RAUNIN DA BA A GANI

Chapter 6:RDBG

by @meefatinkwriters99

RAUNIN DA BA A GANI 

Meefat ink ✍️ writers 

“ toh insha Allah, amma hamma kundawomin da abinda nace kuzomin da shi?” “karki damu ai dole ma” nan dai suka cigabada
wayarsu shiko azan sai murmushi yake dan yakan iya jiyo wayarta su kuma yana jida kanwar tasa sosai. 
Haka dai yagama cin abincin sa yamike zai fita sai Jay yace “cab zaka tara”, juyawa azan yayi ya harari Jay tunuwa dayayi keyn motarma bata hannunsa. 
Suna isowa guests house dinsu suka shiga direct ciki sai Jay yaduba wrist watch dake hannunsa ganin bai wuce 40min yarage ba yace “kaganiko 40min yarage. Azan bai tankaba ya wuce fridge ya dauki smoothie a time din Jay yafito da akwatinsu yana cewa su tafi, yana gama sha ya mike zai shiga daki sai ya jiyo muryar Jay yana cewa “wai me kuma zaka dauko aciki” “trolley na zan dauka” “gashinan ai na fito maka dashi”dariya ne yaso kubcewa azan sanin yau ya kure abukinnasa. 
Isowarsu kenan suka wuce direct gida, securities suna tamusu sannu dazuwa. Jannat ce ta hangosu daga sama sai tayi saurin sauka ta nufi wajensu dadai suna saukowa daga mutan, dagudu tazo ta rungume azan tana dariya shima yana dariyan ya dago ta yana cewa “iyye haka baby Jannat tagirma amma tana abu kamar baby” noke kafada Jannat tayi tace “kaimafa kace baby ni hamma am still young” juyawanda zata yi sai taga Jay “laaa hamma Jay” ta fada tana rungumarasa “ai nayi fushi tunda azan kika gani ko?” sai tayi dariya tace “Allah nayi missing dinku sosai. Side din mamy suka nufa shida Jannat bayan sun shiga parlourn suka zauna Jannat zaune a cinyar azan sai hira take masa. 
Mamy ce ke saukowa daga stairs dai dai time din da Jay ya shigo yana masifa “daka shigo kabarni da kaya ni kadai zan shigo maka dasu ko?”dariya azan yafara yana cewa “meyasa Baka barwa securities ba, wai meke damun kane yau sai masifa kakemin” “ko dai ka bata masa raine” juyawa sukayi atare suna kallon inda suka jiyo muryar mamy, tafiya sukayi dukkansu biyun suka rungumeta, hugging dinsu itama tayi tana shafa kawunansu “Anne, seniözledim”( mom, I miss you ) a yaren turkey sai mamy tace “kajishi jabir, wanda dakyar aka janyoshi ya dawo ne yake cewa yayi kewata” “kyaleshi mamy ai sai Kinga abunda yayimin yau kafin mutashi” cewar Jay “kaima kasan babyn nawa sai a hankali, ko yaushe zai fara sabawa da zama a kasar sa?” cewar mamy, dan azan ya kawar da maganan sai yace “mamy ina sweet angels dina ne” “suna part din ayya, yanzu kutashi kuje kugaisheda mutanen gidan daga nan kuzo kuyi freshening up kuci abinci then sai hutu” “mamy let's start resting first"azan yafada cikin shagwaba, tsaki Jay yayi tareda cewa “wai kai yaushe zaka daina shagwaba ne kamar bakada kanne” itade Jannat sai dariya take da dramar yayyinnata sai tamike tamusu sallama da niyyar anjima zatazo ta karbi tsarabar ta. Hararar jay azan yakeyi har ya mike suka fice da tsarabar kowa a hannayensu, yayinda mamy keyimusu addu'ar kariya daga mugun baki.