PAGE 12
Aisha ta yi cak! A ɗaki tana jira ta ji wane kallo Mama za ta yi wa abun, ai kuwa ta ji ta ce"Kao Sadi! Me kake yi a ɗakin Aisha? Me ya kaika, wa ya kira ka?"
Sadi ya fara kame-kame ya ce"Amm...dama...kin ga Mama tuwo ne na ga ta yi shi ne zan ce ta sammin".
Mama ta ce"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Aisha!".
Aisha ta fito, Mama ta kalli ƙafarta ta ga zani a ɗangale alamar ɗaurin ƙirji ne a jikinta, sai da zuciyarta ta buga duk da ba ta tunanin Aisha za ta iya aikata wani abu makamancin wannan, a sanyaye ta ce"Aisha me ya kai Sadi ɗakinki?"
Aisha ta ce"Fitowata dag wanka kenan ya shigo min ko sallama babu, wai za mu yi magana ta sirri".
Mama ta ci gaba da salati tana tafa hannu ta ce"Yau ga baƙar rana! Kenan dama Sadi ba ka bar halin nan naka ba ko? A kan matar ɗan'uwanka za ka gwada? Ai kuwa da Abba ba zai yafe mini ba".
Ta shige ɗaki da sauri, Aisha ma ta koma ɗaki, Sadi ya ja ƙafa cikin jin kunya ya bar gidan, tun da ya zo gidan ya ƙyalla ido ya ga Aisha ya ji ya kamu da sonta da sha'awar kasancewa da ita, a zatonsa zai samu haɗin kai daga gare ta, tun da mijinta ya yasar da ita ya tafi yawon neman kuɗi, ga ta da ƙuruciya, sai ga shi tun kafin ma ya shigar da buƙatar an kama shi.
Ita kuwa Mama jikinta ne ya yi sanyi, saboda ta san halin Sadi da halin ɗan bunsuru, yara biyu ya yi wa ciki a unguwarsu, ban da waɗanda ya lalata ake yin shiru saboda a rufawa yaran asiri, sannan an ce duk kuɗin da zai samu na neman mata ne, shiyasa tun da ya zo gidan take saka ido akan Muhibba, ashe shi ta kan matar aure ma zai bi saboda shahararsa, tana jin tsoron Abba ya ji wannan badaƙalar don haka ta tashi ta koma ɗakin Aisha.
Lokacin ta saka kaya tana zaune tana mamakin wannan abin da ya faru, Mama ta yi sallama ta shigo, ba ta taɓa shiga ɗakin tana nan ba, idan ka ga Mama a ɗakinta to sai dai idan Aishar ta fita cefane ba ta rufe ɗakin ba sai Mama ta leƙo ta ɗan yi bincike a gurguje ta fita, Aisha ta amsa sallamar, ta tashi ta shimfiɗa mata sallaya, ta zauna ta ce"Aisha maganar da kika faɗa mini iya abin da ya faru kenan?"
Aisha ta ce"Wallahi shikenan, shigowarsa kenan kika shigo".
Mama ta ce"To Alhamdulillah! Don Allah ki yi haƙuri, shi dama halinsa ne, amma ban yi zaton rashin kunyar tasa ta kai ya gwada a cikin gida ba kuma a kan matar aure, ni dai alfarma ɗaya nake nema a wajenki, don Allah kar ki faɗawa Abba wannan abun, kin san ba zai ji daɗi ba".
Aisha ta share hawayen da ya sakko mata ta ce"Mama a gaskiya ba zan iya ci gaba da zama tare da Sadi a gidan nn ba, kuma Abba ai dole ya ji, don ba a san me zai faru gobe ba".
Mama ta ce"Wannan yaron fa ɗan'uwana ne, ki rufa mana asiri, shi ma azal ce take bibiyarsa kishiyar uwa ce ta yi masa asiri yake wannan leƙe-leƙen".
Aisha ba ta ce komai ba.
Mama ta ce"Tun da haka ne ki koma gidanki ki zauna tare da Muhibba, idan an yi hakan ba za ki faɗa ba?"
Daɗi ya kama Aisha ta ce"To shikenan, indai na bar kusa da shi ai magana ta ƙare".
Mama ta ce"Ta ƙare kam, yau za ki koma ko sai gobe?"
Aisha ta ce"Sai yadda kika tsara Mama".
Mama ta ce"To ni a ganina ki koma tun yau, tun da rana ba ta yi ba, ni ba na bayan ƙarya da cin amana, haka kawai yaro ya zo ya saka ni a uku!".
Ta ce"Maza tashi ki fara shiri, zan nemo mai kura".
Aisha ta tashi ta fara haɗa kaya ranta fess.
GIDAN SHAMSU
Satinta biyu a cikin group ɗin lokacin zuwa taron group ya yi, kuɗi aka fara haɗawa wanda a ciki ake hidimar taron, maza kowa dubu biyar mata kuma kyauta ne, wasu daga ciki har dubu ashirin suke sakawa, shi kuwa Aisam da ya tashi dubu hamsin ya saka, hakan ya ƙara tabbatarwa da Ummi da gaske mai kuɗi ne, irin sabon da suka yi da ƴan group ɗin ne ya sa ta ji cewar dole ta je taron nan, ba ta da ƙawa mace ko ɗaya, ta lura ma kamar matan group ɗin hassada suke yi da ita, abokanta da dama na group suna zumuɗin ganinta a zahiri, wani leshi na cikin lefenta ta ɗakko ta kao ɗinki, aka yi mata doguwar rifa mai kyau tun tana ɓoyewa Farida shirin da take yi har dai wataran ta zauna ta zayyana mata, Farida ta yi jimm sannan ta ce"Amma Ummi me yasa za ki yi ƙaryar ba ki da aure? Ba kya jin tsoron wani ya ce zai zo gidanku?"
Ta ce"Ni ma fargabata kenan Farida".
Farida ta ce"Kodayake ba kanki farau ba, dama wasu masu auren fa suna soyayya da maza, wani ma ko ya san kina da aure zai ci gaba da kula ki".
Ummi ta ce"Anya kuwa?"
Farida ta ce"Ke wallahi ko aure dubu ne a kanki wani babu ruwansa, na ga haka wata ƙawata ta yi, ita saboda tsabar ta shahara har ƙofar gidanta saurayin ya zo zance, ƙarshe mijin ya zo ya gansu a tsaye, nan take ya sake ta, wasu kuwa har a hotels suke haɗuwa kin ga wannan ya ma fi sirri".
Ummi ta ce"Hotel? Wannan kuma ai ba soyayya suke yi ba, sai dai idan kawai holewarsu suke yi, ni kam Allah Ya yi mini tsari, zan dai kula su iya ta waya, ina samu ana saka mini data ana ba ni ƴan canji, sannan mu sha fira, tun da shi ya baza ya tafi".
Farida ta ce"Amma dai gaskiya ki bi a hankali, kin ga mijinki bai ma san kina da waya ba, yanzu ya za ki yi da shi idan ya dawo?"
Ummi ta ce"Ba zan taɓa yarda ya gane ba ai".
Ta ce"Ni dai za ki raka ni gidan kwalliya ranar taron nan, Fa'iza za ta zo ta yi min jan lalle haɗaɗɗe, so nake na kere kowa a wajen nan".
Farida ta ce"In sha Allah sai kin fi kowa".
Sai Farida ta koma gida a sanyaye, sam ba ta jin daɗin yadda Ummi take son jefa kanta a sabuwar rayuwar nan ba, a yadda aure yake wahalar nan ta samu miji irin Shamsu mara tsanani kuma mai sonta ga aiki zai samu me ya yi mata zafi ta yi wasa da aurenta? Ita a yadda take ji yanzu ko wanda bai kai Shamsu komai ba ta samu aure shi za ta yi, mazan auren sun gagara, kowa idan ya zo da fasiƙanci yake zuwa, ga shi zaman gidan babu daɗi, duk hidimarta ita take yi wa kanta daidai da wanki idan za ta yi sai ta sayi ruwanta, ba ma zancen omo ake yi ba, shiyasa tun ba ta biyewa mazan har ta fara biye musu take sheƙe ayarta, yanzu haka akwai inplan a jikinta wanda ta saka saboda gudun samun ciki, abu ɗaya da ya sa ba za ta faɗawa Ummi gaskiya ba shi ne don kar ta hana ta samun mafakar kawo zawarawanta, don kuwa Allah ne kaɗai ya san sau nawa suka kwanta da wannan Alhajin a falon Ummi, saboda shi ya ce mata ba ya son zuwa hotel saboda tsaro, yanzu idan ta fahimtar da Ummi ta shiryu ai ta san har zancen ma za ta iya soke shi, don haka ta yanke gara ta bar ta ta dilmiya ita ma, ai maza macuta ne maciya amana, su ƙi auren mace su dinga lalata mata rayuwa alhalin suna da matansu a gida, to gara na gidan su fara fitowa su ma suna cin amanarsu, wa ya sani ko shi ma Shamsun yana can ya samu wata? Ta ayyana haka a ranta.
Ana gobe taro aka yi wa Ummi jan lalle haɗaɗɗe da kitso na brazil davya cika kanta, taron na safe ne ƙarfe tara aka ce zuwa ƙarfe ɗaya, don haka yau ba ta koma baccin asuba ba, ta gama gyara gidan tsaf, sannan ta ɗauki waya ta fara chart kafin a fara shiryawa, sai ga kiran Aisam, ta ɗauka suka gaisa ya ce"Queen yau ne dai haɗuwarmu, wallahi duk na matso, ji nake kamar na juya agogo ya janyo lokacin".
Ta yi ƴar dariya ta ce"Kuma idan ka juya agogon ɗakinka na mutanen duniya fa?"
Ya ce"Sai ki taya ni juyawa".
Suka yi dariya a tare. Ya ce"Na zo na ɗauke mana pls, kin ga na hutar da direbanki"
Ummi ta yi murmushin ƙarfin hali, na ganin duk yadda take faɗawa Aisam ita ƴar talakawa ce ya ƙi yarda, cewa yake shi fa ta kalar fatar mace yake gano wace ce ita, ta ce"Ka rabu da ni, zan taho ni kaɗai"
Ya ce"To na turo a ɗauke ki?"
Ta ce"A'a fa, ni ja rabu da ni, zan hau adaidaita sahu na zo".
Ya yi dariya saboda adidaita sahu da ta ambata, ya ce"To me zai hana ki zo da wuri, kamar takwas da rabi, taron nan ana African time sai ki ga sai goma za a fara, idan muka zo da wuri muka riga kowa sai mu sha firarmu mu na kalle ki sosai har na ƙoshi".
Ta ce"Gaskiya takwas da rabi ya yi kaɗan, yanzu fa takwas saura kwana, ka ga ko karyawa ban yi ba, kuma ina son zuwa gidan kwalliya".
Ya ce"Yes, ni ma ban yi break ba idan kin zo ba sai mu yi ba?"
Ta ce"Kwalliyar fa?"
Ya ce"Oh! Ki bar ta pls wallahi idan na ga mace da wannan kwalliyar ba ta birge ni sam, kamar aljanu fa kuke zama, kar ki indai kina so mu shirya, shirya ki taho pls".
Ta ce"Ok to bari na tashi yanzu na shirya".
Ya ce"Yawwa My, sannan ba ki faɗa mini abin da zan taho miki da shi ba fa, tun rannar kike ta yi mini kwana".
Ta ce"Allah babu komai".
Ya ce"Ok idan kin gama za ki taho ki taɓo ni, ai dai kin san ɗakin taron ko?"
Ta ce"Ban dai taɓa zuwa ba amma ma su adaidaita sahu ai ba za su rasa sani ba".
Ya ce"Ok sai mu haɗu a bakin get".
Suna yin sallama Ummi ta diro daga gado, ta shiga wanka, da ta fito ta ga miss call ɗin Shamsu ba ta bi ta kansa ba, ta hau shiryawa, kafin ta gama Shamsu ya sake kiranta har sau uku, ta yi tsaki tana cewa"Wannan shegiyar waya sai ƙara, ta ɗauka ta cillata a lokar mudubi.
Da ta gama komai ta yi rolling da mayafinta ta ɗauki jakarta ta tsaya ta kalli kanta a mudubi, sai ta sakarwa kanta murmushi saboda kyaun da ta ga ta yi, sai dai idan ta tuna tana da aure kuma haram take aikatawa sai ta ji zuciyarta ta yi rauni, ranta kuma yana ɓaci, daga nan kuma sai wata zuciyar ya faɗa mata ai ba zina take aikatawa ba, kuma ba za ta dawwama a haka ba, gaba za ta daina, da wannan tunanin ta fice daga gidan bayan ta kira Aisam ta faɗa masa ta fito, ya ce mata shi ma ga shi nan fitowa.
Da aka sauke ta a ƙofar ɗakin taron ta sallami mai adaidaita sahu, ta dai ga tsirarun motoci a wajen, ta tsaya tana waigen ta inda Aisam zan ɓullo, wata haɗaɗliyar baƙar mota dake wajen ce ta fata matsowa inda take, tana matsawa motar tana ƙara matsowa, har ranta ya fara ɓaci, sai ta tsaya ta ga gudun ruwan na cikin motar, ya buɗe ya fito yana murmushi, "Aisam!" Ta faɗa da zumuɗi tana murmushi.
Shi ɗin ne dai da gaske na cikin waya, kyakkyawan nan mai kaɗar ƴan hutu, ƙirar ƙasar waje, suka ƙure juna da kallo, a zuciyar Ummi tana raya yanzu shikenan auren Shamsu ya yi mata shamaki da samun wannan namijin da ya tara komai a matsayin mijinta? 'Shamsu ka cuce ni!' Ta faɗa a zuciyarta, har ƙwalla ta fara taruwa a idonta ta yi dauriyar mayar da ita.
Aisam ya buɗe mata hannu alamar yana jira ta yi masa oyoyo, sai ta rufe fuskarta tana dariya, ya ƙaraso yana tafa hannuwa ya ce"Finally yau dai ga ni ga Queen ɗina, welcom my love".
Ummi ta ce"Me too".
Ya ce"Kin ba ni mamaki fa, ashe da gaske a adaidaita sahu za ki zo, me yasa?"
Ta ce"Ai na faɗa maka gidanmu ko babur babu".
Ya ce"Pls ki bar irin wasan nan, shi fa talauci ba a yi masa haka, ni yadda na tsani talauci da talakawa ko da wasa ba na danganta kaina da shi, don haka ki bari pls".
Zuciyar Ummi ta buga da ƙarfi, jin furucinsa wai ya tsani talauci da talakawa, me hakan yake nufi? Kenan ko da aurenta ya mutu ba zai ci gaba da sonta ba? Idan haka ne kuwa akwai matsala.
*** ***
*RANAR KUKA!*
BY
*SADIYA ABDULRAZAƘ*
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR Sandar dukan uwargida Zuciyar mace Miji goma... Iya ruwa... Wani auren Matar shige... Da walakin Wutar ƙaiƙayi Alhakin so ***