PAGE 5
GIDAN SHAMSU
Tun da ya saka ƙafa ya bar garin sabuwar duniya ta buɗewa Ummi ita da ƴan majalisarta, dama ta saba da wani tsari, akwai yaran maƙota wanda iyayensu suke yi musu tsanani ba sa barin su kula samari, saboda a ƙa'ida shekarunsu ba su kai su fara soyayya ba, su kuma rashin ji da rawar ya sa suka ƙi ji, suke kula su a ɓoye, to idan saurayi ya ba ka wani abu na ci sai ka zarce gidan Ummi uwar daba ka ba ta ajiya ko ka zauna ka ci a can ka ba ta kasonta.
Dama wani abun tana ragewa ne saboda idon Shamsu, yanzu kuwa da ba ya nan ai sai ta falle ta shigo da sababbin tsare-tsare, lambar wayarta kuwa ta zama kamar jamfa a Jos, saboda yadda yara ƙananu suke bawa samarinsu, idan sun zo su yi musu plashin su kira su su sha wayarsu.
Ga kuma wani sabon salo da ta tsiro da shi, a da ƴan matan suna janyo samarinsu su yi zance a ƙofar gidanta, to yanzu saboda samun sake har cikin gida suke shigowa, su shiga falonta su yi zance, yarinya ta yo cefane Ummi ta sheƙawa ƙato girki, musamman da ta ga idan za su tafi suna ba ta ɗan canji, cikin yaran har wacce ba ta taɓa zance ba yanzu ta fara yi silar gidan Ummi, har rige-rige ake yi na wacce saurayinta zai zo, ƙarshe sai ta kasa musu abun, wasu su yi na safe wasu na rana wasu na yamma, wasu na dare, haka kuwa ake yi, to cikin samarin akwai ƴan ƙari waɗanda suke zuwa zance hannu na dukan jinya kuma su gama su kaɗe rigarsu su tafi, wata bazawa mai suna Farida ce ta zuga Ummi akan duk wacce saurayinta yake ɗan ƙari to sai dai ta fara biyan kuɗin zance, tun da Ummin ba baiwarsu ba ce da za ta gyara musu ɗaki su yi zance su tashi a banza, Ummi kuwa a yanzu ta fi ɗaukar shawarar Farida akan ta kowa, saboda akwai wanda yake zuwa su yi zance, duk ranar da ya zo to idan zai tafi sai ya ba ta dubu biyu ta bawa Ummin.
Ta sa aka kira mata kowa ta tara su kamar abun arziƙi, sai da kowa ya zo sannan ta fara magana, ta ce"To dama na kira kowa ne saboda a yi a gaban kowa kar wani ya ce an munafurce shi, ko kuma na yanke hukuncin da na tanada wata ta ga kamar ban yi mata adalci ba".
Kowa ya sha jinin jikinsa wasu daga ciki suna fargabar Allah Ya sa ba hana su zance za ta yi ba, ban da Farida da ta tsara abun ta san kwanan zancen.
Ummi ta ɗora da faɗin"Kun san dai wannan zancen da kuke yi a gidana alfarma ce nake yi muku ko? Kuma kun san mijina bai sani ba, idan ya sani kuma ni ce a ruwa ba ku ba, amma a haka nake daurewa saboda na share muku hawayenku na samawa kowa ƴancin soyayya da wanda take so".
Suka ɗauki shewa suna yi mata godiya.
Ummi ta ce"To a gaskiya da sauran rina a kaba! Cikin samarinku akwai ƴan albarka akwai ƴan banza ta faɗi, to ni dai ba zan ce kar ku kula ƴan banza ta faɗi ba, tun da ba ni zan yi muku soyayya da zaman auren ba, duk wacce ta auri ɗan ƙari ita ce za ta ji a jikinta, bari dai na tafi kai tsaye, a gaskiya duk ba sai na yi tone-tone ba, duk wacce ta san saurayinta ba ya ba ni komai idan ya zo to ta san kanta, wasu ma ƙila yana ba su kuɗin zancen noƙewa suke yi, to ni wannan bai shafe ni ba, kawai daga yau zance a gidana ya zama na kuɗi, duk wacce ta yi zance za ta biya kuɗin ɗaki naira ɗari biyar, idan kin san ba zai ba ki kuɗi ba to kar ma ki kawo mini shi gida".
Safiyya da ta gama tsarguwa da ita ake don saurayinta ba ya ba ta uwar komai ta ce"Amma Anti Ummi idan bai baka ba ya za ka yi?"
Ummi ta ce"Wannan matsalarki ce, sai ki roƙe shi ki ce ya ba ki, dama fa ke saurayin nan naki ko kati bai taɓa sako mini ba".
Lawisa ƴar shekara goma sha uku ma ta yi farat ta ce"Wallahi wasu ba sa ba da komai, ni fa saurayina bai ma fara sana'a ba".
Ummi ta ce"Don ƙwal ubansa ya san ba shi da sana'a ya fara soyayya? To za a fito da sabon tsari, zance a cikin gida a falo ɗari biyar, a cikin gida a zaure ɗari uku, a ƙofar gida kuma ɗari biyu, tun da ai an jingina a jikin katangar gidana, ko ba haka ba?" Ummi ta ƙare maganar tana kallon Farida.
Farida ta jinjina kai ta ce"Ƙwarai ma kuwa! Duk wacce ba za ta iya ba ta ƙara gaba, a ce falon nan naki a share a gyare ga ƙamshi ga fanka ga kayan kallo, mutum ya zo ya share ɗuwawu ya gama zance ya tashi ya tafi?"
Ummi ta ce"Gaskiya fa, kowa ya je ya yi shawara".
Wasu a nan take suka amince, wasu kuma suka tafi suna tunani, musamman ƙananun yaran da ba a san suna kula samari ba.
Tun daga ranar doka ta fara aiki, Ummi ta dinga adana kuɗinta, yawanci ƴan matan da kansu suke biyan kuɗin, musamman waɗanda iyayensu suke kasa musu talla sai su zara a ciki, su ba ta, ita kuwa ranta fess tana ta adanawa.
Yau Shamsu sun ɗan samu hutu ga kewarta da yake ji sosai, don haka ya kwanta ya kira ta don su sha fira, sosai yake kewar shirmenta, ya yi kusan minti ashirin yana kira da farko waya ake ta yi, daga baya kuma sai yake ta kora ba a ɗagawa, ransa ya ɓaci, ba yau ya fara kiranta yana jin haka ba, har bacci ya fara ɗaukarsa ya ga kiranta, ya ɗauka suka gaisa ya ce"Ke Ummi da wa kike ta waya haka ne?"
Ta ce"Maƙociyata ce ta ari wayar suke waya da mijinta".
Ya ce"To gaskiya ban yarda ba, ba zan amince ba wallahi, ta ya wani ƙato zai samu lambarki a banza? Shi mijin nata uban me ya hana shi siya mata wayar? To kar na sake kiranki na ji busy".
Ta dinga harara tana murguɗa baki kamar yana kallonta, sannan a daƙile ta ce"Na ji!".
Sai ya sassauta murya ya ce"To ya kike? Ina ta kewarki fa, ke fa?"
Ta taɓe baki ta ce"Ni ai da mutane a gidan ba zan ji kewar komai ba".
Ya ce"Ni da na ji kewar taki ni kaɗai nake rayuwa a daji? Ni ma ai ga mutanen nan, amma zuciyata ke kaɗai take tunani".
Ta ce"Lallai wannan zuciyar taka tana da ƙarfin hali, yanzu duk baƙar wuyar da kake sha ba ta saduda ta sa ka manta da soyayya ba? Lallai ba ka ji wuya ba, ƙila ba ku fara jan ciki a cikin taɓo ba" Ta saka dariya.
Ya yi guntun tsaki ya ce"Ummi kenan, ashe ba kya ma jin tausayina ko? Ke fa na lura ko zan shekara a can bai dame ki ba".
A ranta ta ce'Da za ka shekara ai da na ji daɗi, sai na yi ƙiba kafin ka dawo'.
A fili kuma ta ce"A'a Allah na damu da kai".
Ya ce"Na so a ce kina da babbar waya, da mun ɗan yi vedio call na ganki".
Ta taɓe baki ta ce"Ba ka ƙi siya mini ba, kowa da ƴar wayarsa sai ni ce har yanzu da raka ni kashi".
Ya ce"Ki yi haƙuri ki ci gaba da taya ni addu'a, idan na haye a albashina na farko zan ware kuɗin wayarki in sha Allah!".
Ta yi murmushi ta ce"Ai kuwa da na ji daɗi, Allah Ya sa ka haye ɗin, wa ya gan ni da babbar waya? Ai ina ga ina ga kwana zan yi ranar ina kallonta".
Ya yi ƴar dariya ya ce"Au kenan haka za ki yi mini? Ai kamata ya yi ki kwana kina farantawa wanda ya siya miki wayar rai, haba Ummi, anya kin san yadda nake jinki a raina kuwa? Anya kina jin yadda nake ji kuwa?"
Ta ce"To ni kuwa ta ya zan kwana ina faranta maka? Kenan saka ka zan yi a gaba na yi ta dariya ina cewa ina sonka ko?"
Ya ce"Hmm ke dai ba za ki girma ba".
Za ta yi magana ya ji alamar ana kiranta, ya ce"Kamar kiranki ake yi ma".
Ta ce"E na ji, rabu da su kawai".
Ya ce"Su waye?"
Ta ce"Ƙila mijin maƙociyar nan tawa ne".
Ransa ya ɓaci ya ce"Au wato kenan ma har yana da damar da zai kira wayarki kai tsaye".
Ta ce"To ai idan ya kira kai mata nake yi".
Ya ce"Ki kai mata? Kenan ma ya mayar da ke ƴar aike, to da izinin wa kike fita?"
Wata dariya ta zo mata, tunawa da tun da ya tafi sai ta nemi ƴan rakiya suke zuwa kasuwa cefane, suna tafe suna shirmensu, ita ce kan gaba wajen neman ragi, har rage murya take yi tana"Haba yayana".
Ta danne dariyar ta ce"Don dai nan maƙota?"
Ya ce"Ummi! Daga yau kar ki sake fita sai kin tambaye ni ko ƙofar gida ne, kuma na haramta wannan aron wayar daga yau, ban yarda da shi ba! Ai ba ke kaɗai ce maƙociyarta ba".
Ta ce"To shikenan".
Suka ci gaba da firarsu, can kuma sai ya tuna ai ita ce ma ta kira shi, ya fara tunanin wane ne ya saka mata kati? Ya ce"Ummi wane ne ya saka miki katin da kika kira ni?"
Gabanta ya faɗi ta rasa me za ta ce, ta ce"A cikin kuɗin cefane".
Ya ce"To wa kike kira da za ki dinga loda kati haka a wayarki?"
Ta ce"Ba ga shi na kira ka ba?"
Ya ce"Amma ai ba ki yi niyyar kirana ba, sai da na kira ki, ba zan taɓa yarda saboda ni kika saka katin nan ba".
Suka yi sallama yana jin zuciyarsa babu daɗi.
Bayan an kwana biyu ya sake kira ya ji busy, kuma lokacin wajen sha ɗaya na dare, don wacce take taya ta kwana ce take waya da saurayinta ita Ummi har ta yi bacci, har ya gaji da kira ba a gama wayar ba, ransa ya ɓaci sosai, washegari da asuba ya kira ta, tana ɗagawa a fusace ya ce"Jiya da wa kika kwana kina waya?"
Ta ce"Kwana kuma?"
Ya ce"Ke kar ki raina min hankali mana, da wa kike waya jiya!?" Ya yi maganar cikin daka mata tsawa.
Ta ce"Dama Safna ce fa da ta taya ni kwana, to wayarta babu caji shi ne ta yi waya da saurayinta a tawa".
Ya ce"Dole sai ta yi wayar? Me yasa ba ki da tunani? Yanzu ba ki yi tunanin lambarki za ta iya yaɗuwa a gari ba? Wannan ma ai shirme ne, daga yau kar na sake kiran wayarki na ji busy, ke zan kira Mama kawai ki tafi gida ki zauna har na dawo!".
Tana jin haka ta fashe da kuka, kuka na gaske har zuciyarta, don a yadda take jin daɗin sabuwar rayuwarta har titi za ta iya fita ta ɗora hannu a ka ta dinga rusa ihu idan aka ce ta bar gidanta, kusan kullum sai ta ci nama, ga kayan ciye-ciyr kala-kala, ta ci ta ƙoshi ta kunna kiɗa ta yi rawarta ga kuɗin zance da take ta tarawa, idan aka ce yau babu wannan damar ao an cuce ta, don haka cikin kuka ta ce"Don Allah ka yi haƙuri, wallahi ba zan ƙara bawa kowa wayar nan ba".
Jikinsa ya yi sanyi, ya sassauta murya ya ce"Me yasa kike yi mini haka? Me yasa ba kya jin maganata? Gabaɗaya kin fara saka mini rashin nutsuwa fa, hankalina ya yo gida".
Ta ce"Wallahi na daina komai".
Ya ce"Kenan kin fi son zaman gidan".
Ta ce"E ai dai gara ina ɗakin mijina".
Ya yi murmushi ya ce"Lallai ashe dai Ummi an fara hankali har an fara sanin muhimmancin zama a gidan miji".
Ta yi dariya, daga haka suka yi fira sannan suka yi sallama.
Ummi ta yi shiru tana tunanin mafita, da Farida ta shigo ta sanar da ita halin da ake ciki, ta ƙara da faɗin"Ni dai a tunanina gara na yi blocking ɗin shi kawai, idan ma ya kira wani ɗan'uwanmu ya ce ba ya samuna sai na ce masa wayata ce ta lalace".
Farida ta ce"A'a gaskiya ba ki yi tunani mai kyau ba Ummi, a haƙura kawai a daina waya a nan ɗin, ni zan saka bazawarina ya siya miki wata wayar, da sabon layi sai a dinga yi ta nan".
Ummi ta ji daɗi sosai ta ce"Shikenan haka ne daidai kuwa".
Farida ta ce"In sha Allah yau ɗin nan zai zo ya kawo ta".
A ranar ta faɗawa duk masu waya a wayarta halin da ake ciki, ta ce kowacce ta sanarwa saurayinta kar ya sake kiran layin nan, sai an kawo sabon layi, haka kuwa aka yi, da daddare da bazawarin Farida zai zo sai ga shi da sabuwar waya mai ɗauke da sabon layi, babban abun murna a wajen Ummi shi ne wayar babba ce ba keypad ba, amma sakan ce, Ummi ta kasa ɓoye farincikinta sanda Farida ta kira ta falo da ya zo, tana ta washe baki riƙe da wayar ta ce"Wai da gaske wannan wayata ce Farida?"
Farida ta ce"Ga shi kuwa".
Ta daka tsalle tana cewa"Ashe kuwa zan fara chart".
Alhaji Sadi ya ji wani abu ya caki zuciyarsa silar motsawar da sassan jikinta suka yi, sanadin tsallen da ta yi, har bai san sanda ya shagala da kallonta ba.
*** ***
*RANAR KUKA!*
BY
*SADIYA ABDULRAZAƘ*
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR Sandar dukan uwargida Zuciyar mace Miji goma... Iya ruwa... Wani auren Matar shige... Da walakin Wutar ƙaiƙayi Alhakin so ***