Ranar kuka

PAGE 10

by @sadiyaabdulrazak954

GIDAN ABBA

Bayan kwana biyu ya turo mata kuɗin da za ta siya kayan abinci, a ranar ta shirya ta samu Mama ta ce"Mama zan je can gidanmu akwai kayan da zan kwaso, kuma zan yi shara".

Mama ta ce"Hmm ki ce dai za ki je ki sake ƙulla wani abun".

Aisha ba ta ce komai ba, Mama ta miƙa mata mukullin tana cewa"Ke da gidanki da kike taƙama da shi wa ya isa ya ce ba za ki je ba?"

Ta ɗauki mukullin ta tafi, yau ma kaca-kaca ta tarar da gidan, ga kitchen babu gyara alamar an ci gaba da yin girki a gidan, ɗakin gadon nan kace-kace da kayan sakawar Ashiru, abun takaici a har a kan gadonta, ta ɗauki wayarta ta yi vedion ɗakin ta turawa Abba, ta kira shi ta faɗa masa ya duba whatsApp, babu jimawa ya duba ya gani, shi ma ransa ya ɓaci sosai, ya kira ta ya ce"Yanzu Aisha wannan gadonmu ne haka?"

Ta taɓe baki ta ce"Ai gara ka ganewa idanunka".

Abba ya ce"To fa gaskiya ba zai yiwu ba, gaskiya da sake, ko yaron nan zai ci gaba da kwana a gidan nan to sai dai a rufe ɗakin gadon nan, ki ma zare mukuɗlin tun yanzu".

Ta ce"Ai ga kayansa nan a ɗakin".

Ya ce"Ki watsa su waje mana! Shi da aka ce bacci ne zai dinga kai shi, akan me ma zai kawo kayan sakawar shi?"

Aisha ta ce"Abin da nake nuna maka kenan ka kasa ganewa, wannan sam bai dace ba".

Ya ce"Ki ƙara haƙuri don Allah, zan yi magana da Maman".

Ta ce"To Allah Ya sa ta fahimta".

Ya ce"In sha Allah za ta yarda, yanzu me kike yi?"

Ta ce"Gyara gidan zan yi sai na kwashi kayan da na zo ɗauka".

Ya ce"To a yi aiki lafiya".

Ta gyara gidan tsaf, ta sauke katifar daga kan gadon ta jingine ta a gefe, ta gama abin da za ta yi ta ɗauki kayan ta tafi, ana sallar la'asar ta shiga gidan, ta tarar da Mama a tsakar gida tare da ƙanwar Abba da ta zo tana yi mata kitso, Hafsa da fara'arta ta ce"Anti Aisha ashe kin dawo".

Ita ma Aisha ta saki fuska, don ba tun yau ba ta lura ita Hafsa ba ta yo halin sauran ƴan gidan ba, sannan ta ga kamar ma sun fi shiri da Abba, ta ƙaraso tana cewa"Na dawo Anti Hafsa, ashe kin zo gidan, sannu da zuwa".

Ta kalli Mama ta ce"Mama sannu da gida".

Mama ta ce"Yawwa" Tana yi wa kayan hannunta kallon gefen ido, amma ba ta ce komai ba.

Ta yi alwala ta yi sallar la'asar, Mama ba ta ce mata ga abinci ba, ita ma kuma ba ta tambaya ba, don idan ba ta ba ta ba ƙyale ta take yi, ballantana yau da take ganin abu ya zo gangara tun da gobe za ta fara girkinta, ko hijjabin ba ta cire ba ta tashi ta zo za ta sake fita, Mama ta ce"Aisha! Fita kuma za ki sake yi? Wai ni me kika mayar da aurenki ne? Anya ma kina tambayar mijinki kuwa?"

Hafsa ta ce"Haba Mama, to wa za ta aika? Kuma na san ba za ta ƙi tambayarsa ba".

Mama ta ce"Ke dalla rufe mini baki!".

Aisha ta ce"Wallahi Mama ina tambayar shi".

Mama ta ce"To amma don me aka kawo Muhibba? Wani abun ai sai ki dinga aikenta".

Hafsa ta shigar maganar ta ce"Mama wani aike fa na sirri ne".

A fusace Mama ta ce"Ke Hafsa jakar ubanki! Wai da ke nake yi ne?"

Aisha ta yi ficewarta don ba ta ga amfanin tsayawar ba.

Tana fita Mama ta fizge kanta daga kitson, ta tashi ta shiga ɗakin Aishar, Hafsa ta bi ta da kallon mamaki, sam ba ta jin daɗin irin abin da take yi wa surukar tata, saboda idan aka zage ta su ƴaƴanta ba za su ji daɗi ba, ita kuwa Mama ko a jikinta ta bincika ta ga kayan kitchen ne, ta cika da mamaki, ta fito tana cewa"Ke Hafsa kin ga fa yarinyar nan kayan kitchen ɗinta ne ta kwaso, to me take nufi?"

Hafsa ta ce"To Mama ita da kayanta?"

Mama ta ce"Kodayake bari na zuba ido na ga gudun ruwanta". Ta zauna suka ci gaba da kitson.

Sai da ta siyo komai har kayan miya, ta siyo mangal da gawayi, saboda ba ta ɗakko gas ɗinta ba, ta dawo da kaya riƙi-riƙi, Mama ta kasa yin shiru ta ce"Wai ni Aisha shige da ficen me kike yi ne? Wannan kayan fa?"

Aisha ta ce"Mama dama zan fara yin girki ne, shi ne nake ta haɗa kayan".

Mama ta ce"Girki!? Aisha ware sanwarki za ki yi? Kenan kowa ya dafa na shi sai ka ce masu zaman kishi?"

Aisha ta ce"Ba haka ba ne Mama, wallahi kawai dai bakin nawa ne ba komai nake son ci ba, to kuma sai ya ce kin yi ƙorafi akan siyo wani abun da nake yi ina ci, sai muka yanke shawarar kawai na dinga yin girkina".

Mama ranta ya ɓaci sosai ta ce"Kuka yanke shawara ke da wa?"

Aisha ta ce"Ni da shi".

Mama ta ce"A lallai, Abba wuyansa ya isa yanka, ni ina nan a cikin gidan kuka zagaye kuka yanke shawara? Kodayake dama ai kin fi ni matsayi a wajen shi, babu komai ki je ki yi girkinki".

Hafsa ta ce"Mama ni fa ina ganin wannan ba matsala ba ce, da "Saboda uban wani ne ya yi mini naƙudar yaron ko? Hafsa kar na sake jin bakinki a maganar nan, ke zo ki tattara ki tafi gidanki".

Aisha dai ba ta ce komai ba ta shige ɗakinta, don idan da sabo ya kamata a ce zuwa yanzu ta saba da faɗan Umma har da mara dalili ma, kuma dama ta san za a iya yin fiye da haka ma a kan girkin, amma ita dai ta yanke ko me za a yi sai ta yi girkin nan, ta gaji da wannan musgunawar.

Ta fito da komai ta ajiye a gefe, a gaban Mama ta fito ta kunna gawayi ta ɗora tukunya, ta fara gyaran kayan miya, taliya da miya ta yi, tana dab da gamawa Hafsa ta zo tafiya, Aisha ta ce"Haba Anti Hafsa da ke fa na ɗora, ga shi har an kusa saukewa, don Allah ki tsaya ki ci".

Hafsa ta ce"Wallahi sauri nake, ni ma girkin zan je na yi, ai ana tare wataran zan ci".

Cikin takaici Mama ta ce"Ai sai ki ci tun da babu a gidan naki mijin".

Hafsa ta girgiza kai cikin rashin jin daɗin abin da mahaifiyar tasu take yi, ta yi musu sallama ta tafi.

Da ta sauke girkin ta zuba a kula ta je kai wa Mama, lokacin tana cikin ɗaki suna cin abinci su duka, ta yi sallama, Baba ne kawai ya amsa ta shiga ta ajiye kular tana cewa"Mama ga taliya".

Mama ta ce"An gode ki ɗauke abarki, ga shi mu ma muna cin abin da Allah Ya hore mana".

Baba ya ce"Kamar ya, wace taliya? Ita a ina ta samu taliya?"

Mama ta ce"Au ashe fa ban faɗa maka ba, to ai Aisha ta raba girki da mu, ba za ta iya cin gabzar da muke ci ba, shiyasa Abba ya turo mata kuɗi ta yo siyayyar abin da ranta yake so, take girkinta".

Baba ya ce"Ma sha Allah! Kenan dai yanzu an raba tukunyar, to ai dama ni a ganina haka shi ne daidai, ai ina mamakin a ce suruka ta naɗe ƙafa wai uwar miji ce za ta dafa ta ba ta ta ci, ba wai ita ce za ta dafa ta bawa iyayen miji ba, mu dai a zamaninmu ba a yi haka ba sam, kuma ke ma Hansatu kin sani, amma kika yi biris, to tun da yanzu yarinyar nan ta gano hanya madaidaiciya ke kuma sai ki wanke tukunyarki, idan ta yi sai ta dinga zuba mana".

Gaban Aisha ya ba da rass, wannan tsarin sam bai yi mata ba, ta ya za a ce ita za ta dinga yin girkin duka gida? To ashe ma babu amfanin rabawar.

Ba ta gama tunanin ba ta ji Mama ta ja tsaki ta ce"Kai dai Malam ban san sanda za ka san ka girma ba ka daina kwaɗayin abun duniya, na wanke tukunya fa ka ce, yarinya ƙarama ta dinga dafawa tana sammin? To ba zai yiwu ba!".

Baba ya ce"To ai shikenan, amma dai ita Aisha ki bar ta ta ci gaba da girkinta, don gudun shiga haƙƙinta, Hansatu ina raba ki da haƙƙi fa!".

Mama ta ce"To Malam dama ka ji na hana ne? Ba dai ya fara siya mata kayan abinci ba? To mu kuwa sai abincin ya gagare mu, ko kuma idan ma ya bayar ɗin ya ba ta madara ya ba mu gasara".

Baba ya ce"Ke ya ishe ni haka nan".

Ya ture kwanon shinkafa da waken gabansa yana cewa"Na hana ki wannan girkin samfurin tazarce kin ƙi ji, saboda lalace a dafa shinkafa da wake a ɗirke a kula tun rana, wannan ma tun safe kika dafa ta don sha biyu ba ta yi ba kika gama".

Ya fara lalube yana cewa"Ke Aisha, ina Aisha".

Ta share hawayen da ya sakko mata ta ce"Baba ga ni".

Ya ce"Maza ki ci gaba da yin girkinki, ina abin da kika dafa mene ne?"

Ta ce"Taliya ce da miya".

Ya ce"Yawwa maza miƙo min nan kusa da ni, Allah Ya shi albarka".

Ta muƙa masa kular, ya laluba ya buɗe ya juya ya fara kao loma yana cewa"Idan aka hana ta girki ai kamar an tauye ta ne, yarinyar nan tana da haƙuri fa Hansatu kar ki ƙure ta"

Ita dai Aisha daga haka ta tashi ta fice daga ɗakin, ta yi sallah ta zuba abincinta ta ci ta ƙoshi sannan ta kwanta ta yi wa mijinta plashin ya kira ta suka yi waya.

Suna gamawa ya kira Mama, cike take da shi akan maganar abincin nan, sai kuma ya ƙara mata da maganar Ashiru dole ya daina hawar musu gado, ai kuwa ta ɓarke da masifa ta inda ta shiga ba ta nan take fita ba,ta ce kwana ma yanzu ya fara, ƙarshe dai Abba haƙuri ya ba ta ya ce shikenan.

Ya sake kiran Aisha ya faɗa mata yadda suka yi da Mama, ta ce"Gaskiya ni zan ɗauke katifata, don wallahi yanzu ma ƙyanƙya min kwana a kai zan ji".

Ya ce"To idan kina da inda za ki kaita ai babu matsala sai ki ɗauke".

Ta ce"Zan yi waya da babana idan ya yarda sao na kai".

Haka kuwa aka yi, washegari da safe ta kira babanta ta sanar masa, ya ce babu matsala duk ta kwaso kayan ta kawo gidan ai akwai ɗaki. Indomi ta dafa ta dama costerd, ta zuba a ƙaramar kula shi ma costerd ɗin ta saka a kofi, ta yi sallama a ƙofar ɗakin Mama, lokacin tana banɗaki, sai Baba ya amsa yana cewa"Aisha ce?"

Ta ƙarasa ta gaishe shi, ya amsa, ta ajiye tana cewa"Baba ga indomi babu yawa".

Baba ya washe baki yana cewa"Mai yawan kenan ƴar nan, madallah sannu da ƙoƙari, matso da ita nan kusa da ni".

Ta kai masa har gabansa ta fita daga ɗakin, tana gama karyawa ta yi wanka ta shirya, sannan ta fito, suka gaisa da Mama ta ce mata"Mama mukullin gidanmu..."

Mama ta katse ta da faɗin"To yau ma zuwa za ki yi? Kenan dai ke yanzu a can za ki dinga wuni ko?"

Aisha ta ce"A'a Mama, dama akwai kayan da zan ɗauka ne".

Mama ta taɓe baki ta ce"To ai Ashirun yana can bau tashi ba".

Ta ce"To bari na je".

Da sauran kuɗin hannunta ta samo mai kura suka je har gidan, suka tsaya a bakin ƙofa ta fara bugawa, Ashiru ya ce"Waye?"

Ta ce"Aisha ce".

Ya ce"Kai! Amma wannan yarinyar akwai wahalalliya, daƙiƙiyar banza da wofi!".

Ya kalli Mansura wacce ta yi ɗaiɗai tana shirgar bacci ya ce"Ke Mansura! Dalla tashi".

Ta tashi tana cewa"Amma dai Ashiru na faɗa maka ka daina tashi a daga bacci ko?"

Ya ce"Dalla masu gidan ne suka zo".

Ta janyo kayanta tana cewa"Masu gidan kuma? Dama yayan naka ya dawo ne?"

Ya ce"Ina fa! Matarsa ce wata ƴar wahala, mara kunya, wai take zuwa shara".

Mansura ta ja dogon tsaki ta ce"To sai dai idan kai za ta yi wa rashi kunya ni wallahi saita ta zan yi".

Ta ƙara yin tsaki ta ce"Kai sai na yi wanka ma".

Ashiru ya ce"Babu wani wanka, kawai ki fice".

Ta saka kayanta Aisha hat ta gaji da bugu ta fara tunanin ko ba ya gidan sai ga shi ya zo ya buɗe, macen ce ta fara fitowa, gaban Aisha ya faɗi ta kalli Ashiru wanda ya yi kicin-kicin ya ce"Ya aka yi?"

Ta ce"Kaya na zo ɗiba".

Mansura tana zagba mata harara suka fice da shi, ita kuma ta bi su da kallo sannan ta shiga cikin gidan, dama ko da aka ce yana kawo mata ko kaɗan ba ta yi shakka ba to yau ga shi ta ma gani da idonta.

Suka ɗakko katifar da zannuwan gadonta, aka kai gidan Baba, sannan ta siyo sabon kwaɗo ta rufe kitchen ɗinta da shi, ta koma gida ranta duk a ɓace, da ta faɗawa Abba haƙuri kawai ya ba ta, ya ce mata ya kusa zuwa garin kafin ya tafi zao saita komai, idan ma ya kama za su koma tare ne sai a yi hakan.

*** *RANAR KUKA!*

BY

*SADIYA ABDULRAZAƘ*

*FIRST CLASS WRITERS*

MARUBUCIYAR Zuciyar mace Miji goma... Iya ruwa... Wani auren Matar shige... Da walakin Wutar ƙaiƙayi Alhakin so ***