PAGE 6
Ummi tana ta zumuɗi ta rusuna ta ce"Alhaji na gode fa, Allah Ya saka da alkhairi Ya ƙara arziƙi".
Ya washe baki ya ce"A babu komai, wannan ai ba komai ba ne, ni ne ma da godiya" Ya ƙarasa yana kallon Farida, ita kuwa ta kashe masa ido, saboda su kaɗai suka san wainar da suke toyawa a wannan falon na Ummi, don haka don an siya mawa waya ba komai ba ne.
Suka gama zance ya tafi, zuciyarsa cike da tunanin Ummi, ya yi mamakin kyaunta da ƙuruciyarta, tun da yake zuwa gidan bai taɓa ganinta ba sai yau, ya fara tunanin ko mijinta wane irin dole ne sa yake wasarere da gidansa da iyalinsa har haka? Yarinyar ta burge shi sosai, sai ya ji ina ma ita ce a matsayin Farida da ya more sosai, akwai matan aure da dama da yake mu'amula da su, to amma ita wannan ta zo ne ta hanyar wata abokiyar masha'arsa wacce kuma ita a haukanta zato take yi zai aure ta, saboda haka dole sai dai ya takawa zuciyarsa burki, ya haɗiyi tsinkakken yawu.
A daren nan Ummi ba ta kwanta bacci ba sai da ta saita whatsApp, sai ta kasa yi wa ƴan'uwanta magana saboda kar labarin ta fara chart ya je kunnen mijinta, ƙawayenta kawai ta yi wa magana suka gaisa, wayar tana kusa da kanta a haka ta yi bacci tana jin kamar wannan Alhajin wata duniya mai faɗi ta ɗauka ta ba ta kyauta. Tun daga ranar aka rabawa samari sabuwar lamba aka ɗora daga inda aka tsaya, sai ta bi duk ta yi block ɗinsu ta ƙaramar wayar tata.
GIDAN ABBA
Haka Aisha ta fara sabawa da sabuwar rayuwar zama da surukanta, gefe guda kuma tana rainon cikinta, idan suka dafa abin da ranta ba ya so tan ji tana gani babu mai cewa ta dafa wani abun, ko kuma a ce me za ta ci? Sai dai idan Mama ta fita yawonta ita ma ta fita ta samowa kanta wani abun, idan da daddare ne kuwa sai dai ta kwana da yunwa. Kullum suna waya da Abba, ba ta taɓa yi masa ƙorafi akan abinci ba, ko kuma yanayin zaman gidan, kullum ce masa take lafiya ƙalau, sanda ya fara turo kuɗi ranar tana zaune ta ga ya turo dubu talatin ya ce ta ɗauki dubu biyar ta bawa Mama sauran, ta yi masa godiya, dama tana son zuwa gidan babarta a ranar, sai ba ta faɗawa Mama ya turo kuɗin ba kawai ta bar shi sai ta ciro sannan ta sanar mata, ta gama shiryawa za ta tafi ta fito ta ce da Mama"Mama a ɗan ba ni mukullin gidan nan, ina so na far biyawa ta can na share shi".
Mama ta ce"To ma su abu da abunsu, amma ni dai a ganina babu yadda za a yi Ashiru ya dinga kwana a cikin bola a ce ba ya shara, kodayake gidanki ne kina da iko da shi".
Aisha ta kau da kai ba ta ce komai ba, don ko me za ta ce ita kam sai an ba ta mukullin nan ta je ta ga yadda gidanta yake. Har Mama ta tashi ta ce"Au! Na manta ai kuwa yau Ashiru da ya dawo bai ba ni mukullin nan ba, ƙila ya manta, yana jikinsa, dama ganin kayan amana ne shiyasa na ce da safe idan ya dawo ya dinga ba ni".
Aisha ba ta ji daɗin jin haka ba, saboda ta yi niyyar zuwa, ta rasa me za ta ce ma, Mama ta ce"Aisha kin yi mini tsaye, ko dai ba ji yarda da ni ba ne?"
Ta ce"Ba haka ba ne, ta ya zan ƙi yarda? Kawai dai na saka ran zuwa gidan ne".
Mama ta ce"To bari na kira shi na ji".
Ta ɗauki wayarta ta kira lambar Ashiru, ya ɗauka cikin muryar bacci Mama ta ce"Kai kana ina?"
Ya ce"Ina gidan Abba".
Ta katse wayar tana cewa"Ba ni da kati, kati ma ya fara gagarata, Abba shiru kamar an shuka dusa, yau ko ba ka kawo ajiyar matarka ba ai iyayenka suna da haƙƙi a kanka".
Ta kalli Aisha ta ce"Kin ji yana can gidan ma, sai ki haƙura sai gobe kya je, tun sa ai ba kya yi shara yana ciki ba".
Aisha ta ce"To sai anjima".
Tana fita daga gidan kawai zuciyarta ta fara raya mata ta je ɗin, tun da ita da gidanta zai hana ta shiga ne? Ai tun da gari ya waye ba ta ga amfanin zamansa ba, sai ya fice ya ba ta waje ta yi shararta, don haka ta ɗauki hanyar gidanta, tana hanya Abba ya kira ta, ta ɗaga suka ƙara gaisawa ya ce"Ko bacci kike yi ma na tashe ki?"
Ta ce"A'a ka ga ni ina hanya ma".
Ya ce"Ok kin fitan kenan, ai na zata sai yamma za ki je".
Ta ce"Tunani na yi ya kamata na je can gidanmu na yi shara, tun da ka tafi ban je ba".
Abba ya ce"Uhm! Ki ce dai kawai kewata ta motsa".
Ita ma ta yi dariya.
Ya ce"To idan kin je ki yi wanka ki yi mini kwalliyar nan irin wacce kike yi ta dare, zan kira ki vedio call, kai ni fa ina ga duk sati ma ya dace ki dinga zuwa kina yi mini haka".
Ta ce"Kar ka damu bari na ƙarasa".
Tana ƙarasawa ƙofar gidan ta ga maƙociyarta ta fito daga gida, suka gaisa taba ce mata"Aisha wallahi na yi kewar maƙobtaka, kina can abinki, don ma dai har yanzu gidan ba ya rabo da motsi".
Aisha ta ce"Ai dama tun da ƙaninsa yana kwana a ciki".
Samira ta ce"Yana shagalinsa dai za a ce, wallahi Aisha ban so kika yarda da wannan tsarin ba, me zai hana ki yi zamanki a gidanki? Ai ga shi yanzu zai ɓata miki sunan gida".
Aisha ta ce"Ban gane ba, wani abun ya yi?"
Samira ta ce"Yake yi dai za ki ce, sai dai mu ce Allah Ya kyauta".
Aisha da mamaki tare da fargaba ta ce"Me kike nufi ne? Wani abun Ashiru yake yi mana a gidan?"
Samira ta ce"Dole na faɗa miki gaskiya don idan na ɓoye ban kyauta miki ba, to dai yaron nan abokansa yake tarawa su dinga shaye-shaye, warin wiwi har gidana, musamman da daddare don akwai ma sanda har mijina ya yi musu nasiha amma ba su fasa ba, to cikin kwana biyun nan sai likafa ta ci gaba, don wallahi sun fara kawo mata, wuff za ki ga yarinya ya shige".
Aisha ta daskare da wani irin ɓacin rai, Samira ta ɗora da faɗin"Ba zan ɓoye miki ba, ina zargin har girki ma suke yi, don ina jin kwarafniya da kwanuka, wataran har ƙamshin girki, ga kuma murya mace, ƙila girki take yi masa".
Aisha ta ce"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! A gidan nawa?"
Samira ta ce"Sai haƙuri, amma gaskiya babu daɗi, kuma idan kin san za ki iya to fa ya dace ki yi wa tufkar hanci, don wannan ke suke cuta".
Aisha ta ce"Shikenan Samira na gode, zan yi maganin abun in sha Allah".
Samira ta tafi, ita kuma ta fara ƙwanƙwasa ƙofar gidan da ƙarfi.
Ashiru dake tsaka da baccin shi mai nauyi, saboda cajin da ya yi wa kansa ya ji bugun Aisha kamar za a ɓalle ƙofar, ya yi tsaki yana cewa"Ko wane karfan ne haka?"
Jin bugun ba zai ƙare ba ya sa shi fitowa yana cewa"Wai dalla wane ɗan wahalan ne? Kashe mana ƙofar za a yi?"
Yana buɗewa ya ga Aisha, ta ƙara murtuke fuska tana kallon yanayin da yake ciki na maye, dama can jininsu bai haɗu da juna ba, ko gaisuwa ba ta haɗa su, shi yana ganin ya girme ta ita ya kamata ta dinga gaishe shi, ita kuma tana ganin ba za ta shiga sabgar mara kamun kai ba, don kowa ya san yana shaye-shaye, sannan a ganinta tun da ita matar yayansa ce ai ya kamata ya gaishe ta, yana haɗe rai ya ce"To ya aka yi!?"
Ta ce"Ni da gidana ka ce mini ya aka yi? Shara na zo yi".
Ya ce"Amma ai sai ki sanar za ki zo".
Ta ce"Babu wanda zai kafa mini wannan dokar".
Ya koma ciki, babu jimawa ya fito ta ce"Ina mukullin?"
Ya miƙa mata ya wuce yana ƙunƙuni.
Ta shiga tana bin gidan da kallo, tsakar gidan nan kaca-kaca, duk ƙura da ledoji, ga guntayen sigari a buɗe ta ga ɗakin gadon ta tura ta shiga, wari maza ya buge ta, zanin gadon nan ya haɗa dauɗa, har da wasu gajerun wanduna guda biyu baƙiƙƙirin da su, sigari har kan mudubinta, can ta ga wata rigar baccinta yashe a ƙasa, kayan baccinta da suke can ƙasan sif me ya fito da ita? Me ma zai sa a buɗe mata sif? Irin sif ɗin nan ne da babu mukulli dama shiyasa ba ta rufe ta cire mukullin ba, ranta ya kai ƙololuwar ɓaci, ta ɗakko waya ta kira Abba, ya a ɗagawa kawai sai ta fashe da kuka, ta kasa cewa komai, hankalinsa ya tashi ya ce"Aisha mene ne ya faru? Me aka yi miki?"
Tana kuka ta kwashe komai ta faɗa masa.
Sam bai yi mamaki ba don dama ya yi zargin za a iya hakan, tun da ya san halin ƙaninsa, kawai don ba shi da yadda zai yi ne ya bari Aisha ta bar gidan, murya a sanyaye ya ce"Ya isa haka Aisha, don Allah ki kwantar da hankalinki, wannan fa ba wata matsalar da za ki ɗaga hankali har kina kuka ba ce, ciki ne a jikinki fa, bai kamata kina damuwa ba..."
Ta katse shi da faɗin"Au yanzu wannan ce ba matsalar da za a damu ba? Yanzu wannan ba cin zarafi ba ne? Don wulaƙanci har ya kawo mata suna kwana suna yin girki a kitchen ɗina? Wallahi ba zai yiwu ba!".
Ta sake rushewa da kuka, dama mai neman kuka ne aka jefe shi da kashin shanu, don haka kukan ba ɗaya take yi ba take yi har da na kewar mijinta da kewar gidan aurenta, ga kuma takaicin zama a gidan sutukanta, yana ta yi mata magana ta ƙi kula shi, kuma ta ƙi tsayar da kukan, ƙarshe ma sai ta kashe wayar, ta fito tsakar gida ta zauna a kujerarta ƴar tsuguno ta ci kukanta ta gode Allah, sannan ta ba wa zuciyarta haƙuri, ta tashi ta leƙa falon nan ma ta ga kayan maza riga da wando, ga kafet ɗinta wani waje ya ƙone da alama maganin sauro ne aka kunna ya cinye ya samu wajen, kitchen ɗin nan kace-kace, sai tsami yake, kwanukanta da tukwane baje a ƙasa, duk babu wanki, ƙwalla ta zubo mata ta share, sai lokacin ta cire hijjabinta ta fara gyara gidan, ita da ta yi niyyar har bacci za ta yi a gadonta, sannan ta tashi da yamma ta yi wanka ta tafi gidan nasu, sai ga shi gabaɗaya ma ƙyanƙyamin gadon take ji, ta kwashe zanin gadon ta ajiye a gefe, ta yi wanke-wanke, ta yi komai ta shiga maƙotansu ta samo garwashi ta yi wa gidan, an fara kiran sallar azhar, ta duba randar babu ruwa, ta ɗauki bokiti ta samo a maƙota, ta yi wanka ta ciro kaya a sif ta saka, ta yi alwala ta yi sallah, sai ga wata maƙociyarta ta aiko mata abinci da yake ta faɗa mata shara ta zo yi, ta ci ta ƙoshi, sai a lokacin ta ɗakko wayarta wacce Abba har ya gaji da kira, ƙarshe ya yi mata tex ya ce"Aisha na fi ki damuwa da damuwarki fa, a yanzu haka na fi ki shiga ƙunci sosai sanadin abin da ya faru, kamata ya yi ki ɗauki wayata mu tattauna mu samu mafita ba wai ki yi fushi da ni ba".
Ta ajiye wayar, can kuma sai ta ɗauka ta kira shi, ya katse ya kira ta, tana ɗauka ya ce"Kina ina?"
Ta ce"Ina can".
Ya ce"Ina?"
Ta ce"Gidan mana".
Ya ce"Kin gama kukan?"
Ta yi shiru. Ya ce"Don Allah ki yi haƙuri Aisha, shi ne kaɗai abin da zan ce miki, duk wanda aka bawa haƙuri an san an cuce shi ne, kowane aure akwai ƙalubalensa, ina so ki ɗauki wannan matsalolin da suke faruwa a matsayin namu ƙalubalen, komai zai wuce in sha Allah, watarana sai labari".
Ta ce"Allah Ya sa".
Ya ce"Yanzu mu yi shawara, ya kike ganin za a yi?"
Ta ce"Ni dai kawai a san yadda za a yi, na dawo gidana, ina son zama a ɗakina gaskiya".
Ya sauke numfashi ya ce"Ba lallai Mama ta yarda ba, ni da cewa na yi a rufe gidan kawai duk sati sai ki dinga zuwa kina dubawa".
Ta ce"Wannan ba dabara ba ce, idan aka lura babu mai kwana a gidan komai zai iya faruwa".
Ya ce"Haka ne, to cikin ƴan'uwanki maza fa? Ba za a samu wanda zai dawo nan da kwana ba?"
Ta ce"Kuma kana ganin Maman za ta yarda?"
Ya ce"Sai sa'a".
Ta ceTo ko dai kai ma ba ka so na dawo nan ɗin?"
Ya ce"Wallahi ina so, Aisha nutsuwarki fa ita ce tawa, to kin san shi sha'ani idan aka ce maganar iyaye ce dole sai ka bi komai a hankali, idan ba haka ba ka samu matsala, ki bar ganin mu ne da gaskiya, wallahi idan na bijire mata tsaf lamarina zai taɓarɓare".
Ta ce"Haka ne".
Ya ce"Amma zan yi magana da ita dole, a san abun yi, yanzu dai fatana ki kwantar da hankalinki kawai".
Ta ce"Shikenan ya wuce".
Ya ce"To Alhamdulillah! Yanzu zan samu ki yi mini kwalliyar?"
Ta ce"A'a".
Ya ce"Haka kai tsaye? To shikenan hakan ma na gode, ni dai tun da kin haƙura hankalina ya kwanta ai".
Daga haka suka yi sallama, ta tashi ta fito ta rufe gidan, sai da ta tsaya a hanya ta ciro kuɗin da ya turo sannan ta wuce gidan mahaifiyarta.
*** *** Follow this link to join my group ***
*RANAR KUKA*
BY SADIYA ABDULRAZAK