MATAR GIDA PAGE 7
MATAR GIDA 007
SHUUKRAN/022
P7
A hankali Ɗalha ya nime waje ya zauna tare da dafe kansa murya can ƙasa yana furta kalmar innalillahi wa inna ilaihi ra'jun,su kuwa su Afef da Rayyan har sannan cewa suke mantau ya mant tare da tafa hannu su,ba'a dauki lokaci ba Sudais ya shigo parlour hannusa riƙe da uniform ɗinsu Allah ya taimaka ruwan jikin uniform ɗin ya tsane sai dan sanyi sanyi ne kawai jikin uniform ɗin,da ido Ɗalha ya bishi har ya zuba kayan bisa ɗaya daga cikin kujerun parlourn Ɗalha ya mayar da dubansa ga uniform ɗin yaga duk sun yamutse alamar rashin goga,Sudais ya dauki uniform ɗinsa zai sa ya ji da sanyi hakan yasa ya mayar da dubansa ga Ɗalha da ke zaune kan kujera kamar an dasa shi wajen,sai kallon yaran yake,Sudais ya ce ''Dady uniform ɗin basu gama bushewa ba ya kamata a goge mana kafin mu sa'' Ɗalha da ya yi nisa cikin tunani bai cewa Sudais komai ba hasali ma bai ji abinda Sudais ya faɗa ba tunani yake tare da mamakin yadda Amirah ke yin ayyukan gidan gaba ɗaya kafin karfe takwas ta gama komai,har wanke wanke da shara da moping,ita ke haɗa masa ruwan wanka,ya tuna yadda kullum yake fita daga ɗakinsa cikin shirin zuwa office ya zauna kan daining Amirah ta yi sarving ɗinsa breakfast ta yi ta ihu da yara har haushi yake ji yadda take yiwa yara magana ta yi ta ɗaga murya kamar ba mace ba,sai gashi yau shi ke ɗaga murya ƙila ma ya fita ɗaga murya,haka zai ce abincin sa hankali kwance da ya gama ci ya yi ficewarsa,ya tuna yadda yake tarar da ita da yaran cikin shiri ita cikin shirin zuwa wajen aikinta yara kuma cikin uniform,kusan kullum karfe bakwai da mintina talatin zuwa arba'in Amirh da yara ki fita daga gida,ita ke kaisu makaranta cikin adaidaita,haka zai wuce su ita da yara tsaye bakin kwalta cikin motarsa,baya kai yaran makaranta sai in Amirah bata da lafiya,mayar da dubansa ya yi kan Sudais ya ce ''ka sa haka babu lokaci'' mayar da duban sa ya yi ga Afef da Rayyan da ke jan wandon ɗaya Afef ya ce wandonsa ne,Rayyan ma ya dage sam nasa ne,zuwa wannan lokaci Ɗalha ya gaji da lamarin yaran gaba ɗaya hakan yasa ya ce su basa wandon ya duba ya gani,bayan ya duba ne ya miƙawa Afef ya ce Rayyan ya duba nasa wandon,agogo dake manne jikin bangon parlourn Ɗalha ya kalla yaga karfe 8:05 na safe wani iska ya fesar daga bakinsa ya tashi ya wuce ɗakinsa,bayan shigarsa ɗaki bathroom ya wuce ya yi brush ganin babu lokaci yasa bai yi wanka ba ya wanke fuskarsa kawai da ƙafafu kafin ya fita daga bathroom,ba tare da ɓata lokaci ba ya yi shirin zuwa offince,bayan fitar sa parlour ya tarar har sannan basu gama sa uniform ba hakan yasa ya tsaya ya taimaka masu,karfe 8:30 suka fita daga gida,wayar Ɗalha ya yi ta ringing amma bai ɗaga ba,karfe bakwai ya kamata ya bar gida saboda meeting da suke da shi yau a office meeting ɗin na da muhimmanci sosai a wajensa da ma kamfanin da yake aiki amma babu yadda ya iya,ganin kiran nasu ba me ƙarewa bane yasa Ɗalha sa waya a silent,wani dogon numfashi ya ja kafin a hankali ya fesar,motar ya yi shiru baka jin motsin komai sai ƙarar murfin lunch box,kamshin indomie ne ya gauraye motar kaman Ɗalha bazai yi magana ba sai kuma ya ce ''a cikin ku waye ya buɗe lunch box dinsa?" duk suka yi shiru Ɗalha ya sake tambayar su a karo na biyu ya ce ''ba magana nake maku ba?" Sudais ne ya basa amsa ya ce ''Ummu Abiha ce ke cin abinci'' cike da mamaki Ɗalha ya ce ''wane abincin?" Sudais ya ce ''na lunch box ɗinta'' Sudais ya yi shiru na wasu ƴan mintina kafin ya ce ''kullum lunch box biyu take zuwa da shi school tana cin abincin ɗaya a adaidaita ɗaya kuma ta ci school,lunch box biyu Mumy ke sa mata abinci,duk ranar da Mumy bata sa mata abinci a lunch box biyu ba sai ta yi ta kuka har jikinta ya yi xafi'' shiru Ɗalha ya yi bai ce komai ba ya faɗa dogon tunani ya ma rasa ta inda zai fara yanzu ya zai yi da Ummu Abiha abincin da zata ci da rana ta cinye shi yanzu,da ya so ya fita harkarta sai kuma ya tuna karfe biyar suke tashi in ya barta babu abinci zuwa karfe biyar tabbas zata wahala,tunawa ya yi da Husnah ƙanwar sa dake aure a garin duk faɗin garin ita kaɗai ce dangin sa,daman yana da niyyar kai Fauziyya gidan Husnah saboda yanayin jikinta,sanin kansa ne baza a ƙarɓe ta a makaranta ba saboda bata jin daɗi,ya so ya fara kai su Sudais makaranta kafin ya kai Fauziyya gidan Husnah amma ya canza tunani zai fara kai Fauziyya gidan daga nan sai ya sa Husnah ta zubawa Ummu Abiha abinci
Karfe takwas da mintina hamsin daidai Ɗalha ya yi parking a kofar gidan Husnah,ɗaya daga cikin ƴan aikin Husnah ne ta buɗe masu kofar entrance,sallama dauke bakin Ɗalha ya shiga parlourn tare da yaran Ɗalha ya shiga ƙarewa gidan Husnah kallo ganin ko ina tsaf tsaf,ƴan aikinta ne ke ta faman kaiwa da komuwa,bayan sun gama gaisawa ne Ɗalha ya faɗawa Husnah abinda ke tafe da shi ta yi mamaki sosai ganin yaran a wannan lokaci basu tafi makaranta ba Ɗalha ya ce mata Amirah ta yi tafiya ne shi yasa,taɓe baki Husnah ta yi kafin ta ce ''shi yasa kullum nake faɗa maka ka samawa Maman Sudais ƴar aiki amma ka ƙi,to kaga ranar ƴan aikin yau,da tana da ƴan aiki da yaran nan basu yi lattin zuwa makaranta yau ba,sannan da a gida zaka bar Fauziyya amma kaga sai fama yawo ka ke da yara''shiru ta yi na wasu ƴan mintina kafin ta daura da ''duk ranar da ƴan aiki na basu zo ba ji nake kamar zan yi hauka ni da nake da yara uku,ina kuma ga Maman Sudais da ke da bakwai,ni fa yaya ko home work bani ke masu ba lesson teacher ɗunsu ke zuwa ya yi masu'' tashi Ɗalha ya yi yana faɗin ''mun riga da mun makara Husnah wannan lecture ba ta yau bace'' ya faɗa tare da daukan lunch box ɗin Ummu Abiha wanda ƴar aikin Husnah ta sa mata jollof pasta,Fauziyya dake zaune kan cinyar Husnah ta sake kuka ganin Dadyn ta zai tafi ya barta nan ta shiga kurma ihu tana kiran Dady ko kallo bata ishi Ɗalha ba ya sa kai ya yi ficewar sa daga parlourn,Husnah da nanny mai kula da yaranta suka shiga aikin rarrashin Fauziyya
Karfe tara da mintina shidda Ɗalha ya yi parking a kofar makaranta su Sudais fita ya yi daga motar ya sami security man dake tsaye bakin gate ɗin makarantar ya miƙa masa hannu suka yi masabaha Ɗalha ya ce ''barka da safiya ya aiki?" security man ɗin ya ce ''yauwwa barkan mu dai ya aiki ya iyalai?" Ɗalha ya ce ''Alhamdulillah'' daga nan ya daura da ''dan Allah a yi mana afuwa yau mun makara mahaifiyarsu ce bata gari ta yi tafiya,ka san sha'anin yara sai a hankali'' security man ɗin ya ce ''babu komai amma zai fi kyau ka yi magana da head misstres ɗinsu'' Ɗalha ya ce ''oky to babu damuwa bara na shiga'' Ɗalha ya faɗa tare da shiga cikin makarantar yaran na biye da shi,kamar yadda ya yiwa security man ɗin bayani haka ya yiwa head misstres ɗin su Sudais ta ce babu komai yaran su yi maza su je aji,Ɗalha na shirin offince ɗin head misstres ta jifo masa tambaya ta ce ''ina fatan duk sun yi homework ɗinsu?"sai a sannan Ɗalha ya tuna da homework ɗin da ya ce su zuba masa kan ɗaya daga cikin kujerun parlourn gaba ɗaya ya manta,numfasawa ya yi kafin ya cewa head misstres basu yi ba amma in Allah ya yarda gobe za su kawo,ta ce babu komai ta yi masa uzuri har cikin zuciyarta ta tausaya wa Ɗalha ganin duk ya birkice kana ganinsa kasan baya cikin nitsuwa
SHUUKRAN