Ranar kuka

PAGE 7

by @sadiyaabdulrazak954

hausawa sunce wai da tsohuwar zuma ake magani, kun sani na sani cewar duk inda rayuwa tayi gaba to dai squre one din nan ake dawowa, iyaye da kakaninmu sunyi rayuwarsu ne cikin salama babu irin cuce-cucen wannan zamaninbda ala tabbatar hatta a kwanukan da muke cin abinci yanzu muna iya gamuwa da wasu cututtukan._

_To me zai hana ba zamu kare kanmu daga hakan ba? USWAN COLLECTIONS kamfani ne dake sarrafa dukkan wani nau'in mazubin abinci da ma sauran kayan amfani da sassaken itace wato wood, cikin tsari in na zamani da zai dauki hankalin ka kuma ba tare da fargabar komai ba, akwai plates, jugs, bowls, flasks da ma kayayyaki da yawa wanda zaki siya da kudinki kalilan, babu tsada, na maimata muku babu tsada! Zaku same su a farashi me sauqi Bugu da qari wadanda suke buqatar kayanmu kuma bazasu iya affording at onece Muna da adashen gata wanda zaku Malaki kayanku kaman kyauta 👇🏻 Open this link

Ba ta ɓoyewa mahaifiyarta komai ba ta karance mata matsalolin da take ciki, da abin da ya faru yau ɗin, ran Umma ya ɓaci ta ce"To wai akan wane dalili za a hana ki zaman gidanki?"

Aisha ta ce"Wallahi babu, kawai saboda ta ƙuntata mini ne, ni fa na gaji". Ta faɗa kamar za ta yi kuka

Umma ta ce"A'a Aisha, kar ki ce kin gaji, ki daure duk rintsi ki riƙe aurenki, ki zauna da mijinki, ni fa hango miki zaman gida nake yi, a wane gidan za ki zauna? Ko za ki iya zama da babanki ku biyu a gida?"

Ta girgiza kai alamar a'a.

Ta ce"To shiyasa nake ce miki ki daure, amma zancen gidan nan gaskiya dole a yi shi, ba zai yiwu ya dinga kai muku mata gida ba, don ma ba ya ɗauke-ɗauke da tuni ya yashe gidan tsaf".

Aisha ta ce"To ai shi komai sai ya ce maganar Mama ce, yanzu ma bari ki ga ba lallai fa ya ɗauki wani mataki ba".

Umma ta yi shiru tana tunanin mafita, ta ce"Ga shi ni nan ɗaki ɗaya ne, da sai ki kwaso kayan sakawarki da na kitchen ɗin ki ajiye a nan, to kin ga ni ma a matse nake". Ta yi maganar tana kallon yanayin ƙaramin ɗakin nata dake cunkushe da kaya.

Sannan ta ce"Shi kuwa babanki da mutumin kirki ne da sai ki kai can, to na san kwashewa zai yi ya siyar, kai Allah dai Ya kyauta".

Aisha ta ce"Amin".

Umma ta ce"Sannan maganar abinci, Aisha ciki ne da ke ba zai yiwu ki dinga zama da yunwa ba, ai kowa ya san mai ciki ba komai take iya ci ba, ni a ganina kamar yadda suka ware miki ɗakinki ya kamata su ware miki girkinki, ki kwaso tsirarun kayan kitchen ɗinki ki dinga girkinki".

Ta ce"To zan yi shawara da shi".

Haka suka ci gaba da tattaunawa, dayake ita ce da girki ranar ta saka mata tuwo ta ci, sai bayan magriba ta tafi, ta ba ta dubu biyu a cikin kuɗinta.

Mama tana zaune Abba ya kira ta a waya, suka gama gaisawa ya ce"Mama ke kika ce Ashiru ya dinga kwana a gidanmu...".

Ta katse shi da faɗin"Ni na ce mana, sai me ya faru?"

Ya ce"A gaskiya abin da yake yi a gidan nan bai dace ba, kuma ba zan lamunta ba".

Umma ta tashi tsaye tana gyara zani ta ce"To Allah Ya kawo mu, me kuma ya yi?"

Ya kwashe komai da ya faru ya sanar mata, Mama ta hau salati har da dafe ƙirji ta ce"Na shiga uku! Yanzu sharrin da za ta ƙullawa ɗana kenan? Me na yi wa matarka da zafi haka? Bayan duk zaman haƙurin da nake yi da ita shi ne za ta saka mini da sharri?"

Abba ya ji babu daɗi, ya ce"Haba Mama, wannan fa babu sharri a ciki..."

Ta katse shi da faɗin"Idan kai ta shanye ka ni ba ta isa ba! Kenan ka zaɓi mace akan ɗan'uwanka na jini, tun da har za ta haɗa ƙarya don ta raba ku, to wallahi ba zai yiwu ba".

Duk yadda ya so ta saurare shi ta ƙi, ƙarshe sai haƙuri ya fara ba ta, ya kashe wayar ya bar shi a idan ta huce sai ya sake kira su yi maganar.

Aisha ba ta san wainar da aka toya ba, ta dawo ta shiga gidan da sallama, ta ji shiru Mama ta ƙi amsawa, kuma tana bakin murhu tana girki, ta ƙarasa ta ce"Mama sannu da aiki".

Mama ta juyo ta kalle ta sai ta ja dogon tsaki ta ci gaba da abin da take yi.

Aisha tun da ta ga haka ta san abin da Mama ta taka, don haka ta kama kanta, ta ciro kuɗi ta miƙa mata tana cewa"Ga shi nan, Abba ne ya turo muku ta account ɗina".

Mama ta karɓa tana juya kuɗin ta ce"Ya turo mana ko ya turo miki? Ai tun da nake da ɗana bai taɓa ba ki kuɗi ya ce ki kawo mini ba".

Ta ce"To ni dai ke ya ce na bawa".

Ta juya za ta tafi Mama ta ce"Ke Aisha ashe ɗazu gidan naku kika je? Kuma hakan bai ishe ki ba sai da kika kira mijinki kika kitsa masa sharri? Ke dai burinki ki raba zumunci? Ki gan mu da ɗanmu ki ga Ashiru da ɗan'uwansa ki ce za ki raba? To wallahi sai dai ke da kika zo daga baya ki haƙura ba dai mu ba! Kuma kwanan Ashiru a gidan ɗan'uwansa yanzu ma aka fara! Ai sai ki bari ya kwanta ya mutu idan gidan ya shigo a rabon gadonki sannan ki hana ɗan'uwansa shiga, yanzu kuwa ba ki isa ba!".

Aisha hawaye ya sakko mata ta ce"Mama akan me zan yi masa ƙarya? Mene ne ribata a ciki? Wallahi ya aikata komai, ga shi ma na gani da idona kuma ƴan'unguwa sun tabbatar da yana kai mata gidan".

Mama ta ce"Ko a gaban Allah ba ki da hujja, idan ma aka kai ki kotu sai an yanke miki hukuncin ƙazafi! Kuma na ce kwana a gidan nan yanzu ma ya fara, idan kin ga dama ki kwashe kayanki daga gidan ki kai gidan babanki!".

Baba ya fito yana cewa"Saratu! Maganar nan ba ta ƙare ba ne?"

Mama ta ce"A ina za ta ƙare? Wannan ƙazafin za mu zubawa ido?"

Baba ya ce"Ke Aisha kina ina? Me ya kai ki gidan ne?"

Kamar kar ta yi magana sai kuma ta ce"Shara na je yi".

Ya ce"To ni daga yau na haramta miki zuwa gidan nan, a matsayina na uban Abba kenan".

Ta haɗiyi wani yawu muryarta tana rawa ta ce"Na ji, amma ya daina shigar mini ɗakin gado, gadona na sunna ne" Ta rushe da kuka tana shigewa ɗakinta.

Mama ta fara salati tana cewa"Laaa! To ka ji fa Malam, ka ji faɗa mana take gadon sunna, suna raya sunnaa kan gado da ɗanmu".

Baba ya ɗauki salati shi ma ya ce"Kaico! Kaico rayuwar wannan lalataccen zamanin" Sai ya juya ya koma ɗaki.

Mama ta bi shi tana cewa"Ka ga yanzu ma kuɗi ya turo ta bankinta ya aiko ta ba kawo mana, ba mu da ƙimar da zai ba mu idan da rabonta a ciki ya faɗa a bata, sai dai ya ba ta ta ba mu rabonmu".

Baba ya ce"Kayyasa! Amma dai Abba bai morewa aure ba sam!".

Mama ta ce"Ai wani abun duk da saka hannunka, ka na kallo dai..."

Ya katse ta da faɗin"Ina ji dai, da wane idon zan kalla?"

Ta yi guntun tsaki ta ce"Kai dai ba ka taɓa cin ribar zance. Yanzu duk wani yaƙin ceton yaron nan ba ni kaɗai ce nake yi ba? Kai ba za ka dinga saka baki a maganar ba? Komai sai ni, ai nan gaba ni za a dinga zagi a gari, amma idan muka haɗa ƙarfi da ƙarfe sai ka ga komai ya zo da sauƙi, kuma ku iyaye maza an fi ganin gaskiyarku, mu mata babu damar mu ga matsala mu daƙile sai a ce mun takurawa suruka".

Ya ce"To yanzu ya kike so na yi?"

Ta ce"Kai ma ka yi masa gargaɗi ka nuna ka ji zafin ƙazafin da matarsa ta yi wa yaron nan, sannan zancen turo kuɗin ma ka yi magana ba zai yiwu ya dinga turo mata dukiya tana kalmashewa ba".

Baba ya ce"To idan kin ce haka kina da banki ne? Ko ni ina da shi?"

Ta ce"Idan ba mu da shi ai akwai mau POS ni har gara ya dinga tura musu ina zuwa ina karɓa, ko kuma ma kawai na je na buɗe bankin".

Ya ce"Shikenan kuwa! Maza kira mini shi".

Ta ɗauki waya ta kira shi, yana ɗagawa ya ce"Abba, kai Abba kana jina?"

Abba ya ce"Baba ashe kai ne, ina wuni?"

Baba ya ce"Babu wani ina wuni da za ka faɗa mini, ni ba gaisuwa na kira ka na ji ba".

Abba jikinsa ya yi sanyi ya ce"A yi haƙuri Baba, me ya faru?"

Baba ya ce"Meye ma bai faru ba!? Ashe kai yanzu matarka ta fiye maka ni da mahaifiyarka da ɗan'uwanka?"

Ya ce"Haba Baba, ya kamata ku yi wa yarinyar nan adalci, kun san halin Ashiru fa".

Baba ya ce"To zo ka yi mai kankat kawai ka rufe ni da duka, tun da ni sa'anka ne ina faɗa kana kana faɗa!".

Abba ya ce"Ka yi haƙuri".

Baba ya ci gaba"To wannan yarinyar ba ta isa ta rusa mana tsari ba, dole ɗan'uwanka zai dinga kwana a gidan nan, sannan wace lalacewa ce ta same ka da za ka sako mana kuɗi ta asusun matarka? Saboda ta ƙara raina mu ta san ba mu da amfani da a wajenka ko?"

Ya ce"Subhanallah! Baba ba haka ba ne wallahi, na ga ita ce mai account ɗin shiyasa".

Ya ce"Tun da ita ka mayar mutum ai ka buɗe mata akawun ɗin, amma ga uwarka ba ka buɗe mata ba, to gobe za ta je ta buɗe don haka wannan kuɗin na buɗe account ne bayan ta buɗe sai ka turo wasu ta asusunta".

Abba ya ce"To babu damuwa".

Mama ta karɓi wayar ta ce"Abba!".

Ya ce"Na'am".

Ta ce"Nawa ka ba ta ita Aishan?"

Ya ce"Dubu biyar".

Ta ce"Hmm dubu biyar? Ita da ba ita take siyan kayan abinci ba, kodayake Muhibba ta ce tana siyan wani abun ta shiga ɗaki ta ci idan ta raina girkin gidan".

Abba ya ce"Ni dai Mama ku yi haƙuri don Allah maganar nan ta wuce haka".

Mama ta ce"Ai kai ne za ka so ta wuce ko a ci gaba da yinta, amma gaskiya ka gargaɗe ta aka fita siyan abinci da take yi, iya ƙarfinmu muke dafawa, idan ba za ta ci ba ta haƙura".

Ya ce"Mama na san ba rainawa ta yi ba, ai yanayin jikin nata ne, ɗanɗanon bakin ya canza, shiyasa".

Mama ta ce"Au haka ɓa za ka ce? To shikenan ta ci gaba".

Ta kashe wayar ta ajiye.

Suna gama waya da Mama ya kira Aisha, suka gaisa ya ce"Kin dawo?"

Ta ce"E ban daɗe da shigowa ba".

Ya ce"Don Allah Aisha komai ya wuce, kar a sake tada zancen nan".

Ta ce"Kenan a zuba masa ido ya ci gaba da abin da ya ga dama a gidan?"

Ya ce"Komai lokaci ne, ki yi haƙuri, yanzu lallaɓa Mama nake yi, so nake na san abun yi, kin san ba zan taɓa yarda a ce ki dawwama a nan ba, dole za ki biyo ni, amma sai mun bi komai a hankali".

Ta ce"To shikenan".

Ya ce"Ya babyna? Da fatan dai kina cin abinci sosai ko? Yaushe za ki fara zuwa awo ne?"

Ta ce"Sai wani watan in sha Allah!".

Ya ce"Allah Ya kaimu".

Suka ɗan yi shiru, sannan ya ce"Kina ci kina ƙoshi ko? Yau me da me kika ci?"

Ta ce"Yanzu na gama cin tuwo a gidan Umma".

Ya ce"Ma sha Allah! Amma yanzu da muka yi waya da Mama ta faɗa mini abin da ban ji daɗinsa ba".

Aisha gabanta ya faɗi, ta ce"Me ta faɗa maka?"

Ya ce"Ta ce kina zaɓen abinci, sai a dafa ki fita waje ki siyo, haba Aisha me yasa kike haka? Wani ya ga kin je siyan abinci ai sai ya zarge mu ni da iyayena".

Ta ce"Wallahi ban raina musu ba, kawai dai yanzun ba komai nake iya ci ba, kuma dam ni ina son magana da kai".

Ya ce"To ina jinki".

Ta ce"Gaskiya ni fa ina ga zan fara yin girkina, zan kwaso wasu kayan kitchen ɗin nawa na dinga girkina kamar hakab zai fi".

Ya ce"E kuma fa kin kawo shawara, kin ga sai ki dafa abin da ranki yake so, haka za a yi, yanzu ki bari zuwa jibi in sha Allah zan turo miki kuɗi sai ki siyo abin da kike buƙata".

Ta ce"To na gode Allah Ya ƙara buɗi".

Ya ce"Amin, yau kin yi aiki kin gaji ki kwanta ki yi baccinki kin ji".

Suka yi sallama ta kwanta.

Har bacci ya fara fizgarta ta fara jiyo hayaniya sama-sama, Ashiru ne, tun da ta tashe shi daga baccin nan sai yanzu ya shigo gidan, Mama ta tare shi da maganar, ahi ne ya fara hayagaga.

Ya zo ya doko ƙofar ɗakin Aishan yana cewa"Ke kina ina!?"

Aisha ta ji gabanta ya faɗi, sannan ɓacin ranta ya dawo sabo, kamar ta yi banza da shi sai kuma ta kasa jurewa ta zo ta buɗe, ta ce"Ga ni, me ya faru?"

Ya ce"Ni za ki yi wa sharri!? Gidan uban waye da za ki hana ni kwana a ciki?"

Ta ce"Gidan mijina ne, kuma kai ba ka isa na tsaya musayar yawu da kai ba, kai ka san ka aikata, don haka ka je kai da Allah! Kuma idan ka sake hawa gadona ban yafe maka ba!".

Daidai nan Mama ta ƙaraso ta ce"Au Allah? To sannu uwar shi, ke kika haife shi da zai ɗaiɗaice don ba ki yafe masa ba?"

Ashiru yana huci ya ce"Mama yarinyar nan ta fara zaƙewa fa, ki bar ni da ita na saita ta a kan layi".

Mama ta ce"A'a ƙyale ta, ai ba laifinta ba ne, ɗaure mata ƙugu aka yi, dama ta samu".

Aisha ta kasa cewa komai, ta koma ta rufe ƙofarta, ta zauna hawaye ya fara zubo mata, tana jin Ashiru yana ta zaginta Mama tana tausar shi, har ya gama ya tafi, da ƙyar ta samu bacci mai cike da baƙinciki ya ɗauke ta.

*** ***

*RANAR KUKA!*

BY

*SADIYA ABDULRAZAƘ*

*FIRST CLASS WRITERS*

MARUBUCIYAR Sandar dukan uwargida Zuciyar mace Miji goma... Iya ruwa... Wani auren Matar shige... Da walakin Wutar ƙaiƙayi Alhakin so ***