PAGE 15
Abba ya ce"Mama! Dama tana zuwa gidan nan?"
Aisha ta ce"Wallahi ba ta zuwa, tun da na dawo ba ta zo ba".
Ya ce"To ai kuwa idan babu rami babu abin da zai kawo maganar rami, tabbas Mama ta ji muryarki ɗazun nan da muna waya, ko kuma ta samu labarin na zo".
Aisha ta ce"Gaskiya haka kawai ba za ta yi sammako haka ba, yanzu ya kenan?"
Ya ce"Je ki buɗe kawai na miƙa wuya".
Aisha ta ce"Ka rufa mana asiri, wallahi duka ni za a ɗorawa laifin, ka ɓuya kawai".
Ya ce"Amma Aisha..."
Ta katse shi da faɗin"Ka je ko ƙarƙashin gafo ka shiga don Allah ko cikin sif".
Ya ce"Haba Aisha, ta ya zan shiga ƙarƙashin gado? Ina laifin ma banɗaki?"
Ta ce"Za ta iya shiga banɗaki, ka tafi don Allah wannan ɓata lokacin zai ƙara mata zarginmu".
Ya kwasa da sauri ya shiga ɗaki ya shiga ƙarƙashin gado ya kwanta flat, sannan Aisha ta je ta buɗe, ta ga Mama fuska babu yabo babu fallasa, ta ɗan yi yaƙe ta ce"Yi haƙuri Mama a banɗaki nake ne".
Mama tana yi mata kallon tsaf ta ce"To, ba ni waje mana ko na koma?"
Aisha ta yi saurin mata ta shigo tana yamutse fuska, ta ja ta tsaya, Aisha ta ce"Mama ki shiga".
Mama ta shiga falon da sallama, ganin farko idonta ya sauka a kan kwanukan da suka gama cin abinci, kofuna biyu ga plate ɗin da aka ci indomi da cokali guda biyu a ciki, wannan ya ƙara ƙarfafa zarginta, Aisha da ba ta yi tunanin komai ba ta fara harhaɗa kwanukan ta kai kitchen, tana dawowa Mama cikin bugar ciki ta ce"Ina Abban yake, ko bai ji shigowata ba?"
Gaban Aisha ya faɗi, amma ta yi dauriyar cewa"Abba kuma?"
Mama ta ce"E mana, ko a tunaninku ban san ya dawo garin ba?"
Kamar Aisha ta saddaƙar sai kuma ta yi tunanin Mama bugar cikinta take yi, ta daure ta ce"Mama ta ya za a yi Abba ya dawo garin nan ba ki sani ba? Wane ne ya ce ya dawo?"
Mama ta ce"To ƙila wanda ya faɗa min ɗin bai ji daidai ba".
Aisha ta ce"Gaskiya dai".
Sai kuma ta ce"Amma kafin ki kwashe kwanukan nan na ga kofuna biyu cokula biyu, ke da wa kuka ci? Ko kuwa da hannu biyu-biyu kike ci?"
Zuciyar Aisha ta buga, ta ce"Dama yarinyar da take taya ni kwana ce ta karya a nan".
Mama ta ce"A lallai! Wani abun sai a gidan Alhaji Abba, yanzu a zamanin nan na tsadar rayuwa a ce har ƴar tayin kwana ma a nan take cin abinci? Hmmm kodayake ban san abin da yake jibge miki ba".
Aisha ta ce"Mama yau ne fa ta karya, saboda babarta ba ta nan".
Mama ta ce"Ai shikenan".
Sai ta sakko daga kujerar ta zauna a ƙasa alamar ba ta da niyyar tafiya ta ce"Kira min Abban a waya mu gaisa".
Gaban Aisha ya ƙara faɗuwa saboda ta san idan ta kira za a iya jiyo ƙarar ringin ɗin, Allah ma ya taimake ta wayar tana can ɗakin gadon, sai ta ce"To bari na ɗakko"
Tana shiga ta leƙa ƙarƙashin gadon ta hango shi yana muzurai, ta ce"Ina wayarka?"
Ya ce"Tana kan mudubi".
Ta ce"Ka daure kar ka fito don Allah, ka ga na faɗa mata ƙarya ne ba ka dawo ba".
Ya ce"To, Allah Ya sa ta tafi da wuri, don har na gaji".
Ta ɗauki wayar ta kashe ta, ta saka a ƙarƙashin filo, sannan ta ɗauki tata ta tafi falon tana neman lambar, ta saka a hans free ta yadda Mama take jin komai, nan aka sanar da cewar wayar a kashe take, Mama ta ce"Ko dai ba ki da kati ne? Ungo kira ta wayata".
Aisha ta karɓa ta kira nan ma duk amsa ɗaya ce, Mama ta ce"Ko a ina ya saka wayar?"
Wata zuciyar ta fara faɗa mata ko dai ba muryar Aisha ta ji ba? Idan kuwa haka ne to kenan Abba ya fara neman matan banza ne da har ta ji muryar mace tana maganar ruwan wanka?"
Mama ta ce"Amma Aisha yaushe rabon da ku yi waya da shi?"
Ta ce"Jiya da daddare ne".
Mama ta ce"Ai shikenan".
Kamar ta tashi ta tafi sai kuma zuciya take raya mata ƙila fita ya yi yanzu ko anjima zai dawo gara ta zauna ta ga abin da ya turewa buzu naɗi, don haka ta janyo fulon kujera ta kishingiɗa ta kunna rediyo a wayarta.
Hakan ya sake jefa Aisha cikin fargaba, da kuma gasgata tabbas Mama tana zarginsu, don ba ta taɓa zuwa gidanta ta kwanta ba, ta fara salati a ranta, ta zauna jigum kafin ta tashi ta ce"Mama bari na yi wanke-wanke".
Mama ta ce"To".
Aisha ta fita ta shiga ɗakin gadon a sanyaye ta ce"Abba".
Ya ce"Na'am ta tashi na fito?"
Ta ce"Akwai matsala fa, gaskiya Mama tana zarginmu, ka ga fa ta kwanta ba ta da niyyar tafiya".
Ya ce"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Kenan ni haka zan dawwama a nan har sai sanda ta tafi?"
Aisha ta ce"Haba Abba, ya ana ga yaƙi kana ya ƙura? Ni ina fargabar abin da zai faru idan ta san kana cikin gidan nan kai kana maganar dawwama a ƙarƙashin gado?"
Ya ce"A'a dole fa na yi, kin san a yadda nake kuwa? Sau uku kaina yana gwaruwa da karagar gadon nan, na danne kirjina numfashina yana neman sarƙewa, gaskiya fitowa zan yi".
Aisha ta ce"Ka rufa mana asiri mana, ka ƙara haƙuri har ta tafin don Allah, idan tsautsayi ya sa ta leƙo fa?"
Ta fita ta fara aikin gidan, tana yi tana kallon falon, tana mamaki ganin Mama ba ta da alamun fitowa, sai yanzu ma ta tuna ba ta yi mata tayin abinci ba, ta koma kitchen ta haɗo mata shayi da biredi ta soya ƙwai biyu ta kawo mata, ta ajiye tana cewa"Mama ki tashi ki karya".
Mama ta ce"To ajiye sai na tashi".
Aisha ta koma ta ci gaba da aikinta, ta gama ta shiga wanka, Mama tana jin ƙarar ruwa zuciyarta ta raya mata ta leƙa ɗakin gadon ta gani, saboda zuwa yanzu ta san indai da gaske ya zo garin to yana cikin gidan nan, don daɗewar da ta yi ya ci a ce idan fita ya yi ya dawo, don haka ta tashi ta shiga ɗakin gadon, tsam ta tsaya tana ƙarewa ɗakin kallo, Abba dake jigace a ƙasan gado ya hango zanin Mama, duk a zatonsa Aishar ce, a wahalce ya ce"Aisha ni fa na gaji, kamar zan mutu gaskiya fitowa zan yi komai zai faru ya faru".
Salatin da Mama ta rafka ne ya sa zuciyarsa bugawa da ƙarfi, Mama ta waiwaya don murya kawai ta ji babu mutum ta ce"Abba! Kana ina? Ni za ka yi wa haka?"
Ba ta jira ya fito ba ta juya ta bar ɗakin, shi kuma ya fito da sauri ya same ta tana saka hijjabi ranta a ɓace, daidai nan Aisha ta fito daga wanka, ta saki bokitin hannunta cikin firgici.
Abba ya ƙaraso gabanta ya ce"Mama..."
Ta ɗaga masa hannu ta ce"Kar ka ce mini komai! Ba dai ka zaɓi mace a kaina ba? Abba na ɗauki cikinka a jikina tsawon wata tara, na yi naƙudarka, ban taɓa shan wahalar da na sha a haihuwarka ba, na jigata na daɗe ina naƙuda amma da ka tashi fitowa ta hannu ka taho, hannu kawai kake miƙowa, da ƙyar na haife ka, na zo na yi zaman shayarwa da raino, har ka zama mutum, amma a ce Abba yau ni ce wacce za ka zaɓi mace a kaina, yanzu wannan ce sakayyar da za ka yi mini?"
Kamar zai yi kuka ya ce"Don Allah Mama ki fahimce ni".
Ta ce"Ba zan taɓa fahimtarka na, wannan matar taka ba alkhairi ba ce a rayuwarka, ni ba zan yi maka dole ka bi umarnina ba, amma a yau sai ka tsaɓi ɗaya tsakanin ni da ita! Idan ka zaɓe ni to babu kai babu ita har abada, yanzu a nan za ka sake ta, idan kuwa ita ka zaɓa babu ni babu kai! Kada ka sake zuwa inda nake ka je ka rayu da matarka".
Abba ya shiga wani irin yanayi mara misali, shi kaɗai ya san yadda yake ji a zuciyarsa, wanne zai zaɓa tsakanin yankakken kare da mushen rago? A raunace ya ce"Mama babu wanda zan ɗauka a nan, ke mahaifiyata ce ba zan taɓa canza ki ba har abada, matsayinki a wajena ya wuce na haɗa matata da ke".
Mama ta ji kanta ya fashe, kuma ta ji sanyi a zuciyarta, saboda ko banza ya nuna mata shi ɗanta ne kuma ɗan halak, sannan Aisha ta gane har yanzu ba ta gama janye shi ba, ta sake haɗe rai ta ce"Abba wannan zantukan naka ba za su yi tasiri a zuciyata ba, kawai idan ita ka zaɓa ka faɗa mini na tafi, idan kuma ni ka zaɓa ka sallame ta yanzu a gabana".
Abba ya ce"Mama ke na zaɓa, amma..."
Ta katse shi da faɗin"Kar ka sake na ji amma, ka sallame ta kawai, domin duk macen da za ta so raba ka da mahaifanka ba matar zama ba ce".
Aisha da take ta hawaye ta durƙusa ta saka gwiwarta a ƙasa cikin kuka ta ce"Mama mun yi kuskure, amma don Allah ki yi haƙuri ki yafe mana, in sha Allah ba zan sake marmarin zuwan shi garin nan ba, ko da kuwa ya tafi kenan har abada". Idan ka ji a yadda ta yi maganar za ka gane ba ta cikin nutsuwarta.
Mama ta ce"Ka ji ko? To yanzu ai sai ka yi wa kanka hisabi ka gane cewa yarinyar nan ba sonka take yi ba, tun da har ta yarda idan ka tafi kar ka dawo har abada, wato ke tun da ya ba ki mafaka kina zaune a muhallinsa yana turo miki kuɗi kina cin abin da ranki yake so, ki yi sutura ko?"
Aisha ta fara girgiza kai alamar a'a.
Mama ta kalli Abba ta ce"Ka san dai ba kai ka haife ni ba ko? To na gaji da jira ka sallame ni zan tafi".
Shi ma sai ya durƙusa a gabanta ya ce"Mama don Allah..."
Mama ta ce"Ni fa na gama magana".
Ya ce"Don Allah Mama ki yi yi haƙuri ba zan iya rabuwa da Aisha ba".
Mama ta ce"To ni kuma za ka rabu da ni har abada".
Ta fara tafiya za ta tafi, ya tashi ya sha gabanta ya ce"Shikenan Mama na ji na yarda".
Da sauri Aisha ta ce"Me kake nufi?"
Ya kalli Mama ya ga shi take kallo, ya mayar da dubansa ga Aishar da ƙyar ya furta"Aisha, ki je gida".
Tashin hankali ya rufto mata ta ce"Na je gida?"
Cikin ƙarfin hali ya ce"E ki je gida, zan aiko miki da saƙo".
Aisha ta shiga ɗaki tana fashewa da kuka.
Mama sai ta ji zuciyarta ta karye, ta ji tausayin ɗanta amma ta dake ba ta nuna ba, ta juya ta fice daga gidan, ya bi bayanta ya tsayar mata da adidaitasahu ta shiga ta tafi sannan ya koma gidan.
Ya tarar da Aisha tana ta loda kaya a akwati, ya ce"Aisha don Allah ki yi haƙuri, shi umarnin iyaye..."
Ta katse shi cikin kuka ta ce"Wallahi na fahimce ka, babu komai, Allah Ya sa hakan shi ya fi alkhairi".
Ya ce"Ni fa ban sake ki ba, kawai dai ki je gida".
Ta ce"Ba zan yi zaman rashin sanin makomata ba, saboda haka dole ka sake ni kafin na bar gidan nan!".
LITTAFIN NAN NA KUƊI NE AKAN NAIRA 500 8028966015 Sadiya Abdulrazak opay
*** ***
Abun da kike so shi zaki zaba hjyta☺️💃 Duk abinda ranki yake so na kitchen shi zaa siya maki da kudin adashenki…Kikwashi kayanki tamkar kyauta🤭💃💃 Gold Kitchen Adashe dinmu ba wasa aciki! 100% aminci, 100% sauki !kayan kitchen masu kyau da aminci na jiranki!
*RANAR KUKA!*
BY
*SADIYA ABDULRAZAƘ*
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR Zuciyar mace Miji goma... Iya ruwa... Wani auren Matar shige... Da walakin Wutar ƙaiƙayi Alhakin so ***