Ranar kuka

PAGE 13

by @sadiyaabdulrazak954

Ya ce"Me yasa kike son hawa adaidaita sahu? Yanzu da wani namijin ya zauna a kusa da ke fa? Kin san an cutar da ni?" Ya ƙarasa maganar yana ƙashe mata ido.

Ta haɗiyi wani yawu mai taure sannan ta ce"Ba a gidanmu na kwana ba jiya, ina can gidan yayan babanmu, to kuma direban ya tafi kai yara makaranta bai dawo ba, ƙila an aike shi, shiyasa kawai na taho".

Ya ce"Ban yarda ba, ai dama kina ta furta a adaidaita sahu za ki zo".

Gabanta ya ɗan faɗi ta ce"To ƙila fata na yi wa kaina, amma fa ni dama ina hawa adaidaita sahu, musamman idan zan je waje na sirri wanda ba na so a sani a gida".

Ya ce"To yanzu an san kin zo nan, ko shi ma sirrin ne?"

Ya ce"Ba a sani ba, cewa na yi birthday ɗin ƙawata zan je".

Ya yi dariya ya ce"Wow!Amma na yi mamaki, kamar ki ai kin girma da yi miki kulle, ya dace a ce kin samu ƴancin zuwa inda kike so, ƙaramar yarinya ake yi wa wannan tsaron ke kuwa kin san ciwon kanki".

Ta ce"Gaskiya ina da yaya mai zafi sosai, yana saka ido a kaina".

Ya zaro ido ya ce"Amma dai uwa ɗaya uba ɗaya kuke ko?"

Ta ce"E".

Ya dafa ƙirjinsa yana cewa"To Alhamdulillah! Kin ga mu ƙarasa daga motar, na ga sai kallonki ake yi".

Ya buɗe mata gidan gaba ta shiga ta zauna, sanyin AC da ƙamshi ya dake ta, har sai da ta sauke ajiyar zuciya, shi ma ya shiga ya rufe motar, sai bin ta yake da wani shu'umin kallo ƙasa-ƙasa, har ta rufe fuska tana cewa"Sai kallona kake yi".

Ya ce"To ba dole ba, kin ƙi na zo gidanku, yau tun da Allah Ya sa kin zo hannu ai sai kin yi haƙuri da abin da za ki gani".

Ta ce"Me zan gani?"

Ya ce"Zan ta kallonki mana".

Ya ce"Ina za mu je mu yi break ɗin ne? Ina ne favorite ɗinki?"

Ta haɗiyi yawun fargaba ta ce"Ni ko'ina ma is ok".

Ya ce"Kenan ke kowane waje ma zuwa kike yi har mara class? To bari mu je inda na fi zuwa".

Ya ja mota suka tafi, yana tuƙi yana kallonta, komai na Ummi ya birge shi, ƴar daidai shi abun sha'awa, da dai yana ta cewa ba a haifi matar da zai aura ba, ashe an haife ta har ta girma ba su haɗu ba, maganar Ummi ta katse masa tunaninsa ta ce"Ni dai kar ka kifar da ni, kana driving kana kallona".

Ya ce"Sorry, na kasa riƙe kaina ne fa".

Suka yi dariya, suna fira har suka ƙarasa wani ƙasaitaccen waje, suka ci abinci, daga nan ya wuce da su wani wajen sha iska, sun zauna yake cewa"Baby me zan ba ki ne? Ba zai yiwu a ce haɗuwarmu ta farko ban ba ki wata kyauta ba".

Ummi ta ce"Ni fa iya kallonka ma ai kyauta ce, ba sai ka ba ni komai ba".

Ya ciro wayarsa ya dawo kusa da ita tana zaune a kujera shi yana tsaye ya sunkuyo ya yi musu hoto suna ta murmushi, ya koma ya zauna ya ce"Wow! Mun yi kyau, kin ga yadda kika haska ni kuwa?"

Ta ce"Ko kuma ka haska ni ba".

Ya ce"A'a ke ce kika haska ni kika fito da ni, yes ina da kyau amma ki sani ke kyaunki na musamman ne".

Ummi ta ji kanya ya fashe, Aisam ya ce"Ina wayarki?"

Gabanta ya faɗi, a gaskiya tana jin kunyar ta nuna masa wayarta, a da ba ta ganin laifin ƴar sakan ɗin wayar tata amma yanzu da ta ga ta shi sai sheƙi take da sulɓi ya sa ta raina tata, ta fara laluben jaka kamar mai neman wani abu, sai kuma ta ce"Kai, ai kuwa ina ga na manto wayata a gida".

Ya ce"Da gaske? Duk saboda zumuɗin ganina ko?"

Ta ce"Kamar ka sani".

Ya ce"To bari idan an gama taron sai mu je na siya miki wata, kin ga na samu kyautar da zan ɗaga na ce na yiwa masoyiyata a haɗuwarmu ta farko".

Ummi ta yi murmushi ta ce"Na gode sosai".

Ya ce"Babu godiya a tsakaninmu, ai wannan dolena ne, kana son mace ai dole ne komai ka samu nata ne, komai ta ce tana so ka sama mata nan take, wannan shi ne soyayya".

Nan suka lalace da fira har ƙarfe goma ta yi, sannan suka koma wajen taron, a hanya yake cewa"Ni fa sau ɗaya na taɓa zuwa wannan taron nasu".

Ummi ta ce"Me yasa?"

Ya ce"Sam babu class, abun nasu babu wani armashi, matan nan su yi ta yi maka magana wasu su roƙe ka ku yi hoto, sai ka ga wata gaja ta zo tana binka ƙarshe ma saboda raini ta ce tana sonka, irin kalar matan da ko a ƴan aikin gidana ba zan ɗauke su ba fa".

Ummi ta yi dariya, ya ce"Allah kuwa my Queen, ni saboda ke na zo, amma ke fa? Kin saba zuwa taron groups?"

Ta ce"Wallahi ban taɓa zuwa ba sai yau, ni ma kuma saboda kai na zo".

Ya ce"To me zai hana mu tafi wani wajen mu ci gaba da firarmu?"

Ta ce"Ka san fa sun ce idan aka yi taro uku mutum bai zo ba za su cire shi daga group ɗin".

Ya yi tsaki ya ce"Ƙarya suke yi".

Ta ce"Ni dai ina son zuwa".

Ya ce"To ba damuwa".

Suna shiga wajen ido ya dawo kansu, da sauri ɗaya daga cikin admin ya je ya raɗawa MC nan aka fara yi wa Aisam kirari da sannu da zuwa, shi kuma kansa ya fara fashewa yana murmushi yana ɗaga musu hannu, aka ba su waje suka zauna shi da Ummi, ƴan matan group da suke yi wa Ummi hassada abu ya ƙaru, don yawancinsu suna son Aisam wasu da yawa sun ce suna son shi bai saurare su ba, wasu kuma sai dai ya yi ta birge su, sai ga shi wannan yarinyar daga shigowarta group wai har sun jone.

Shi kuwa admin Yusuf wato mai group ɗin wani mugun kishi ne ya turnuƙe shi, ya gama tsara yau zai tunkari Ummi kuma ya bi ta har gidansu su daidaita, dama ya lura cikin kwanakin nan idan ya yi mata magana ma sai ta daɗe take dubawa, idan ya kira ta yawanci ba ta ɗagawa, ko ta ɗaga ta ce masa aiki take yi, ashe ita ta jone da Aisam, ya san ba lallai ya iya takara da Aisam ba, amma zai gwada, ya daure ya saki jiki ana ta harkoki don kar mutane su gane.

Paty ya yi paty an zo da yawa an yi bayanai sosai akan ci gaban group, an ci an sha, Ummi ta ci abinci saɓanin Aisam da bai ci komai ba, hankalinsa yana kan Ummi, bai bari ta tashi ta je ko'ina ba, su biyu suka yi taronsu, ƙarfe biyu sauta aka tashi.

Sun fito ta ce"To ni zan tafi sai mun yi waya ko?"

Ya ce"Kin manta da wayarki? Mu je na siya miki ni ma akwai inda zan je ƙarfe uku".

Suka shiga mota, suka je wani shagon siyar da wayoyi, ya siya mata waya mai kyau da tsada, har tsoro ya kama Ummi, amma ta dake don kar ya gane, kuma ya ƙi bari ta yi masa godiya, ya ce"Mu je na sauke ki, kin ga daga nan na ga gidanku sai ki saka mini ranar da zan fara zuwa zance".

Ummi ta ce"Na gode, ka bar shi kawai, zan koma da kaina".

Ya ce"No pls, idan na mayar da ke gida sai hankalina ya fi kwanciya".

Ta ce"Don Allah ka rufa mini asiri, ka je kawai na gode".

Ransa ya ɓaci, ya ce"Ok!"

Daga haka ya shiga motar ya ja ta ya tafi, sai jikin Ummi ya yi sanyi, ta ji ba ta ji daɗi ba sam, to amma ta ya za ta yarda ya kai ta gidanta? Ita ma ta tari adaidaita sahu ta shiga, tana jin faɗuwar gaba da rashin nutsuwa sun addabi zuciyarta.

Har cikin layin nasu ta sa adaidaita sahu ta shiga, saboda ta yi sauri ta shige don kar ƴan sa ido su ganta tun da doguwar rigar leshi ce a jikinta kuma ta yi rolling da mayafi iya kanta, ita ma ta san wannan shigar ba ta dace da matar aure ba, don haka ta sa ya ƙarasa da ita har ƙofar gida, da yake rana ta yi unguwar wayam sai tsirarun mutane, ta buɗe gidan ta shiga, ta buɗe ɗaki ta ajiye mayafinta, ta baje waya tana kallonta kawai ta ji an turo ƙofar gidan da ƙarfi, "Assalamu alaikum!".

Ta ji muryar Shamsu rass a kunnuwanta, wani tsalle ta yi ta duro daga gwadon ta bararraje, ta yi saurin kwasar kayan wayar da jakarta ta watsa su ƙarƙashin gado, Shamsu ya ƙaraso yana ƙara yin sallama, Ummi ta tashi tsaye alamun rashin gaskiya da kuma mamakin ganinsa suka bayyana a fuskarta, ya ƙarasa yana murmushi ya rungume ta, sai ta zame tana kallonsa tana dariya ta ce"Yaya Shamsu, dama yau za ka dawo?"

Ya ce"Tun ƙarfe goma na dawo, na tarar ba kya nan, ina kika je?"

Gabanta ya faɗi, ta ce"Ai kai ne ba ka faɗa mini za ka dawo yau ba".

Ya ce"Ina ta kiranki ba ki ɗauka ba ai, amma Ummi mun yi da ke duk inda za ki je sai kin kira ni kin faɗa mini ko? Me yasa kika fita ba ki sanar da ni ba?"

Ta ce"Ka yi haƙuri, auren ƙawata ne ake yi, jiya dinner aka yi shiyasa ban je ba, yau kuma da safe za a ɗaura aure can Sokoto za a kaita ka ga da wuri za su tafi, shi ne ta yi wuninta da safe, shi ne na je".

Ya ce"Zuwan ba laifi ba ne, amma ya kamata na san za ki je, kin ga ai ba hana ki fita nake yi ba ko?"

Ta gyaɗa masa kai alamar e.

Ya ce"Na dawo da kewarki, na zo na ga gida a rufe, sai gidan Umma na je na ajiye kayana na yi wanka na ci abinci, shi ne na zo na ga ko kin dawo".

Ummi ta yi murmushi ta ce"Sannu da zuwa".

Ya ce"Yawwa ke ma sannu da gida, kin yi kewata kuwa? Na ga kamar ma ƙiba kika yi, zo mu gani, zo ki faɗa ba ni labarin abin da ya faru ba na nan".

Ya jawo ta jikinsa, ta zame ta ce"Bari na yi sallah".

Ta yi wanka ta canza kaya ta yi sallah, sannan ta tashi za ta ɗora girki ya ce"Ni fa a ƙoshe nake, ki zo kawai mu yi fira sai na samo miki abin da za ki ci".

Ta ce"Ni ma na ci abinci a can gidan bikin".

Wuni guda cirr Shamsu ya hana ta buɗe gida, duk baƙin da aka yi sai ya ce kowaye ba za a buɗe ba, hutawa yake yi, sun gama wanka ya kwanta yana ta baccin gajiya, Ummi ta kafe shi da kallo, baƙi ne sosai mai dogon hanci da ƙananun idanuwa, dogo mai kaurin jiki da faɗi, saɓanin Aisam da yake siriri kamar ba ya cin abinci, yau ɗin sai ta ga munin Shamsu sosai, da ta tuna fushin da ya yi da ita sai ta ji duk ta rasa sukuni, shin ta yaya ma za ta ci gaba da sabuwar rayuwarta tun da mijinta ya dawo? Wannan tunanin ne ya hana ta sakat, duk ta firgice.

*** ***

*RANAR KUKA!*

BY

*SADIYA ABDULRAZAƘ*

*FIRST CLASS WRITERS*

MARUBUCIYAR Zuciyar mace Miji goma... Iya ruwa... Wani auren Matar shige... Da walakin Wutar ƙaiƙayi Alhakin so ***