe baki ta ce"To Allah Ya kyauta".

*** ***

*RANAR KUKA!*

BY

*SADIYA ABDULRAZAƘ*

*FIRST CLASS WRITERS*

MARUBUCIYAR Sandar dukan uwargida Zuciyar mace Miji goma... Iya ruwa... Wani auren Matar shige... Da walakin Wutar ƙaiƙayi Alhakin so ***