PAGE 11
Tana jiyo Mama tana tijara, da alama wata ƙaryar Ashiru ya zo ya haɗa mata ta hau kai ta zauna, ita dai ba ta kula ta ba, yau tuwo ta yi da rana har dare, ta zuba ta kai wa Baba, ya karɓe yana ta saka mata albarka, wannan karɓar abincin da Baba yake yi ba ƙaramin ɓatawa Mama rai yake yi ba, amma dai haka ta yi shiru, ita dai ba ta taɓa cin abincin Aisha ba, wataran tana jin ƙamshin girkin take jin sha'awar ci, amma haka take daure zuciyarta. Shi kuwa Baba da likafa ta ci gaba ma, har cewa yake idan tana da abu kaza ta ɗan dafa masa, amma sai ranar da ya ga Mama ba ta gidan.
Ware girkinta bai sa ta daina yi wa Mama aiki ba, kullum za ta haɗa kayan wanke-wankenta da na Mama ta wanke ta gyara gidan, girkin ma tana karɓa wataran kuma Mama ta hana ta, yanzu hankalinta ya fara kwanciya, musamman da Abba yake samu sosai. Akwai ranar da ya sa abokinsa ya siyo kaji uku ya yanko ya kawowa Aisha, ya ce ta soya su ci, da zuciyarta ɗaya ta fara aikin kajin, ranar Mama ba ta gidan, ta fara sulale ta dawo lokacin ƙamshi ya buɗe gidan, Mama ta kalli tukunyar da take ta tururi ta jinjina kai, Baba da ke ƙofar gida a zaune jin dawowar Mama ya saka shi shigowa gidan, shi ma ya ji ƙamshi ya cika masa hanci, ya ce"Ikon Allah! Kaji ake dafawa a gidan namu ko daga maƙota ne?" Ya yi maganar yana ƙara buɗe ƙofofin hanci don ya shaƙa da kyau.
Takaicinsa ya hana Mama magana, ya nemi waje ya zauna yana cewa"Hansatu magana fa nake yi saboda Allah kin share ni".
Ta ce"Don Allah Malam ka rabu da ni".
Ya ce"Ai shikenan, amma ni ina mamakin yadda matane ba sa sanin haƙƙin maƙobtaka, ki duba ki ji wannan ƙamshi, kuma a ce babu hakki? Gaskiya akwai sakayya".
Aisha tana jin shi ba ta tanka ba, saboda zuwa yanzu kwaɗayin nan na Baba ya fara ba ta haushi, tana fara suya Baba ya zabura ya ce"Yasin kamar ƙarar suya, Hansatu ba ki ji ba kamar an tsoma nama a cikin mai?"
Mama ta ce"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Ni dai ba don auren saurayi da buduruwa muka yi ba da sai in ce ban san jinsin da na aura ba".
Ya ce"Kamar ya me kike nufi?"
Ta ce"To ka saka ni a gaba da zancen nama, a gaban surukarka kake dai sai ka ji kunya".
Ya ce"Au! Aisha ashe kina kusa".
Aisha ta ce"Sannu Baba".
Ya ce"Sannu ƴar albarka, ko dai ke ce kike sulala kaza?"
Ta ce"E so nake na kwashe kaskon farko sai na zubo maka, Abba ne ya aiko ɗazu ya ce a soya kowa ya ci".
Baba ya gyara zama yana haɗiyar yawu ya ce"Allahu akhbar! Ashe ma abun a kusa da ni yake, Allah sarki Abba Allah dai Ya ƙara buɗa masa".
Mama kuwa ji ta yi kamar an caka mata mashi, wai ɗanta ne ya aikowa matarsa kaji ita tana zaune a gidan. Baba ya ce"Amma Hansatu kina ji ina tambaya shi ne kika yi banza da ni?"
Mama ta tashi ta ɗauki wayarta ta fita fuuu, a ƙofar gida ta tsaya ta kira Abba a waya, ko gaisawa ba su yi ba ta ce"Abba ni na haife ka ko uwar Aisha?"
Ya ce"A Mama me ya faru?"
Ta ce"Abba ni za ka nunawa matarka ta fi ni daraja a idonka ko? Duk kazar da kake aiko mata a gashe ta shiga ɗaki ta ci ba ta isa ba sai ka fara aiko mata ɗanya ko?"
Abba ya ce"Subhanallah! Ni fa ku na aikowa gabaɗaya, abin da ya sa na ce a ba ta saboda na san idan ma ke ɗin aka bawa dole ita ce za ta gyara, wallahi ni ban yi haka da wata manufa ba".
Mama ta ce"A'a wallahi iya ka aikowa, ni dai ko ɗanɗane ba zan ci ba, ƙila shi kwaɗayayyen mahaifinka zai ci".
Abba zai yi magana ta katse shi da faɗin"Kai Abba tsaya ka ji ni da kyau! Dole sai an yi zama da ni da kai, dole sai an zaɓi ɗaya ko dai Aisha ta daina girkinta ita kaɗai ko kuma ta bar mini gidana".
Abba ya ce"Haba Mama..."
Ta ce"Na dai faɗa maka".
Ya ce"To zan yi shawara Mama don Allah ki yi haƙuri".
Ba ta kula shi ba ta kashe wayar.
Ta koma gidan ta ɗora girki, Aisha tana juye kaskon farko ta samu farantai guda biyu ta zuzzuba, ta je gaban Baba da yake ta haɗiyar yawu ta ajiye ɗaya tana cewa"Baba ga taɓin gishiri".
Baba ya laluba farantin ya ce"Wannan duk taɓin gishiri ne, ba a raba ba kenan ko?"
Ta ce"E wannan taɓin gishiri ne".
Ya ce"To madallah Allah Ya shi albarka".
Ta amsa da amin, sannan ta ɗauki ɗayan farantin ta je ta ajiyewa Mama, kafin ta yi magana Mama ta yi shot da shi naman ya zube ta ce"Kwashe tsiyarki! Je ki bincika kaf danginmu babu maye".
Baba ya ce"To a nan waye mayen? Wai ke Hansatu me yasa kika ƙi girma ne? Gabaɗaya kin fitini yarinya!"
Cikin jin haushi Mama ta ce"Da wanda ya tsargu nake, kuma fitina ba ka ma ganta ba! Kana zubar da girmanka saboda kwaɗayi, to ai barin gidan za ta yi sai ka bi ta, ta dinga dafa uwarta tana ba ka".
Aisha ta tattare naman ta miƙawa Muhibba, sannan ta ce"Haba Mama, don Allah ki dinga fahimtata, ya kawo abun nan ba kya nan, ni kuma na ga bai dace a ce na bar shi sai kin dawo ba, tun da idan ma kina nan zan iya gyarawa shiyasa, amma idan na gama dama ke zan kawowa ki raba".
Mama ta taɓe baki tama ɗaga hannuwa sama ta ce"Allah Ya kiyaye, ni a suwa? Ke isasshiya ai ke ce da gida, kar ma ki sake ki doso ni da tsiyarki".
Aisha ta je ta ci gaba da suya, Baba yana yagar tsoka yake cewa"Rabu da ita ƴar nan, ke da gidan nan mutu-ka-raba, babu inda za ki je".
A zuciyar Aisha ta ce'Mutu-ka-raba? Lallai tsohon nan ka fi kowa son zuciya'.
Da ta gama suya ko ɗaya ba ta ɗauka ba ta kai ɗakin Mama ta ajiye, Mama ba ta kalle shi ba, har aka yi sallar isha'i, shi kuma Baba yana ta jira Aisha ta kawo nama bai san abu yana kusa da shi ba. Can Aisha ta gama tuwon dare ta kawo masa, ya karɓa yana godiya ya ce"Aisha har an gama suyar an yi tuwo?"
Ta ce"An gama Baba".
Ya ce"To ki ɗakko ki kawo mata ta kasa don kar ta ƙullace ki".
Aisha ta ce"Baba ai tun ɗazu da na gama na kawo, ga shi nan".
Baba ya ce"Hansatu! Hansatu me kike nufi ne? Shin ba za ki raba ba?"
Ta ce"Kanku ake ji" Ta ɗakko rediyonta ta kunna ta kafa a kunne.
Baba ya ce"Ke Indo miƙo mini abun nan ki ga".
Ta miƙa masa, ya ce mu nawa ne? Samo mini kwanuka".
Ta ɗakko kwanuka guda biyar ta ba shi, ya ce"Ya har biyar?"
Ta ce"Da Mama, Ashiru, Muhibba sai kai da ni".
Baba ya ce fara rabo idan ya ɗakko ɗaya sai ya mammatsa ya ji yanayin tsokar jiki, sai ya saka a kwanon gabansa, idan ya ji ƙashi ya saka a na Mama haka har ya gama rabon ya ce ta ɗauki nata, dayake Aisha tana lura da son kan da ya yi a rabon, ta waiga ta ga hankalin Mama ba ya kansu, Muhibba kuwa ba ta ɗakin, sai ta ɗauke na gaban Baban ta canza masa da nata, ta fita tana cewa"Sai anjima Baba".
Baba ya ce"Hansatu ga rabonki da na ƴaƴanki".
Ta ce"Ni fa ba na ci!".
Ya ce"Wai ke me yasa kike haka ne? Me yasa ba za ki tausasa zuciyarki ki bar yarinyar nan ta huta ba?"
Ta yi banza da shi, ya ce"To idan ba kya ci ga na yaranki nan sai ki ɗauka ki adana musu".
Mama ta tashi saɗaf-saɗaf ta ɗauki ƙato a kwanon shi ta ƙara a nata, sannan ta kwashe sauran ta matsar gefe, ta bar ɗakin. Muhibba ta dawo daga aiken da Mama ta yi mata ta ce ta shiga za ta ga nama ta ɗauki kwano ɗaya, tana shiga ta tarar da Baba yana ta laluba kwano yana cewa"Ni wai ina daƙwalen da na zuba? Anya ba da jinnu nake cin abun nan ba kuwa? Bari dai na ƙara bisimillah".
Muhibba ta hango ƙundu abin da take mutuwar so, sai kuwa ta lallaɓa ta kwashe su, ta zuba a nata ta bar ɗakin, Baba ya laluba ya tsaya jin gabasa na tsananta faɗuwa ya ce"Tabbas tare da wani muke cin naman nan, ga shi ban ga ƙundu ba?" Sai tsoro ya shige shi, ya rufe ya mayar gefe. Can wajen tara na dare bacci ya ɗauke Mama, Baba kuma yana zaune yana jin rediyo, Muhibba ta yi saɗaf ta buɗe kwanon namansa ta kwashe duka, ta tafi ɗakin Aisha inda take kwana, ya gama komai zai kwanta zuciyarsa ta raya masa ya ɗauki naman ya ci, babu wasu jinnu wasu-wasi ne kawai, yana buɗe kwano ya laluba ya ji wayam ko ƙashi babu, sai ya ƙara ƙarfafa zarginsa, a nan ya ɓingire ya kwanta yana ta salati ƙasa-ƙasa, ya yi shiru bai yi cigiya ba, bai bawa wani labari ba.
Da safe Mama ta sakko ta ci naman ita ma.
Washegari da safe Aisha suna waya da Abba yake ba ta labarin yadda Mama ta nuna jin haushi akan naman nan, Aisha ta ce"Ai sai ka ba ta haƙuri, in sha Allah daga yanzu ko me ka kawo zan dinga jiranta".
Ya ce"Ke ma ki ƙara haƙuri kin san halin Mama".
Ta ce"Babu komai, ai uwata ce, iyaye kuwa dole a yi haƙuri da su".
Ya ce"To dama jiyan da muna magana sai take ce mini ita za ki bar mata gidanta ma, shi ne na ce to ko kawai a yi hakan?"
Daɗi ya kama Aisha ta ce"Tun da har ita ta faɗa me zai hana?"
Ya ce"To zan ƙara yin magana da ita, idan ya so ko Muhibban ce sai ki tafi da ita ko?"
Ta ce"To babu damuwa".
Suna gamawa ya kira Mama suka gaisa, ya ce"Dama Mama akan maganar da na ji kin yi jiya ne".
Ta ce"Wace magana?"
Ya ce"Da kika ce Aisha ta koma can gidan namu, shi ne na ce to yaushe ya kamata ta koma?"
Mama ta ɗauki salati ta dire ta ce"Lallai Abba, kenan dama kai da itan akan ƙaya kuke ko? Ta gaji da zama da jaɓa, to babu inda za ta tafi na janye!".
Abba ya ce"To shikenan, kuma wallahi Mama Aisha ba ta ce mini ta gaji ba".
Ta ce"Kai can! Sai ta faɗa? Ai a idonta da take-takenta ma na karanta".
Ya ce"Mama kenan. Nan da sati biyu zan zo in sha Allah".
Mama ta ce"To! Yaushe ka tafi da har za ka fara zuwa? So kake ɗan abin da kake samu ya dinga tafiya a kuɗin mota?"
Ya ce"Ba haka ba ne, wallahi gajiya na yi da kewarku Mama".
Ta ce"Kewar matarka dai, to tsaya ka saurare ni da kyau, ni ba zan yarda da wannan shirmen ba, ba yanzu za ka zo ba, sai ka yi wata biyar ƙwarara, sannan ka tara abin da ka tara".
Ya ce"Mama amma fa..."
Ta ce"Wannan umarni ne!".
Ya ce"To shikenan Allah Ya sa hakan shi ya fi alkhairi".
Haka ya kira Aisha ya sanar da ita ya fasa zuwa, ga kuma zancen komawa gidanta da aka janye, har kuka ta yi bayan sun gama wayar, haka ta haƙura ta fawwala wa Allah komai.
Cikin satin ta fara zuwa awo, cikin nata wata biyar ne, ta yi scanning komai lafiya.
Haka aka ci gaba da zama da daɗi da babu daɗi, girkinta dai kullum da Baba take dafawa su ci, ranar da ta ji kasalar yin girkin ba ta yi, sai dai ta yi ƴan kame-kamenta, sai ka ji Baba yana ta faɗa shi kaɗai.
Watarana suka yi wani baƙo, wani ɗan'uwan Mama ne ya zo daga can garinsu, wai ya zo yin jarabawa ne a garin, saurayi ne, don haka aka ba shi ɗakin Ashiru yake kwana a ciki, tsakaninsa da Aisha gaisuwa ce kawai, shi ma don ta ga yana da nutsuwa ne ba kamar Ashiru ba da ko kallonsa ba ta yi ballanatan ta gaishe shi, idan ya dawo daga makarantar ba ya fita ko'ina yana zaune a tsakar gida suna fira da Baba, a hankali Aisha ta lura da yadda saurayin nan yake yawan bin ta da kallo, yadda ta saba zama a gidanta haka take yi a nan ma, tun da Ashiru ba ma zama yake yi a gida ba, amma ganin irin kallon da yake yi mata ya sa ta fara saka hijjabi tun da ta ga ba muharraminta ba ne.
Watarana ya dawo daga makaranta Mama ba ta nan, Baba kuma yana ɗaki yana bacci, ita kuma Aisha fitowarta daga wanka kenan, kwatsam ta ga mutum ya faɗo ɗakinta kamar an jeho shi, gabanta ya faɗi ta tashi a razane ta warto hijjabi ta saka tana cewa"Sadi lafiya? Ya za ka shigo min babu sallama?"
Ya ce"Dama wata magana nake so mu yi ta sirri".
Ta fara bin shi da wani kallo kafin ta ce"To ka fita anjima ma yi".
Zai yi magana ta daka tsawa ta ce"Ka fita kar ma wani ya zo ya ganka a ɗakina!".
Ya fice yana waiwayen ɗakin, salatin da Mama ta rafka ne ya ankarar da Aisha ta ga fitar shi daga ɗakin.
*** *RANAR KUKA!*
BY
*SADIYA ABDULRAZAƘ*
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR Zuciyar mace Miji goma... Iya ruwa... Wani auren Matar shige... Da walakin Wutar ƙaiƙayi Alhakin so ***