Hs 28
by @legendspen
_Page 28_
"Zinariyar tana tafe a baya cikin ƙasaita, cikin isahhhhh a tare da 'yan uwanta.
Ga aji..... ga ilimi.
Ga isa da kwalliya kaman wata ɗawisu.
Ga nasaba....... Duk a gurin Senate ɗinan ke kaɗai gayya.
Kin kira taro an amsa, kin tara gari, garin ya haɗu gaba ɗaya.
Amasu kyawu ita ɗin mai kyawu ce ajin farko.
Irin kyan da zaka ji masana na bada labarin guda ɗaya akeyi a nahiya.
Kyawunta ya kai kyawun da mutum zai bada labari, ya doki ƙirji ya ce ga mai kyawu ta iso.
Murmushinta kaɗai abun ka kalla ka ƙara kallo ne.
Murmushin da yake sanyaya zuciyar dukkan wani masoyi.
Murmushi da ko a hanya idan ka kalli murmushin nan sai ka ce wayyo Allah kalon Senate bai isheni haka ba.
A kyawu keɗin za a bada labarin kina sa kyawu.
A aminci, amintaciyace a cikin bayi.
Muna ƙarai muku lale, muna ƙarai muku marhabun, muna ƙarai muku sallama Assalamu alaikum, warahmatullahi ta ala wabarakatuhum.
Yau kuma da wanan kirarin Bhatool ta ƙarasa mazauninta, Masu hoto da bidiyo sun cika wajen kamar za ayi daukan film, banda manyan wayoyi da suke ta shi wajen, daga ɓari daya adon da ƙawayen Mom su ka yi yau, ya ninka na jiya dau dari dan kamar anyi musi gorin gwala-gwalai, kowacce fantamawa take da Gwala-gwala da leshi mai tsada.
Abincin yau har ya fi na jiya, liƙin da aka yi yau ma ya fi na jiya, komai ci gaba aka samu.
Sai wajen ƙarfe 12:30 na dare aka tashi, kowa ya nufi makwancinsa.
Washe gari kasancewar bawani babban events ba ne, Amarya ce zata yi da ƙawayenta shima Ango zai yi na shi daban da abokansa. Anam gida kuma Mama ta haɗa saukar alƙur'ani mai girma, haka ma ɓangaren Mom ta ɗakko manyan malamai suna sauka wasu anam gidansu, wasu kuma can gidan da amarya da ango zasu zauna.
Duk masifar su Goggo larai ds su Ilyasu sai da suka kwana gidan, abun kunya har da su mazan, sai shago aka nema musu a waje wai sun zauna a ci arzikin dan-uwansu da su, Goggo Larai tun safe take faman zuga Furee da habi, amma sunƙi sauraronta sai ma ce mata da sukeyi. "Yanzu babu ƙyashi babu hassada a tare da mu, kalli yadda mukayi ƙiba muka murmure, dan haka mu zama nan yanzu muka fara har karatun boko zamu koma, mu samu gina gobe mai kyau."
"Eyh lallai ne asararru, to ku sani wyaanan iyayen baƙar zuciyar ba zasu taɓa son ku ba." Goggo larai ta faɗa musu. "Ni kinga tafiyata." Furee ta faɗa, habi ma ta ce. "Kuna cin arzikinsu kuna musu hassada."
Haka Goggo larai taita sababi tai ta masifa, kowa kuma ya yi mata banza, har ƙanwar Mama autarsu ta ce zata ci mata mutuncin amam sauran suka hanata, wacce ita Bhatool ta gado sak a wajen rashin mutunci, basa shakkar kowa ba sa shayin kowa.
Yau a S Twinkles zasuyi Ladies night ɗin nasu, kawayen sun yi ankon baƙi ita kuma ta yi na fari sun bada style mai kyau da daukan hankali, sun yi abu a gayyacin, cike da ilimi da wayewa. Ƙarfe tara dai-dai suka ta shi abunsu.
Washe gari kuma Kamun Ummah, shima Hall ɗin da suka kama yana cikin manyan hall a garin Yobe, sun yi ƙoƙari sosai wajen abinci da tsarin wajen, sanan ƙawayen Mom da ita sun samu hallarta, an mutunta sosai sama da yanda suka yi suma, duk da suma sun yi matukar kokari, abokan amgo sun xo amma sai daga baya, Abdul da abokansa ne suka cika wajen kuma suma sun zuba liƙi, sai ga ƙawayen Bhatool da wata sabuwar al'ada wai suma sun siya wankam ango naira miliyan ɗaya, wajem da ya yi trending sosai a social media, bidiyon ya zaga ko ina tare da burge mutane, wamsa karshe ma abokan angon sai da suka bada sama da kuɗin da suka amsa.
Washe garin kuma suka yi Cockail, anan ne aka zuba biki, ango da abokansa amarya da ƙawayenta babu mafaɗi, Ashe senate taƙadirin kansa ne, sai yanzu ya sami dama har mamaki yake bawa Bhatool na irin rawar da yake yi a wajen shi da abokansa, itama Bhatool da ƙawayenta suka sha rawa abunsu.
Washe gari yakama ranar ƙarshe, Mom za ta yi nata event ɗin amma na rana uku za a ta shi a huce da amarya gidansu, su yi nasu yini kafin daukan amarya, yau ƙawayen amarya basu da anko, kowacce dress ɗin ta za ta yi, kuma iya ƙawayen amrayar ne zasu su ƙawaye da yan uwan mama suna gida suna yininsu, wasu ƙawayen ma na Bhatool gida zasu.
Tun takwas suka fita gidan kwalliya, amma ba su suka isa wajen ba sai ƙarfe ɗaya na rana. Yau komai na wajen kamar na sarauta, ga basu da algaita kayan da suka saka, ango har da rawani amaryar da alyabba, kirarin Mc ya da ce da komai na wajen.
"Wanan busar idan ba Saraki ba, ko an busa ta ba za ta hau ba.
Algaita iya algaita, busar ɗan gidan Saraki ango senate, da busar ƙasaitaciyar basarakiya zinariya abar adon yan mata.
Zinariya abun alfaharin kowa ya riƙe.
Lu'u-lu'u abun alfahari ba gidan kowa ba.
Takowar da ake a gurinan, da ango ne Senate da Amarya Bhatool, da Anti Fauza matar ministan kuɗi, da Anti Shuwa ƙawar da ta zama yar uwa, da Momin Amarya momin Ango, Yau Bhatool ta zama zinariyar mata.
Lu'u-lu'u abun adon da ba kowa yake taɓa gani ba
Lu'u-lu'u abun adon da kowa sai dai ya gani a addu'a.
Haka kike ko acikin al'umma.
Kainuwa ce dashen Allah.
Itace kalmar da ake kira kyawu.
Idan aka kalli wasu za ace masu kyawu ne.
Itako idan akace kyau, dukkan wata fassara da ake nema a duniya itace fassarar kyau.
Bata taɓa zama mai kama da model ba.
Domin ita da kanta model ce.
Kuma role model ce.
Idan katara mace ɗari.
Guda hamsin sai tace maka Bhatool nake kwaikwayo.
Dukkan ɗabi'unta cassain da takwas a cikin ɗari.
Dabi'une da kowane mahaluki yake cewa yana son irinsu.
A cikin mu'amala, ba kowa kake samu mai halinta ba.
Idan ka kallesu a tare ka kwana kana kallo, Bhatool ne da senate.
Bazaka gaji da kallonsu ba.
A cikin alfarma ta uwa.
Acikim albarka uwa.
A soyayya ta 'yan uwa.
A karamci irin na uba mahaifi.
A haka suka rayu.
A haka aka haife su.
Saboda haka dukkan rayuwarsu aminci ne cikin aminci.
Aminci da muke kara nema a yarda da amincin Allah.
Daren su Bhatool, masu algaita, sarkin busa, da sauran yan-uwa muce Allah ya kyautata makwancin mahaifin Bhatool.
Kukam da Bhatool ke riƙewa ne ya fito, da sauri Senate ya rungumeta, tun lokacin da aka fara ambatar kalamar mahaifi Bhatool ta fara zubar da hawaye, ita shikenan nata ya mutu, da yana raye haka za a dinga faɗin sunanshi tana jin daɗi, amɓa yanzu babu shi, ba ta taɓa kuka daga cikin zuciyarta ba tun rashin Abbanta ba sai yau, daga cikin zuciyarta take yin shi, tana matuƙar kaunar abbanta, amma tun tana ƙarama ya mutu.
A hankali senate ke shafa mata bayanta, har tasamu sauki daga kukan da take. Gaba ɗaya Bhatool ba ta ji daɗim event ɗin ba, mussaman da ta ƙara tunawa yau fa zata bar gidansu, zata bar Umma za ta tafi wani wajen tayi ta rayuwa a can, zama bana kwana daya ba bana biyu ba, ba irin zaman da take yi gidan Yaya Karima ba, ji tai kamar ta kwanta a ƙasa ta fashe da kuka taita burgemi a ƙasa.
A haka aka lallaɓa aka ƙarasa Senate ya dawo da ita, a lokacin gidansu ya cika maƙil, Yaya Karima ce ta tsaya a kanta ta shirya sabida Senate ya sanar da ita kukan da ta yi wajen, daga nan ta kawo mata abinci ta dole ta cusa shi, daga nan ta fito aka dinga gaisawa da yan uwa da iyaye.
Daga nan aka sake sa Bhatool a ɗaki ta hau wani shirin, bayan ta shirya aka naɗe ta cikin lafaya aka barta zaune a ɗakin ita ka dai babu kowa, su Amrah suna can tare da sauran ƙawayensu. Kuka ta fara a hankali a hankali hae ya fara nisa, sai da ta yi kusan awa guda aka shigo da Mama da Anty Abu Babar yayarsu Mama sai kuma Yaya Karima.
Anty Abu ce ta fara magana. "Bhatool! Aure wata rayuwa ce sabuwa, rayuwa mai cike da abu kala-kala, rayuwar da dole hakuri ne mahaɗin tafiyar, ba wai faɗa ko nuna zallan soyayya ba, Bhatool rayuwa ce da ake fatan dauma tare har mutuwa, kamar yadda kila ga mahiafiyarki na zaune gidan mijinta duk da baya raye, kamar yadda kika ga yayarki na xaune gidan mijinta ba tare da samun wani saɓani ba, to Bhatool duk wanda ya ce mili gidan aure gidan ba gidan hakuri ba ne ya yi miki ƙarya, duk irin daɗi da kika mace na sha a gidan mijinta akwai matsalal da take fuskanta, a rayuwa a naso a ko da yaushe ka dinga ganin alkhairin mutum fiye da sharrinsa.Bhatool ki yi hakuri, ki yi biyayya ga mijinki zaki yi nasara a rayuwa, ki ba shi sau da ƙafa."
Gaba daya jikin Bhatool ya yi sanyi, hawaye na sauka a fuskarta ɗis-ɗis. Yaya karima ta fara magana. "Bhatool duk wacca kika ga ta ji daɗi gidan mijinta ita ta siya da kuɗinta, haka duk wacca ta sha wahala ma ita ta siya da kuɗinta."
Legendspen ***