Ranar kuka

PAGE 9

by @sadiyaabdulrazak954

GIDAN HABIBU

Mahaifiyar Halima tana ganinta da kaya ga yara gabanta ya faɗi, bayan sun zauna sun gaisa ta ce"Halima lafiya dai ko?"

Halima ta ce"Gwaggo ba lafiya ba, gaskiya akwai matsala".

Gwaggo ta ce"Subhallah! Me yake faruwa? Shi da ba ya garin ma ke kuwa Halima me zai haɗa ku faɗa?"

Halima ta ce"To Gwaggo kin ga fa tun da ya tafin nan babu wani abun arziƙi, duk kuɗin da yake samu shi ya san me yake yi da shi, ba ya ba ni komai, ƙarshe dai yanzu ɗora tukunya ma ta gagare mu, sai dai ya turawa babarsa kuɗi ta dafa ta zubo mana, safe, rana, dare, kuma ba isarmu yake yi ba, abincin yara biyar ni ta shida a ƴar kula, da safen nan kuwa kullum wani ɗan iskab koko ne mai tsami da dankali, wataran ma kokon tsurar shi..."

Gwaggo ta katse ta da faɗin"Don Allah ya isa haka Halima, gaskiya ba na son rashin kirki da rashin godiya ga Allah, kin san halina akan raina na gaba da ke za mu ɓata yanzu-yanzu".

Halima ta ce"Amma Gwaggo wannan abin da yake yi ya dace kenan ya ci gaba?"

Gwaggo ta ce"A'a sam, indai abin da kika faɗa gaskiya to akwai matsala, to amma fa ba za a yanke masa hukunci ba har sai an tabbatar da yana samun kuɗin da gaske ke ɗin ce ba ya yi miki".

Halima ta ce"To na nawa kuma? Ga shi ita kullum sai ta yi girkin".

Gwaggo ta ce"Idan ta yi girki abun mamaki ne? Tana da miji, tana da ƴaƴa maza kuma tana sana'a, to ya za ta gagara yin girki?"

Halima ta ce"Yanzu ma fa wai dubu goma ce ya turo mini, don Allah me za ta yi mana? Shinkafa kwano ɗaya ma fa dubu biyar ce, kwana nawa za ta yi mana mu shida? Yanzu yaran nan haka suke tafiya makaranta babu kuɗin break ga shi ba ƙoshi suka ba".

Gwaggo ta ce"Gaskiya babu daɗi, to amma fa wannan ba shi ne zai ba ki lasisin zuwa gida ki zauna ba, saboda haka yadda kika kwaso kaya kika taho haka za ki kwashe su ki koma".

Halima ta ce"To gaskiya ni dai tafiyar nan tashi ba ta yi mini rana ba, gaskiya ni zan iya bin shi".

Gwaggo ta ce"Tashi ki bi shi, amma waɗan nan yaran ki sani ko ɗaya ba za ki ɗauka ba, sai dai ki bar su a nan ko gidan mahaifiyarsa, saboda ba zai yiwu ki kwashi yara ki tafi da su cikin kafirai ba, babu kalar yawon neman kuɗin da babanku bai yi ba, amma ina nan gidan yake tafiya ya dawo ya tarar da ni, kar ma ki sake ki ce za ki fara bin miji wannan yawace-yawacen, akwai matsala babba, ko ɗamara ce da shi soja ko ɗan sanda babu inda za ki bi shi, ya je ya dawo ya tarar da ke, wannan ya fi miki kwanciyar hankali".

To ita ma Halima ta faɗa ne kawai, amma ko da za a ce ta bi shi ɗin ba bin shi za ta yi ba, ta ce"Amma haka zan ci gaba da wannan rayuwar?"

Gwaggo ta ce"A'a rayuwa a haka kam ba za ta yiwu ba, yanzu zan je gidan iyayen nasa a yi magana, a san abun yi, amma a yau za ki koma ɗakinki, haba Halima kin yi girma da yin yaji ai, jiya ba yau ba, ke yanzu ko sakinki Habibu ya yi ai sai dai ya kwashe kayan shi ya tafi, saboda kin zama uwar garke kin ci gida".

Halima tana gida har dare, da babanta ya dawo nasiha ya yi mata sosai, shi ma sam bai goyi bayan ta zauna a gidan ba, sannan shi ma ra'ayinsa ɗaya da Gwaggo babu inda za ta bi Habibu da yara, don haka bayan magriba ta koma gidan, Baba ya sa aka ɗibar mata kayan abinci ya kuma ba ta ɗan kuɗi ta riƙe a hannunta, sannan ya ce zai sa yayyunta ma su bata.

Washegari Gwaggo ta wanke ƙafa ta je gidan su Habibu, ta shigarwa da babarsa ƙorafin Halima, Umma ta ce"Don Allah ku yi haƙuri, wallahi na san duk abin da yake faruwa, kuma ban kare Habibu ba, ni na san inda ya fara samu wallahi ba za a ji shiru har haka ba, wannan na ɗan lokaci ne in sha Allah komai zai wuce, don Allah ki ƙara ba ta haƙuri, ni ma anjima zan je gidan".

Da haka suka rabu, da yamma kuwa ta je gidan, ta bawa Halima haƙuri a tsaitsaye ta tafi, saboda yadda ta ga Halimar ta karɓe ta a shatale, ita Umma ba mace ba ce mai son fitina da biyewa surukai tana kiyaye duk abin da zai janyo mata raini, shiyasa ba ta zuwa gidajensu ma sai ta kama.

Umma ta kira Habibu a waya, suka gaisa ta ce masa"Habibu don Allah idan ka fara samu ka yi ƙoƙari ka kula da gidanka, ba na son abin da za a ce ba ka yi adalci ba".

Ya ce"In sha Allah Umma zan yi iya ƙoƙarina, amma wani abu ya faru ne?"

Ta ce"Babu komai, dama iyayen Halima ne suka kawo ƙorafi, amma na ba su haƙuri ita ma kuma na je na ba ta haƙuri".

Ransa ya ɓaci ya ce"Umma wa ya ce ki je? A kan me za ki saurare su? Ita da ta ce za ta tafi gidansu me ya hana ta tafiya?"

Umma ta ce"A'a Habibu na haka ake rayuwa ba, ka ga fa a nan tana da gaskiya, duk da kai ma kana da gaskiya tun da ya dace a yi maka azuri, to amma ka san ɗan adam kowa da fahimtarsa, fushi da zafin zuciya ba naka ba ne, haƙuri za ka ba ta a lallaɓa har zuwa lokacin da komai zai warware, irin wannan ƙaddarar ba kowace mace ba ce take iya jurewa ba".

Ya ce"To Umma wane irin bayani ne ban yi mata ba? Ita fa ba ƙaramar yarinya ba ce".

Umma ta yi murmushi ta ce"Habibu Halima fa idan ta ƙi fahimtarka ban ga laifinta ba, saboda tun daga kan neman aurenta har zuwa auren da zaman auren ba ka nuna mata yanayin rayuwa yakan iya canzawa ba, kai komai a kwai baja-baja, ba a ce ka tauye iyalinka ba amma ka yi komai saffa-saffa, ka dinga nuna mata ba koyaushe ake neman komai a samu ba, idan Halima ta nemi abu ko bashi sai ka ci ka yi mata, nan har filinka ka siyar ka ba ta jari, yanzu ina jarin yake? Ita rayuwa dole sai ka nunawa mace akwai babu, wacce za ta iya riskar mutum idan Allah Ya ƙaddara, wannan ranar nake ta guje maka, domin na san dole za ta zo, wato ranar kuka, saboda haka dole ka rarrashe ta".

Ya sauke ajiyar zuciya ya ce"Shikenan Umma Allah Ya rufa asiri".

Ta yi masa nasiha sosai sannan suka yi sallama, ya kwanta da tunanin mafita, ya dinga tuna rayuwarsu ta baya tun daga sanda ya fara soyayya da Halima har zuwa yanzu, tabbas ya hidimtawa Halima kafin aure da bayan auren, don shi mutum ne da ba ya so ya ga an fi nashi wani abun, babu kalar aikin wahalar da ba ya yi saboda ya farantawa Halima, bai taɓa zaton idan ya shiga wani yanayi na babu Halima za ta juya masa baya ba, yanzu ya ƙara gane wace ce mace.

Duk da a kwana biyun ta fara girki amma idan Umma ta aiko mata tana karɓa, sai ta ce ai raba arne da makami ibada ne, yanzu kam hankalin ya ɗan kwanta ta rage takurawa Habibu saboda yayyunta maza duk sun turo mata kuɗi, wasu har da kayan abinci.

Sannu a hankali Habibu ya fara samu, dayake yana kishin Halima ta dinga fita barkatai sai yake turawa mai shagon kusa da su kuɗi, yana kai mata kayan abinci, cefanen ma yana yawan ce mata ta dinga aike yara, amma ba ta ji, a cewarta ba ya garin bai isa ya yi mata kulle ba, ficewarta take yi ta yi cefanenta, hankalinta ya fara kwanciya tun da yanzu ga shi har kuɗi suna rara a hannunta ta adana, duk yadda Habibu ya yi da ita ta kama sana'a ta ƙi yi, akwai ranar da suna waya yake cewa"Halima ni fa saboda ƙaruwarki nake son ki dinga sana'ar nan, kin ga wani abun idan kin gani kina so ko kuma za ki yi wa ƴan'uwanki alkhairi sai dai kawai ki yi".

Ta taɓe baki kamar yana kallonta ta ce"Ka ga, kai dai kawai ka ce kana so na fara sana'a ka daina ba ni ɗan abin da kake ba ni, to nawa aka yi? Ku fa maza da kun ga mace tama sana'a shikenan sai ku sakar mata ragamar gidan, to ko na yi sana'a ni ba za a yi wannan tsarin da ni ba wallahi, don haka maganin kar a yi kar a fara".

Ya ce"To shikenan, in sha Allah daga yau ba zan sake yi miki maganar sana'a ba, tun da ƙaruwarki ce".

Daga ranar kuwa bai sake yi mata magana ba, ita kuma da ta duba ta ga ba ta nemi komau ta rasa ba sai ta watsar ta ci gaba da harkokin rayuwarta.

A yanzu abu biyu ne yake damun Habibu, kewar iyalinsa, wato matarsa, ƴaƴansa, da kuma danginsa, sai kuma matsalar da ya ji ya fara shiga ta buƙatar matarsa a kusa da shi, kusan kullum da kewarta yake yin bacci, don haka kodayaushe cikin mafarkai yake, ga shi ya rasa ita Halima wace irin mace ce, sam ba ta nuna alamar ta yi kewarsa, idan ya ja ta da irin firar ma sai ta faɗa masa babu daɗi, akwai ranar da suna waya cikin wasa yake ce mata"Maman Islam, ina ta fama da kaina fa, gaskiya ni dai na zo ajin ƙarshe a buƙatuwa, yanzu ya zan yi?"

Ta ce"Ya za ka yi kuwa? Dama ai ka ce za ka ƙara aure ku tafi da amaryar can, wato yanzu ka ga ka fara samu, a maimakon ka nutsu ka fara shirin yi mana gini mu rabu da gidan hayar nan, shi ne har ka fara hangen ƙara aure, to Allah Ya ba da sa'a".

Ya ce"Haba Halima, yanzu me ya kawo zancen ƙarin aure a nan? Wallahi sam ni ba haka nake nufi ba, ke me yasa ba kya tsayawa ki fahimci magana?"

Ta ce"To ai sai a bar maganar".

Ya ce"Ina tunanin ƙarshen watan nan fa zan zo".

Ta ce"To! Tun yanzu?"

Ya ce"To ya zan yi? Nema fa nake yi na rasa nutsuwata, gara na zo na ɗan rage zafi, idan kuma ma mun daidaita kin yarda kin bi ni kin ga ai shikenan" Ya ƙarasa maganar cikin zolaya, saboda ya san abu ne mai wuya ta bi shi ɗin, amma inda za ta bi shi ɗin yana so har yanzu.

Ta ce"Hmm baban Islam kenan, Allah Ya kawo lafiya, amma fa gaskiya ga daina saka ran ni zan bi ka wannan garin".

Ya ce"Hmm! Allah Ya kawo ni lafiya".

Daga haka suka yi sallama. Kamar yadda ya faɗa ƙarshen watan ya zo, ba za ta ce ba ta yi kewarsa ba, har wata nutsuwa ta ji a zuciyarta, satinsa ɗaya ya koma, bayan ya sake yi mata roƙon su tafi, har cewa ya yi ta kai yaran gidan iyayen shi, tun da tarbiyyarsu take tsoro, ta ce ita ba za ta rabu da ƴaƴanta ba, haka ya tafi cike da kewar iyalinsa.

*** ***

*RANAR KUKA!*

BY

*SADIYA ABDULRAZAƘ*

*FIRST CLASS WRITERS*

MARUBUCIYAR Zuciyar mace Miji goma... Iya ruwa... Wani auren Matar shige... Da walakin Wutar ƙaiƙayi Alhakin so ***