PAGE 8
GIDAN SHAMSU
Tun daga ranar Ummi ta samu abun yi, wuni take tana chart da ƙawayenta, hotuna kuwa kaf sababbin kayanta babu wanda ba ta saka ta yi hoto da su ba, hotonta kamar hauka a wayar, ta samu wani hotonta mai kyau ta ɗora a dp, ɗan kuɗin da take tarawa na masu zuwa zance a ciki take zara tana saka data, idan ta duƙufa ta fara kallon tiktok ko yunwar cikinta ba ta ji, sai dai idan ba ta da caji shi ne za ka ga ta tashi ta yi komai na gidan a kan lokaci, jin wayar nan take yi tamkar rayuwarta, don ba ta san daɗin babbar waya ba sai yanzu.
Cikin haka ne ta ga an saka ta a wani group mai suna ƴan zamani, ba ta san wanda ya ba da lanbarta ba, ta dai ganta a ciki ne kawai, ta shiga duba firarsu, sai ta lura babu matan aure duk ƴan'mata ne da samari ake ta fira, sai firar tasu ta birge musamman da ta ga an yi wani program na masoya, aka haɗa wata ƴar drama tsakanin wata da wani, kamar masu soyayyar gaske sai musayar kalaman soyayya suke yi, abun ya burge ta matuƙa, can zuwa dare ta ga wani admin ya fito ya yi tagging ɗinta ya ce"Na ga mun yi baƙuwa, kuma ba ki fito kin gabatar da kanki ba, ki turo hotonki tare da cikakken sunanki da nike name, sannan da sunan garinku da unguwa".
Gaban Ummi ya faɗi, ta shiga tunanin ta tura ko kar ta tura? Sannan ta faɗa musu tana da aure ko ta yi ƙarya? Ta kasa raba ɗayan biyu, amma abin da ta sani ƙaunar zaman group ɗin ta shiga ƙasan zuciyarta, gaskiya idan aka cire ta an rage mata jin daɗi, sai dai kuma ba ta sani ba ko suna buƙatar matar aure, sai wata dabara ta faɗo mata, ta nemo lambar wanda aka gama program da shi mai suna Safwan one love, ta yi masa sallama, ta yi sa'a yana online ya duba babu jimawa ya amsa, ta rubuta masa cewar"Ni ce baƙuwar group ɗinku, yau na shigo, don Allah mene ne ƙa'idar group ɗin? Amma dai babu matan aure ko?"
Safwan ya ba ta amsa da cewar"Idan kika gabatar da kanki za a turo miki dokokin gidan, kuma babu matan aure, me zai kawo matar aure cikin samari haka?"
Zuciyarta ta tsinke, har tana ji a ranta wannan auren takura ne a gare ta, don zai hana ta more rayuwarta, sai zuciya ta ba ta shawarar ta yi ƙaryar ba ta da aure, tun da dai ai abu ne na waya ba zuwa gidanta za a yi a gani ba, kuma ita ba soyayya za ta yi da wani ba.
Ta mayar masa da amsa ta ce"Ok, dama na ga mata da maza ne shiyasa na tambaye ka, na gode".
Ta koma cikin group ɗin, ta zaɓo wani hotonta mai shegen kyau, da mayafi a jikinta ta yi shi tana murmushi har haƙoranta sun bayyana, sannan ta gabatar da kanta, kuma ta saka har garin da take da unguwa, ta tura.
Nan da nan aka fara comments ana ma sha Allah, admin ya turo dokokin gidan, ta fara dubawa, cikin dokar har da ta tura Friday pics, duk ranar Juma'a kowa sai ya tura hotonsa, mutane uku da hotonsu ya fi na kowa kyau suna da kyautar data, sannan kuma duk bayan wata uku akwai taron group da ake yi, kuma wajibi ne ka je, idan aka yi taro uku ba ka je ba za a cire ka daga group ɗin, idan auren wani ko wata ya tashi ana gaɗa gudunmawa sannan ana haɗa paty don taya shi murna shi ma dole ne kowa sai ya halarta, idan sunanka ya fito a list ɗin wanda za su yi program ba za a karɓi wani uzuri ba dole sai ka yi ko ka ba da tarar dubu ɗaya, duk wanda ya yi kwana uku bai yi magana a group ba kuma yana hawa online zai gan shi a waje, daga ƙarshe aka ce"Amincewa da duka dokokinmu shi zai ba da tabbacin zama cikakken mamba a group ɗin nan, kin amince?"
Ummi ta ce"Na amince".
Nan aka fara turo mata stikers wasu suna janta da fira. Tana fitowa daga cikin group ɗin ta ga lambaobi a jere duk an yi mata sallama wasu kuma stika, abun ya ba ta mamaki, ta ga Safwan one love ma ya ƙara yi mata magana, sai ta fara duba duba nashi saƙon ce mata ya yi"Ashe wannan hoton na dp ke ce".
Ta ce"E ni ce".
Ya ce"Wow! Gaskiya ma sha Allah, ke kyakkyawa ce".
Ta ji daɗi ya kamata, tana so da yabe ta, musamma kyaunta, ta ce"Allah?"
Ya ce"Sosai ma kuwa, wallahi ke ta musamman ce".
Ta ce"Na gode".
Ya ci gaba da typing, sai ta fita ta fara duba baƙin lambobin, ta amsawa wani sallama ya ce"Welcome new member, ke ta musamman ce".
Ta ce"Na gode sosai".
Ta yi gaba, nan ma tana amsa sallama aka ce mata"Beuaty ya kike, ya hutu?"
Ta ce"Alhamdulillah".
Ta yi gaba, nan ta ga admin ɗin da ya yi tag ɗinta a group ne, ya yi mata sallama ya ce"Baby Ummi ya kike?"
Ta ce"Lafiya ƙalau".
Ya ce"Ina son zama abokinki pls idan babu damuwa".
Ta ce"Wannan ba komai ba ne, na gode".
Ya ce"Sai dai fa ina da kishi, ba na son ina abokata da mace na ga wani ma yana kula ta, kin ga dai na riga kowa, pls ki karɓe ni nu kaɗai".
Idan ka ga bakin Ummi a sanda kanta ya ɗauki caji da girma tana ta karɓar saƙonni sai ka yi zaton aljanna take kallo a cikin wayar, gabaɗaya ta kiɗime da yadda maza suke ta biyo ta suna yabon kyaunta, har wani ladabi suke yi mata, a fili ta ce"Ashe kyauna har ya kai haka? Lallai dole Shamsu ya dage".
Ta ga wani ya yi mata sallama, ta kalli hoton dake kan dp ta ga wani fari kyakkyawa ya sha baƙar shadda sai sheƙi take yi, ga bakin glass da agogo kamar ba ɗan Najeriya ba, kanta ya ƙara fashewa, ta amsa masa, suka fara gaisawa ta kasa haƙuri ta ce"Don Allah kai ne a dp?"
Ya ce"Yess".
Zuciyarta ta fara azalzala ta ce"Kana da kyau".
Ya ce"Ai ban kai ki ba Dear".
Ta ce"Allah ka fi ni".
Ya ce"Haka dai kika ce, pls ki yi mini voice".
Ummi har da maƙale murya ta yi masa voice tana cewa"To me kake so na ce?"
Ya ce"Wow! Nice voce".
Sannan ya yo mata voice shi ma ya ce"Sunana Aisam Khalil, zan iya zama abokinki?" Ya faɗa cikin wani irin maƙale murya da ƙasa da ita tamkar tsonon kwarto.
Kafin ta ba shi amsa ƙaramar wayarta ta fara ƙara, ta duba ta ga Shamsu ne, ta samu kanta da jin ɓacin rai, har sai da ta ja tsaki, saboda ya katse mata nishaɗinta, ta ɗaga da sallama, tana ɓata rai kamar yana kallonta, Shamsu ya ce"Matata ta fi ta kowa".
A ranta ta ce'Ai dole ka ce haka mana, tun da ka rufe ni a gida, ga maza masu aji da suka fi ka duk sun ruɗe saboda ni'
A fili kuma ta ce"Ummm".
Ya ce"To, yau kuma rigima za a yi mini?"
Ta ce"Rigimar me?"
Ya ce"Ai na ga kina shagwaɓa kamar ba kya son yin magana".
Ta ce"Bacci na fara yi fa".
Ya ce"Ok, yi kwanciyarki to, dama kira na yi na ji lafiyarki, da safe zan kira ki".
Ta ce"To".
Tana ajiye wayar ta ɗauki babbar ta ɗora daga inda ta tsaya.
A ranar Ummi ba ta yi bacci ba sai ƙarfe ɗaya da rabi, shi ma baccin ne ya rafke ta, ba ta san ma sanda wayar ta sulale daga hannunta ba, sai da ta farka ta kashe data, ta jona caji ta koma ta kwanta, nan kuma tunanin Aisam ya faɗo mata, za ta iya cewa ba ta taɓa jin namiji mai daɗin murya irin tashi ba, ga shi kyakkyawa, ƙila ma ƙarshe ya ce yana sonta, wani baƙinciki ya turnuƙe ta, da ta tuna ita fa matar aure ce, wacce ba ta da damar sake auren wani, ga kuma tunanin gobe Juma'a za ta tura Friday pic, da wannan saƙe-saƙen ta ci gaba da baccinta.
Washegari ba ta tashi da wuri ba, tana idar da sallah da ta koma sai ƙarfe tara ta tashi, tana sane jiya ba ta yi wanke-wanke ba, har da sauran na shekaran jiya, ga shi doguwar rigar da take so ta saka ta yi Friday pic na yau ba a wanke take ba, saboda haka ta yi wa kanta faɗa ba ta kula wayar ba, ta fara wanke rigar ta shanya, ta yi wanke-wanke, ta yi shara sannan ta dafa abun karyawa ta zauna ta kunna data ta fara sana'a.
Zuwa ƙarfe goma aka fara turo hotuna, ta kalli yanayin gidan nata ta ga sam babu wani waje mai kyau sosai da hoto zai fito fess saboda so take yi a ce tana ɗaya daga cikin ukun da za a ce nasu ya cinye, duk sai ta ji abun duniya ya dame ta, dabara ta faɗo mata, ta tashi ta shiga maƙotansu, gidan da yake kallon nata, matar tana da mutunci sosai, babba ce don ƴaƴanta har da wanda suka girmi Ummin, Ummin tana shiga haka jifa-jifa suna gaisawa, ta shiga da sallama suka gaisa, ta ce"Momy hoto fa na zo yi".
Ta yi dariya ta ce"Hoto kuma, ke ma kamar wata yarinya?"
Ummi ta ce"Yarinyar ce mana".
Nisaiba da za ta yi sa'ar Ummin ta ce"Mu je na yi miki, a daidai ina za ki yi?"
Ummi ta ce"A waje sai ya fi".
Suka fita waje, tana miƙawa Nusaiba wayar ta fara dariya, ta ce"Da wannan wayar za ki yo hoto? Yasin ba zai fita tarr ba".
Ummi ta ce"To taimaka ki yi mini da taki".
Ta ce"Bari na aro miki ta Yaya Mustapha, sai na tura miki".
Ta karɓo wayarsa babba mai tsada, ta yi wa Ummi hoton, Ummi ta ruɗe ganin yadda hoton ya yi kyau sosai, ta ce"Don Allah tsaya na je na canza kaya".
Gudu-gudu sauri-sauri ta canzo kaya aka ƙara yi mata, aka tura mata, ta tafi tana ta godiya.
Ai kuwa kwalliya ta biya kuɗin sabulu, domin ita ce ta zo ɗaya a wannan satin, har ɗora hoton aka yi a icon ɗin group ɗin, sai da ya yi kwana ɗaya aka sauke, data 3gb aka ba ta a matsayin kyautarta, bayan nan Aisam ya fito group ya ce zai ƙara mata dubu ashirin, ta ajiye account, nan ran admin ya fara ɓaci, saboda kishi, ya so a ce yana da kuɗi da sai ya ba ta dubu hamsin saboda ya kece raini, abin da Aisam ya yi ya sa shi yi wa Ummi magana ya ce"Ya muka yi da ke akan maganar abotarmu?"
Ta ce"Abotarmu tana nan".
Ya ce"Me ya haɗa ki da Aisam?"
Ta ce"Ban ma san shi ba sai yau".
Yusuf Admin ya ɗan ji dama-dama ya ce"To ko ya zo miki da wani zance kar ki kula shi, saboda mayaudari ne, ƴan matan group ɗin nan babu wacce bai yaudara ba".
Ummi ta ce"Ok na gode".
Ba ta da account number, sai ta Farida ta bayar aka turo mata kuɗin. Da Farida ta tambaye ta sai ta ce mata wani ɗan'uwansu ne.
Wannan hoton sosai ya ɗaga darajar Ummi a group ɗin ƴan zamani, kusan rabin mazan group ɗin duk sun biyo ta, sai ta zaɓi wanda ya yi mata suna chart, idan kuma ta ga mutum ya yi kalat ƴan ku ci ku ba mu ba ta sauraron shi, idan ta ɗauki waya har mantawa take yi da aurenta.
*** ***
*RANAR KUKA!*
BY
*SADIYA ABDULRAZAƘ*
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR Zuciyar mace Miji goma... Iya ruwa... Wani auren Matar shige... Da walakin Wutar ƙaiƙayi Alhakin so ***