RAUNIN DA BA A GANI

Chapter 10 :RDBG

by @meefatinkwriters99

RAUNIN DA BA A GANI 

Meefat ink ✍️ writers 

Ruhy ta ajiye lace din dake hannunta ta dubi kawarta tace “fina meyasa zan damuda wanda ban taba ganiba? Ko yazo ko bai zoba, ai bazai canza min komai ba, abinda yadameni yanzu shine yanda zan kammala wannan dinkin kafin yamma” sai fina ta girgiza kai tana dariya tacigaba “to amma naji ana cewa in shi Alhaji dawud bai samu dawowa daga kasar da yajeba, to dansa me zai wakilcesa” ruhy tasake komawa kan aikinta tace “ ko dansa, ko shi kansa banida damuwa dasu, nidai ina fatan bikin ya gudana lafiya, mu karbi kyaututtukanmu idan Allah ya nufa” fina tana dariya dan ita ruhyn ma dariya take bata sai ta dauki wani design dinda tayi tana yaba yanda kayan ya dinku, ahaka dai sai aka kawo chapter dinki da design.u  

YOLA HOLDINGS GROUP OF COMPANIES 

Azan yacigabada kallon IV card dindake hannunsa tun ficewar su head of yola University, kafin yasaukeshi a hankali kan table din office dinsa. Sai yadan jingina da kujera ya lumshe idonsa nadan wani lokaci, kafin ya kara wani motsi a kayi knocking kofar office din, “come in” yanada dama, secretarynsa ce maryam tashigo cikin girmamawa tace “sir these are the documents you requested” bai Bude idonsaba yace “thank you, just leave them here, anything else?” sai ta ajiye manyan files din agabansa, sannan tace “sir… the directors are asking if today's meeting is still by four o'clock” a hankali yabude idonsa ya sauke akan babban watch ⌚ dindake office din sannan yace “ no.. Move it to five. I need some time” “ ok sir” sai ta juya daniyyan fita sai taji yace “the invitation… Keep it on my schedule” “yes sir”. Bayan tafita sai azan yabude daya daga cikin files dinda takawomasa wanda yake daukeda bayanana companyn, bacause tun zuwansu Nigeria mahaifinsa ya dauki ragamar YOLA HOLDINGS wato babban companynsu dake nan adamawa ya damka musu. 
Batareda anyi knocking ba kofar office din tabude, “ Mr. Busy CEO…”azan bai dagoba dan yasan wayene, sai Jay yazauna akan kujerar dake facing azan yace” so… have u changed ur mind?” baidagoba yace “about what?” Jay ya xaro ido yace “seriously? har kamanta” sai azan ya dan murmusa yace “am just kiddin” Jay ya girgiza kai yace “wallahi one day zakasa na daina zuwa office dinka”