RAUNIN DA BA A GANI

Chapter 9:RDBG

by @meefatinkwriters99

RAUNIN DA BA A GANI 

Meefat ink ✍️ writers 

“kada ka wani cemin ayya, tun yaushe nake cewa kadawo gida, amma kullum sai ace aiki aiki daga kai har jabir din” sai Jay yayi dariya yace “, ayya kiyi hakuri, da kyar na shawo kansa yazo” sai ta hararesa tace “ kaima kamin shuru ai duk ku biyun dayane, dan kun girma a turkiyya baya nanufin kumance kasar kubane”nisha ce ta zauna kusa da ayyan tace “ayya ai yanzu sunzo kibar yimusu fada mana”batabi takan nishan ba tacigaba “inaso kusani Koda duniyar gabadayanta kuka zaga, kasar ku dai kasar kuce nidai bana son naga jikokina suzama bako a kasar su” 
Sai azan ya matsa kusa da ita yakamu hannunta yace “inshaa Allah ayya this time around zan zauna fiye da yadda nakeyi abaya” sai tace “zaka gani zan rikekane bakai bakomawa kenan,”waro ido waje azan yayi yace “ayyyyaaaaa….”ai sai falon ya kaure da dariya asailin Jay ya tsaya kallon riyya yana murmushi sai itama ta saci kallonsan tana murmushi, azan kuwa hankalinsa gabadaya yana kan kakarsa, wadda dukda yawan mita da takeyi, kaunarta garesu tafi karfin komai. 

A daya banagaren garin kuwa Ruhy ce zaune acikin shop dinta, gabanta wata lace ce mai launin ruwan madara datake dorawa allurai cikin nutsuwa, dukda kasancewarta daliban pharmacy kirar kaya itace sanaarda take alfahari da ita tun tana karama,. A hankali kofar shagin tabude “Assalamu alaikum” ruhy tadaga kai tana murmushi tace “wa alaikum assalam fina!, ashe kece” fina tashi go sai taja kujera ta zauna tana cewa “wallahi nice nace bari nazo naga ko har yanzu kina binne kanki acikin aikin dinki"sai ruhy tai dariya tace “idan banyiba to wazaiyi min” “to madam pharmacist da fashion designer” sai dukkansu sukayi dariya sai fina tace “kawata kinji labarinda yake yawo a makaranta?” “wani labari kuma?” “gameda bikin award recognition day mana"sai ruhy ta girgiza kai “a'a bansani ba ai Jiya bansamu zuwa school din bama” sai fina tacigaba maganar cikin kaudi “ana cewa wai za'a gayyaci manyan baki sosai, har naji wasu malamai na cewa sun shirya gayyatar Alhaji dawud yola” sai ruhy tadan dakata kadan sannan tacigabada dinkin “to?” sai fina ta zaro ido tace “to?, shine kadai abinda zakice” ruhy tadan murmusa tace “ to meyakamata nace” “kinsan ko waye Alhaji yola kuwa?” sai ruhy tace “na taba jin sunansa, ance babban dan kasuwa neko?” “ba babban dan kasuwa kadaiba shikeda babban companyn yola holdings adamawa fa kuma yanda naji ake cewa companyn yanada branches dayawa anan kasar dama wajenta, kuma yana daya daga cikin fitattun attajiran adamawa kai da kasarma baki daya"sai ruhy ta daga kafada alamun bai shafeniba tace “ toh Allah ya kara masa budi” ai sai fina ta kwashe da dariya tace “ kedai wallahi ruhy ba acin dadin zance da ke, ke kwata kwata bakya son jin labarai samm.”.