Chapter 7:RDBG
RAUNIN DA BA A GANI
Meefat ink ✍️ writers
Tun bayanda adamawa state University ta sanar da ranar gudanarda bikin (award recognition day ) jami'ar ta sauya, kowani malam da dalibi nata shirye shirye domin ganin an gudanarda taron cikin tsari da martaba.
Babban dakin taro na jami'ar cike yake da manyan shugabannin makarantar, a tsakiyar dakin akwai dogon table da kujeru kewaye dashi, asaman table din akwai files, takardun kasafin kudi, jerin sunayen daliban da zaabawa lambobin yabo, dakuma takardunda suka shafi bakinda ake son gayyata.
A setin table dinne vice Chancellor yake zaune gefensa kuma deputy vice Chancellor (academic ) da registrer, sauran kijerun kuma sun kasance Burser, Dean of student's affairs, Dean na faculty of pharmacy, Head of departments, public relations officer da protocol officer. Dukkansu sun kasance cikin nutsuwa domin taron bakarami bane, VC ya daga idanunsa daga kan takardar dayake dubawa yace “good morning everyone” “good morning sir” kowa ya amsa sai VC yacigaba “kamar yadda kowa yasani mun taru a yaune domin mu kammala shirye shiryen University award and recognition day, wannan event bana faculty dayabane, it represents the entire University, so we have to be careful with the arrangements”.sai registrer yabude file dinsa yace “yes sir we have the preliminary programme. Amma akwai wasu abubuwa da har yanzu muke bukatan muyi finalising musamman guest list, protocol, sitting arrangements da invitations”.VC ya gyada yace “ok let's start from the guest list, who are the major personalities we want to invite?” Dean na faculty of pharmacy ya dan gyara zama sannan yace “
Sir ina ganin yakamata mugayyaci wasu Prominents Individuals da suke da connection da Universityn, musamman wadanda suke contributing to education and community development ”sai deputy vice Chancellor yace “ I agree, we should also consider notable alumni, respected community leaders, major business personalities and people who have contributed to the development of education in the state” sai protocol officer yafara rubutu “sir what about Alhaji dawud yola?”, sai wasu daga cikin jami'an suka kalli juna, Dean na pharmacy ya gyada kai yace “Alhaji dawud yola? Yes that's actually a very good suggestion, his presence would give the event more prestige “sai Burser yayi murmushi yace “kuma sunansa sanannene sosai, his presence alone can attract attention”, VC ya kalli registrer yace “have we check his availability?” “mun bincika sir” “then?” VC yatambaya sai registrer yace “akwai matsala guda daya Alhaji dawud yola baya kasar dan abayananda mukasamu baya cikin kasar a yanzu”sai Dean na pharmacy yace “that's unfortunate I was hoping we could have him as our distinguished guest” deputy vice Chancellor yajingina da kujera sannan yace “maybe we should consider someone else”, protocol officer yaduba jerin sunayen sannan yace “sir there is another possibility” “go ahead” cewar VC “ naji labari cewa dan Alhaji yola dake rayuwa a kasar waje yayi landing a yola yau dinnan"sai Dean yace “is that the young man dake leading yola holdings branch a turkey?” “eh sir shine tareda danuwansa suke leading yola investment turkey.”
Sai deputy vice Chancellor ya kalli VC yace “to idan mahaifinsa bayanan why don't we invite the son?”sai Dean na pharmacy ya amsa dafadin “in fact I think that maybe better. We don't necessarily have to invite him as his father's representative, we can invite him in his own capacity” sai kuma registrer ya tambaya “sir should we state in the invitation that he is coming on behalf of his father?” ananne VC ya girgiza kai yace “ a'a, I don't think we should make it sound like he's merely replacing his father”, sai ya daga hannu yace “invite him as azan yola, a distinguished guest, we can mention that his father is unavailable, but the invitation should be addressed to him personally”Dean na pharmacy ya gyada kai yace “yes sir, that sounds more appropriate” public relation officer yace “also if he accept, we should prepare a proper media and protocol arrangement.”sai protocol officer ya rubuta hakan a littafinsa “noted sir” VC ya kalli registrer yace “add his name to the final guest list, prepare an official invitation vimmediately “yes sir” also make sure the invitation reaches him before the end of the week” registrer ya gyada kai yace “consider it done sir"sai VC ya rufe files din sannan yace “to yanzu mu wuce zuwa award recepients”da haka aka cigaba da tattaunawa akan sunayen dalibai da sukayi fice, malamai daza a girmama, wadanda zasu gabatarda jawabai, da kuma wadanda zasu bada lambobin yabo.
Daga karshe VC yace “gentlemen and ladies, I want this event to be memorable. Not just because of the awards, but bacause of the way we conduct ourselves, everything must be professional” kowa ya amsa da girmamawa.
Su azan sashen mama suka fara Shiga a matsayinta na first wife wanda takeda yara shidda ciki harda Jannat, macece wanda baka sanin abunda ke zuciyarta kullum cikin yake take baa iya gane farincikinta ko akasin hakan, shigowarsu parlourn kenan suka sameta kishingide akan kujera sai suka tsugunna suka gaisheta “saukan yaushe haka zuwa ba notice” murmushi azan yayi sai yace.