PAGE 14
GIDAN ABBA Mama ta samo mai kura aka kwashe kayan Aisha tass, da ta zo tafiya Mama ta sake tsayar da ita ta ce"Don Allah Aisha wannan abin da ya faru ya zama sirri, don Allah kar kowa ya ji, kin san Abba ba zai ji daɗi ba, ki koma ɗakinki ki zauna tun da nan ɗin akwai barazana ga mutuncinki".
Aisha ta ce"In sha Allah babu wanda zai ji".
Mama ta ce"To kuma sai ki ji tsoron Allah, ki bar Abba ya dinga ajiye wani abun ba wai komai ya samu ya turo miki ba, irin wannan ne sai ki ga mutum ya kwashe shekaru yana bauta amma bai ajiye komai ba".
Aisha ta ce"In sha Allah haka ba zai faru ba Mama".
Ta shiga ɗakin da Baba yake ciki, ta yi sallama, ya amsa yana cewa"Aisha, har an sauke tukunyar ne?"
Ya yi maganar yana tashi zaune, saboda yunwar da yake ji, tun ɗazu Mama ta gama girki ta kawo masa, amma ya ƙi ci shi na Aisha yake jira.
Aisha ta ce"Ai Baba yau ban yi girki ba ma, sallama na zo yi maka".
Ya ce"Haba Aisha ke kuwa me yasa za ki dinga wasa da cikinki? Saboda Allah don za ki fita shikenan sai ki ƙi yin girki? To yanzu ma yadda rayuwar nan ta zama ai an daina zuwa gidan mutane da yunwa".
Ta ce"Baba can gidan namu fa zan koma har an yi gaba da kayan".
Baba ya zabura ya ce"Za ki koma ko za ki je sharar da kika saba?"
Ta ce"A'a komawa zan yo gabaɗaya".
Ya ce"Subhanallah! Ke kuwa Aisha me ya yi zafi har haka? Ko dai wani abun matar nan ta yi miki?"
Aisha ta ce"Wallahi babu komai Baba, kawai dai zan koma ɗin".
Baba ya ce"Aisha idan akan maganar Ashiru ne sai fa a daidaita ya daina kwana a gidan a rufe muku abunku".
Ta ce"A'a Baba ba akan haka ba ne".
Baba ya gyara zama ya ce"To ni dai na san ruwa ba ya tsami banza, a kan me..."
Mama da take laɓe tana sauraron su ta bankaɗo cikin ɗakin a fusace ta ce"Haba Malam ya isa haka don Allah! Ya za ka ritsa yarinya kana neman ƙure ta? Ta ce babu komai kuma har sai ta fara yi maka ƙarya?"
Baba ya ce"A'a Hansatu ba haka ba ne, ni fa abin da nake dubawa yarinyar nan amana ce Abba ya ba mu, don haka dole mu ji ko wani cikinmu ne ya ɓata mata rai ta yanke wannan hukuncin na guje mana".
Mama ta ce"Kai dai ka ce hankalinka ya tashi saboda za ka daina cin abincin kwaɗayi".
Ta kalli Aisha ta ce"Tashi ki tafi Allah Ya tsare, idan Muhibba ta dawo za a kawo ta"
Ta kalli Baba ta ce"Kai kuma za ka iya binta ka dinga cin abincin a can".
Aisha ta tashi ta fita, Baba da bai san ta tafi ba can anjima ya ce"Kin ga Aisha tsaya mu yi sulhu a samu maslaha, yanzu kira mini shi Abban a waya, idan ma shi ne yake ganin kamar cutarki ake yi ya ce ki koma sai na ji".
Jin shiru ya sa shi cewa"Aisha! Aisha ko dai kuka kike don na hana ki tafiya? Ni fa ina so na tabbatar ba ki tafi da haƙƙin wani ba ne".
Mama ta ce"Ai sai ka bi ta ka ci gaba da bayanin, tun tuni ta bar ɗakin nan kai ne ba ka san yadda take kallonka ba, dama ba ka nuna mata son abun duniya a fili ba, ai dole raini ya shiga tsakani".
Ta fice daga ɗakin ta bar shi yana ta sababi.
Tass Aisha ta gyara gidanta, ta ɗora girki ta zauna tana jin nutsuwa tana ratsa ta, ta ɗauki waya ta kira Baba ta faɗa masa ta koma gidanta, sannna ta ce gobe za ta aiko a ɗaukar mata katifa da kayanta, ya ce babu damuwa, sai da ta gama girki ta ci ta yi wanka, sannan ta kira Abba a waya, sun gaisa take cewa"Jiya wace addu'ar ka yi a kan Mama?"
Ya ce"Mene ne?"
Ta ce"To Mama dai haka kawai ina zaune ta ce ya kamata na koma ɗakina, yanzu haka zancen da nake yi maka iba can gidanmu".
Abba ya ce"Kin san dai ba na son wasa ko?"
Ta ce"Wallahi da gaske nake, ina can har na gyara komai, sai na ji ma kamar ban bar gidan na wani lokaci ba, sai nake ji a jikina kamar idan lokacin dawowarka ya yi zan ganka ka shigo".
Ya ce"Alhamdulillah! Tabbas addu'a ce ta karɓo, amma fa na yi mamaki, Aisha anya wani abu bai haɗa ku ba?"
Ta ce"Allah babu abin da ya haɗa mu, lafiyar Allah muka rabu, don ita ce ma ta kira mai kurar da ya kawo kayan".
Abba ya ji daɗi sosai ya ce"To Alhamdulillah! Wallahi har hankalina ya kwanta, don Allah ki kula da gidan sosai, za ki samu mai taya ki kwana?"
Ta ce"E ba za a rasa ba a maƙota, idan kuma Muhibba ta dawo nan ɗin shikenan".
Abba ya ɗan yi jim, sannan ya ce"A'a ki bar zancen yarinyar nan, saboda gaskiya dole zan zo ƙarshen watan nan fa, kuma da na yi wa Mama zancen ta hana, zan sake tuntuɓarta idan ta yarda shikenan idan ba ta yarda ba to zan zo a ɓoye ko sati ɗaya na yi, ba tare da kowa ya sani ba".
Aisha ta ce"Anya haka zai yiwu kuwa? Da ka haƙura har sai ta yarda ɗin".
Ya ce"Da kin san halin da nake ciki ba za ki ce haka ba, wallahi na gaji da kewarki, kamar ba zan jure ba, ina fargabar kar na shiga wata rayuwar, kin san zuciya ba ta da ƙashi".
Gabanta ya faɗi ta ce"Me kake nufi? Ka san ba za ka iya jurewa me yasa ka yarda ka tafi?"
Ya ce"Ni fa ba wani abun nake nufi ba, kawai na faɗa miki ne don ki daina dakatar da ni, nan da kwana goma zan zo".
Ta ce"To shikenan Allah Ya kawo ka lafiya".
Suka yi sallama ya kira Mama a waya, sai da gabanta ya faɗi da ta ji muryarsa, kawai tana ganin kamar Aishan ta faɗa masa komai, suka gaisa ta ce"Abba lafiya?"
Ya ce"Lafiya ƙalau, kira na yi mu gaisa".
Ta ce"To madallah ya aiki?"
Ya ce"Alhamdulillah!".
Ya ɗan yi jim kafin ya ce"Yanzu Aisha ta kira ni, take cewa wai ta koma can gidan namu".
Mama ta ce"E ɗazu ta tafi".
Abba ya ce"To Mama amma dai ba wani laifin ta yi ba ko?"
Mama ta ce"Ko ɗaya, wallahi babu abin da ta yiwa kowa, kawai dai na ga har yanzu ta ƙi sakewa ne, na duba na ga kar fa na shiga hakkin yarinyar nan Allah Ya tambaye ni ranar shaida na shiga uku, shi ne na ce kawai ta tafi ɗakinta".
Abba ya ce"To ma sha Allah, duk tsoro ya kama ni na zata wani abun ne ya faru".
Mama ta ce"Babu ɗaya ka kwantar da hankalinka ma. Amma gobe Muhibba za ta koma can ɗin".
Abba ya ce"Amma Mama na ga makarantar da take zuwa da nisa da nan ɗin, ni a ganina da kin rabu da Aishan kawai, kin san unguwarmu da yara, kuma na ga suna shigo mata, ba za ta rasa ɗan tayin kwana ba".
Mama ta ce"To shikenan, ni dama wai ganin tana da nauyi ne yasa na ce ko wanke-wanke sai ta dinga taya ta".
Ya ce"Babu komai ai ba ta da ganda".
Suka yi sallama yana ta yi mata godiya.
A ranar ta roƙi yaran maƙotanta su biyu suka fara zuwa taya ta kwana. Sosai Ashiru ya yi tijara saboda komawar Aisha gidan nan, don ma Mama ta taka masa burki, Baba kuwa kowa na gidan ya gaji da jin mitarsa babu abin da bai faɗa ba, kuma ya yi ya yi Mama ta kira masa Abba ta ƙi kira ta ce wayarsa ba ta shiga.
Washegari aka ɗakko mata katifarta, ta ƙara gyara ɗakinta. Ta samu nutsuwa sosai da kwanciyar hankali, ta yi irin shigar da take so tana juyi a gidanta ta dafa son ranta ta ci ta ƙoshi, babu Mama da kullum cikin fargabar ta yi mata laifi take, sati ɗaya da dawowarta ta yi tuwo mai rai da lafiya ta shirya ta kai wa Baba, ta yanke a ranta duk sati za ta dinga kai masa abinci, Baba yana zabga loma ya ce"Yanzu ke Aisha shikenan zaman can gidan ya fi yi miki?"
Ta ce"Baba ba haka ba ne".
Ya ce"Kamar ya ba haka ba ne? Idan ba hakan ba ne to ki dawo mana? Me yasa kika tafi?"
Ta yi shiru, ya ƙaraci surutansa, ba ta daɗe na ta tashi ta tafi.
Tun daga ranar ta fara shirin tarbar mijinta, ta yi kwalima, ta yi kitso ta yi ƙunshi, tana ta jin daɗi, gefe ɗaya kuma tana jin rashin nutsuwa saboda tana ganin kamar bai dace ba a ce ya zo garin bai je gidan iyayensa ba, to amma ya za a yi? Wasu iyayen su ne suke janyowa ƴaƴansu su munafurce su.
Ranar da Abba ya dawo saukar asuba ya yi, saboda kwana suka yi a hanya, ƙarfe shida ya ƙaraso gida cike da shauƙin ganin matarsa, suka rungume juna kamar kar su rabu, har ƙwallar farinciki ta yi saboda yadda ta yi kewar shi, ta kai masa ruwan wanka kafin ya fito ta kawo masa shayi da biredi sannan ta je ta hau haɗa masa doya da ƙwai, suka sha fira kafin ya kwanta baccin gajiya.
Wunu cir suka yi a gida suna fira, aikin girkin ma tare suke yi, sai yanzu yake ƙara jin ya yi kewarta sosai, ji yake kamar kar ya koma, ko kuma su tafi tare, sun gama cin abincin dare yake cewa"Yanzu Aisha babu yadda za a yi ki bi ni mu tafi? Wallahi ina shiga wani hali".
Ta ce"Idan akwai yadda za a yi ai za ka fi ni sani".
Ya ce"Kai! Wannan wace irin ƙaddara ce, ina da mata amma a can wani gwauron ma ya fi ni gata, wai ke ba kya jin kewata? Kina jin daɗin zama a gidan nan ke kaɗai?"
Ta ce"Allah ne kaɗai Ya san yadda nake jin kewarka, kuma maganar jin daɗi kai ma ka san duk jin daɗin da zan samu babu mijina a kusa da ni sunan shi lami, don haka dauriya kawai nake saboda kar na raunana zuciyarka".
Ya ce"Komai zai wuce in sha Allah!".
Ya yo mata tsaraba da yawa, har jikinta ya yi sanyi ta ce"Yanzu haka za a ce wannan tsarabar ni kaɗai ban da Mama?"
Ya ce"To ba ita ce ta ja ba? Ko so kike a kai mata tsaraba ta san na zo garin?"
Aisha ta ce"Ni fa sai nake ganin kamar ma wannan zuwan naka ba zai ɓoyu ba, za ta iya sani, tun da za ka iya fita wani ya ganka ko cikin abokanka".
Ya ce"To shikenan ki yi mini baki a gan ni ɗin".
Ta yi dariya ta ce"Ai ni ma ba na fatan haka".
Kwanansa uku a gidan, masallaci kawai yake fita saboda tsaro, yau yana kwance da safe ya kira Mama a waya suna gaisawa, Aisha kuma tama kitchen tana haɗa musu abun karyawa, daga ƙofar ɗaki ta ɗan ɗaga murya ta ce"Yanzu za ka yi wanka na ɗora maka maka ruwan zafi?"
Ya yi saurin katse kiran sannan ya amsa mata da e ta ɗora, ba tare da sanin cewa Mama ta jiyo muryar Aisha tarr ba, ta bi wayar da kallon mamaki, gabanta yana faɗuwa a fili ta ce"Me zai kawo muryar Aisha kusa da Abba? A ɗora maka ruwan zafi" Mama ta maimaita maganar Aishar.
Ta ce"Tabɗijan! Kar dai yaron nan dawowa ya yi ya munafurce ni, amma anya kuwa Abba zai iya yi mini haka?"
Baba dake zaune yana jinta ya ce"To Hansatu dai tafiya ta tafi kenan, kin fara susucewa, ai ni dai na san hakkin yarinyar nan ba lallai ya bar ki ba, yanzu ga irinta nan kina ta sambatu ke kaɗai".
Mama ba ta ce komai ba ta tashi ta saka hijjabi, tana ce masa "Malam bari na je gidan Abba, ashe Aisha ba ta da lafiya".
Ya ce"To subhanallah! Allah Ya sawaƙe, me ya same ta?"
Ta ce"Ni ma ban sani ba sai na je zan ji".
Ya ce"To don Allah ki yi mata sannu, da yamma ni ma zan je".
Shiru Abba ya yi yana tunanin Mama ta ji maganar Aisha ko ba ta ji ba? Sai kuma ya watsar ya bar shi a ba ta ji ba, sun gama karyawa kenan ko kwashe kwanukan Aisha ba ta yi ba suka ji ana buga ƙofa, sai da gaban Abba ya faɗi, Aisha ta tashi za ta buɗe ya ce"Ki tambaya ki ji ko waye".
Ta ɗaga murya ta ce"Waye?"
Mama ta ce"Hansatu ce!".
A tare ƙirjinsu ya buga da ƙarfi, Aisha har da ɗora hannu a ka, Mama kuma ta ci gaba da bugawa.
WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE AKAN NAIRA 500 KACAL
8028966015 Sadiya Abdulrazak opay
*** ***
Abun da kike so shi zaki zaba hjyta☺️💃 Duk abinda ranki yake so na kitchen shi zaa siya maki da kudin adashenki…Kikwashi kayanki tamkar kyauta🤭💃💃 Gold Kitchen Adashe dinmu ba wasa aciki! 100% aminci, 100% sauki !kayan kitchen masu kyau da aminci na jiranki!
*RANAR KUKA!*
BY
*SADIYA ABDULRAZAƘ*
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR Zuciyar mace Miji goma... Iya ruwa... Wani auren Matar shige... Da walakin Wutar ƙaiƙayi Alhakin so ***