RAUNIN DA BA A GANI

Chapter 8:RDBG

by @meefatinkwriters99

RAUNIN DA BA A GANI 

Meefat ink ✍️ writers 

Tsugunnawa sukayi cikin girmamawa suka gaisheta “saukan yaushe haka zuwa ba notice” cewar mama sai azan yayi murmushi yace “yanzu bai dade ba muka iso” jiyo muryar khadija sukayi cikin kaudi take cewa “kai wanake gani kamar hamma Jay wai dan Allah kaine ko dai idonane kemin gizau” sai ta karaso tareda tabashi “wallahi dagaske shine mama” sai kuma tayi hugging dinsa cikin murna tana cewa “I really miss you hamma hope dai zaku dade this time around” cireta yayi ajikinsa tareda mikewa sai yace “mama bara muwuce part din umma” “a a da kuntsaya khadija tasa muku abinci kuncin tukun” “a'a babu komai wallahi akoshe ma muke sai dai in wani lokacin”fadin Jay tareda juyawa ya nufi kofar fita dan Allah ma yasani bakaunar ganin yarinyar yakeba da haka sai azan ya musu sallama Shima yafita. Direct side din umma suka nufa kamar kullum ta amsa musu sama sama, umma itace second wife a matan Alhaji dawud,kuma ita macece wanda bata shiga harkar kowa agidan baruwanta da kowa tanada yara hudu kuma duk matane, sai mamy ta karshe wacce takasance y'ar turkiyya gaba da baya. Azan ne ya tashi yafita sannan Jay ya bi bayanshi zuwa side din ayya wanda yakeda tabbacin kannennasa suna can, sai tsokanar Jay azan yake da abunda khadija ta masa yana dariya, cikin takaici jaya yace “wallahi yarinyar nan batada hankali dude, kuma fa agaban mamarta” sai azan yace “tunda kaga haka that means da saninta takeyi” “kumafa hakane hmm” ai sai azan ya sake tuntsurewa da dariya yana hugging din Jay ganin yanda yayi kicin kicin da fuska, sai yace “ nifa yanda tazo tayi hugging dinka nefa yabani dariya ko nidinma bata like she didn't even realise that I was there, turesa Jay yayi yana cewa “in akace ka dade a Nigeria kodan hausanka ya nuna bakaji” “who told you ban iya hausa ba, kasan nafika” “ kafini? Kaida yanzu kakasa hada complete sentence da hausa” cewar Jay “eh nafika, I know more than you” sai Jay ya girgiza kai yace “wai a haka kana karatun hausa books for improvement” “whatever, I know more than you” “okay Mr experts hausa, lemme hear you speak”adaidai suna isowa part din sai azan yabashi amsa da “just wait I will show you cewa I know more than you”. 
Tun kafin su karasa shiga parlourn wata murya ta daki kunnuwansu “toh ni lokacin bacci na yayi kutashi kuje gurin ubanku kurufemun kofata” wata budurwa wanda akiyasi bazata wuce 22 bane ta daga kyawawan idanunta ta sauke akan kakartasu yayinda dayan ke bata amsa da “ayya kinmanta daddy yayi tafiya UK ko dai tsufanne yafara sakaki mantuwa ne"tafada tana shirin guduwa dan tasan tsaf ayya zata iya jifanta da pillow, duk da cewa ayya bata son mamy amma hakan bai shafi yarantaba dukda tana nuna banbanci tsakanin ta da sauran matan amma bata tabayi akan yaranba kuma koda zata zage mamynne bata taba yi agaban yaran hakanne yasa suma yaran suka sake da ita sai dai idan har yayan mamy na wajen ayya tofa bazakaga kowa daga cikin yaran ba sai dai Jannat . Murmushi azan yayi azuciyarshi yace “wannan muryar dai bata canja ba”. Da sallama suka shiga, nisha ce tafara hangosu ai sai tasaki ihu tace “hamma azan hamma jay” tatafi wajensu da gudu sai alokacin riyya ta ankara dasu sai itama tabiyo bayan kanwartata tana murmushi mai kamada dariya, nisha ta rungume Jay riyya kuma azan “hamma kamanta damu” nisha ta fada cikida shagwaba sai azan yayi murmushi yace “nine namanta daku ko kuma kune bakwasun zuwa turkey kuganni” “haka kullum kuke cewa kai da hamma Jay” cewar riyya tana kallon Jay. Ayya kuwa tana zaune a kujera tana musu kallon zakuzo kusamenine ai, sai azan ya karaso wajenta ya dan tsugunna yace “barka da dare ayya” sai ta amsa atakaice ta kawar da kai, sai kuma ta juya tana kallonsa tace “ sai yanzu kasamu lokacin zuwa kenan kai da dan uwannaka” sai azan yadaga kai yana murmushi sanin kawai so take tabashi ciwon kai shikuma yasan yanda zaiyi da ita sai yace “ ayya….