PAGE 4
GIDAN HABIBU
Yau kwana uku da tafiyarsa, ya kama aikin da ya kai shi ya fara yi tuƙuru, babbar damuwarsa dai ɗaya ce ta yadda ya san ya baro iyalinsa babu wadatar komai a gidan, ga shi kullum idan suka yi waya da Halima sai ta yi masa ƙorafi, har ya fara nadamar tafiyar tun kafin a ci Talata ballantana Laraba. Wannan dubu biyar babu inda ta kai musu ta ƙare, ga shi ita ba sana'ar komai take yi ba ballantana ta tallafa, ƙarshe dai sai mahaifiyarsa ya yi wa bayani, take aika musu abinci idan ta dafa, a haka ma Halima ba ta bar shi da mitar ba ya isar su ba, yau da sassafe yana kwance yana bacci cike da gajiya ta kira shi, suna gaisawa ta ce"Yanzu baban Islam a haka rayuwarmu za ta ci gaba da tafiya?"
Ya tashi zaune yana cewa"Wannan wace irin magana ce haka Halima? Me kuma ya faru?"
Ta ce"Ka ga fa wani ɗan koko sa aka aiko mana ko iya yaran ne suka shanye ba isarsu zai yi ba, koko haka tsurarsa ko ƙosai babu, gaskiya ni fa na fara gajiya!".
Takaici ya kama shi, don ya gaji da ƙorafinta, yanzu haka babu komai a cikinsa, don jiya ma haka ya kwana bai ci ba, kuma ya tashi babu ko sisi. Ya ce"Haba Halima, kin san fa ba wai kuɗi na bawa mahaifiyata na ce ta dinga ba ku abinci ba, taimako ne take yi, duk wanda aka samu ya kamata ki karɓa ki gode, Allah ma cewa ya yi idan mun gode masa zai ƙara mana".
Ta ce"Ni dama ai ban ce dole sai ta ba mu ba, tun da ba haƙƙinta ba ne, kai ne dai za ka nema ka ba mu, ni gaskiya na fara gajiya, yanzu da kake ƙafafar sai mun tafi tare da na kwashi ƴaƴan mun tafi me za ka ba mu mu ci? Ko bara za mu yi?"
Ya ce"Kin ga Halima don Allah Ya ishe ni haka, kin fara kai ni bango, ni ɗanki ne da za ki kira ni kina ɗaga mini murya? Ko kuma ke ba ki san ƙaddara ba? Sata zan yi na ba ki?"
Ta ce"Kar ka yi sata, amma ka sani ni dai na gaji zan tafi gidanmu, don ba zan yi zaman yunwa ba!".
Ya ce"Idan kin ga hakan shi ya fi to Allah Ya tsare hanya".
Mamaki ya daskarar da ita, saboda ko me suke yi da Habibu da zarar ta ambaci tafiya gidansu yake yin ladab, amma ta ga yanzu tafarat ɗaya ya ce ta tafi. Ta zauna jaɓar riƙe da waya ta ce"To me yake faruwa ne? Ko don ya ga ba ya garin?"
Haka suka taɓa kokon, yara suka tafi makaranta. Ta wuni tana nazarin shin ta tafi gidan ko ta haƙura? Ba ta son a ce daga tafiyarsa har ta fara kai ƙararsa, tun da take ba ta taɓa yin yaji ba, sai ta yanke gara ta haƙura ta ga gudun ruwansa.
Sati ɗaya a tsakani ya kira ta a waya, tun ranar da ta ce za ta tafi gida ba su sake yin waya ba sai yau, kuma ya san ba ta tafin ba, don da ta tafi mahaifiyarsa za ta faɗa masa ta aika mata abinci ba a same ta ba, tun da ita kullum suna yin waya, ya ƙi kiranta be don ya nuna mata kuskurenta, ita kuma ta hau dokin zuciya ba ta kira shi ba, yau ɗin ma wani abokinsa ne ya yi masa biyan bashin dubu goma sha biyar da yake bin sa tun kafin ya tafi, shiyasa ya kira ta don ya ba ta kuɗin, kamar kar ta ɗauki wayar saboda tana fushi da shi, sai kuma ta danne zuciyarta ta ɗauka don ta ji da wacce zai zo, ta ɗaga ta yi shiru, ya ce"Assalamu alaikum, Halima".
Ta yi wata harara kamar yana kallonta ba ta ce komai ba, ya ce"Hello".
Ta ce"Ina jinka fa, ka yi maganarka kai tsaye kawai".
Ya ce"Au kina jina shi ne ko gaisuwa babu?"
Ta yi shiru.
Ya ce"To ki turo min account number da zan saka miki ɗan wani abu".
"Ɗan wani abu?" Ta tambaya cikin ɓacin rai.
Sannan ta ɗora da faɗin"Yanzu duk kwanakin da ka kwashe ka bar mu da raɓe-raɓe a ci a sammana shi ne za ka ce ɗan wani abu za ka turo mini?"
Ya ce"Idan ba za ki turo ba ki bar shi, sai na sakawa Umma duka kuɗin ta ci gaba da sammuku". Daga haka ya katse kiran.
Ta bi wayar da kallon mamaki, kamar kar ta tura sai dai ta daure ta tura ko don ta ga gudun ruwansa, babu jimawa ta ga alert ɗin dubu goma, don raba musu ya yi, ya ba wa Umma dubiyar ita kuma goma, mamaki ya kama ta da ganin wannan kuɗin, ita fa bayan tunanin tarbiyyar yaranta har da bin shawarar ƙawarta a wannan rashin yarda ta bi shi ɗin, ƙawarta Hadiza ita ma mijinta ba ya garin ya tafi neman kuɗi, ta ce ita hakan gaba ya kaita sosai, saboda uwar ribar da take ci a kuɗin abincin da yake turo mata, ita ma indai tana cancanawa za ta samu alheri, sai ga shi ita ba ta ga alamar za a yi abun arziƙi da nata mijin ba.
Ƙarshe dai ta ba wa zuciyarta haƙuri ta bar shi ta ga duk bayan kwana nawa ne zai dinga turo mata dubu goman. Da kanta ta fita ta siyo musu kayan abincin, ita da ko cefane ba ya barinta ta fita ta yo, shi ne yake yin abinsa, saboda yana kishin ta je shago ko wajen mai kayan miya, amma sai ga shi yau ta samu ƴancin fita duk inda take so.
Gida ne wanda hatta ruwan amfani sai an siya, omo, sabulu, man shafawa, a yi awon abinci kuma a yi cefane saboda haka dubu goma ba komai ba ce, shi kansa ya sani tun da shi ne mai yin cefanen, amma ya zai yi? Jira dai yake yi komai ya daidaita a fara biyansa.
Bayan kwana biyu Halima ta faɗa masa ba su da komai, sai aka koma ƴar gidan jiya ake aiko musu abinci daga gidansu. Wataran ƙawarta Hadiza ta zo kawo mata ziyara, da fari ta so ɓoye mata halin da suke ciki da Habibu, to amma sai ta ga ba ta da niyyar tafiya da alama wuni ta zo yi, ga shi ita ba ta saba cin bashi ba ballantana ta fita maƙota ta aro ta yi cefane ta yi girki, don ta san abun kunya ne Hadiza ta ji yanzu ɗora tukunya ma ya gagari gidanta sai dai uwar miji ta aiko mata.
Musamman yadda ta ji Hadizan tana zugata da cewar"Yanzu za ki tashi daga Maman Islam ki koma Hajiya Maman Islam, ke ni sai na ga kamar ma har kin fara yin ƙiba, ko dai mai balangu kike kai wa ziyara?"
Halima ta yi dariya ta ce"Hmm! Hadiza kenan".
Hadiza ta ce"Allah kuwa, ni dai ba na taɓa yin kwana uku ban ci kaza ko balangu ba, yana can yana wahalarsa ina nan ina cin daɗin".
Halima ta ce"Ma sha Allah! Dole ki ci".
Hadiza ta ce"Ai wallahi ni wannan tafiyar gaba ta kai ni, kin san fa da farko har ina rantsuwar sai na bi shi, shi ne fa ya ƙi tafiya da ni, na yi zaton guduwa zai yi ya bar ni da wahala, sai ga shi ashe ƙarshe ni ke da riba".
Halima ta ce"To ke har nawa yake aiko miki ne?"
Hadiza ta ce"Kin ga duk wata zai turawa ƙaninsa kuɗi ya siyo mana kayan abinci, komai da komai, hatta ashana wannan kar ki cire ta, kayan miya kawai nake siya, sai kuma ya turo mini dubu hamsin a account ɗina na cefane, bayan nan kuma duk wani abu da ya taso na buƙatata zan faɗa masa ya turo mini, anko har na ƙanwar ƙawa ba ya wuce ni, ki ga yanzu haka kawai ma ɗinkuna nake yi, da kuwa sai sallah-sallah, kin ga yanzu kaf gidanmu iyayena sun fi alfahari da ni, saboda kuɗin da nake kai musu, wai ba ki san yanzu Umma ta daina fanken siyarwa ba?"
Halima ta ce"Allah Hadiza? Kuma wai duk a cikin kuɗin da yake aiko miki?"
Gaban Hadiza ya faɗi, ta yi murmushin yaƙe ta ce"Ai bayan wannan kuɗin ma ina yin ɗan kasuwancina".
Don kar ma ta tambaye ta wane kasuwanci, sai ta ɗora da faɗin"Ke yanzu nawa kuka yi da shi zai dinga aiko miki?"
Halima ta ce"Hmm! Ni fa babu wani abun arziƙi, don kin ga tun sa ya tafi sau ɗaya ya aiko mini dubu goma, yanzu haka zancen da nake yi miki ba na yin girki, abinci tun daga na safe har dare aiko mana ake yi daga gidansu".
Hadiza ta fara salati tana tafa hannuwa ta ce"Shi kenan! Shikenan Halima kin kashe kanki! Yanzu da gaske uwar miji ce take aiko miki abinci? Ko na ce take sammiki?"
Halima ta yi ƙwafa ta ce"Hmm, kina zaune a nan za ta aiko na rana, ɗan haka a kula ko ƙoshi ba ma yi, da na yi maza ƙorafi sai cewa ya yi na godewa Allah tun da ba biyanta yake yi ba".
Hadiza ta ce"Wannan ai wulaƙanci ne a ce ke da yara biyar za a dinga sammuku abinci, wallahi laifinki ne da kika yi masa lakwa-lakwa".
Halima ta ce"To ya ce ba a fara biyansa ba ya zan yi?"
Hadiza ta ce"Ƙarya yake yi! Duk yadda aka yi ita uwar tashi ce ta tsara masa ita zai dinga turawa kuɗin, ki yi tunani mana, wallahi tura mata yake tana sammuku".
Halima ta ce"Kai gaskiya ba na tunanin Umma za ta yi haka, ƙila da gaske ba a fara biyan nashi ba, shi mijinki aikin me yake yi a can ɗin?"
Hadiza ta ce"Oho masa! Aikin ƙarfi ne fa duk suke zuwa su yi, a can an san muhimmancin mutum ana biyansu da daraja".
Tana rufe baki sai ga sallamar yaro ya shigo da kular abinci, Hadiza ce ta karɓa ta buɗe tana kallon shinkafa da waken a shatale, sannan ta dangwarar da kular ta ce"Lallai Halima kina wani hali mai wuyar fita!".
Halima ta ce"To ya zan yi?"
Hadiza ta ce"Ke kuwa kike da yadda za ki yi, wani abun fa sai ka yi bore ka yi jan ido ka nuna kai shege ne sannan ake raga maka, ki nuna masa wannan zaman fa ba da ke za a yi shi ba".
Ta ce"Wallahi na faɗa masa har barazanar zan tafi gidanmu na yi masa, amma sai cewa ya yi na tafi ɗin".
Hadiza ta ce"A haf! Wallahi kin kar kanki, da kuka yi haka da shi to me ya hana ki tafiya? Wannan ne fa yake ba shi lasisin ci gaba da yin yadda ya so, tun da ya san komai kika faɗa barazana ne, ba za ki iya aiwatarwa ba, inda a ce kin tafin ai za a daidaita, kuma gobe idan kika ce za ki tafin sai ki ga ya yi miki yadda kike so".
Halima ta ce"Ni kuma sai nake ganin kamar ba zai damu ba, tun da ba ya garin ballantana a ce zai ji gidan babu daɗi".
Hadiza ta ce"To shikenan Halima ki zauna, ki zauna ki ƙare rayuwarki a haka, ni dai kin ga tafiyata".
Ta ƙarasa tana tashi ta ɗauki mayafinya ta yafa.
Halima ta ce"A'a ga abinci an kawo ki tsaya na zuba miki".
Hadiza ta ce"A habawa, wannan guntun abincin naku zan saka muku rani?"
Ta ciro dubu biyu a jakarta ta miƙa mata tana cewa"Ga wannan kya yi wani abun, Allah Ya rufa asiri".
Halima ta yi mata godiya ta raka ta har ƙofar gida.
Ta dawo ta zauna tana ta auna maganganun ƙawar tata, ta yarda ɗari nisa ɗari gaskiya ta faɗa mata, saboda haka ta yanke hukuncin gara ta je gidan a yi wacce za a yi, yaran suna dawowa daga makaranta suka ci abincin suka yi wanka ta loda kaya a akwatuna biyu ta tisa su a gaba suka tafi gidan iyayenta. ***
*RANAR KUKA!*
BY
*SADIYA ABDULRAZAƘ*
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR Sandar dukan uwargida Zuciyar mace Miji goma... Iya ruwa... Wani auren Matar shige... Da walakin Wutar ƙaiƙayi Alhakin so ***