Chapter 12
RAUNIN DA BA A GANI
Meefat ink ✍️ writers
Isowarsu katafaren gidan Alhaji dawud yola wanda yakasance daya daga cikin manyan gidajenda garin yola, akwai babban sashen Alhaji dawud wanda ake kira da daddy da kuma inda yake karbar manyan baki da gudanarda tarurrikansa. Agefen dama akwai sashen mama mai daukeda 3 parlours da kuma resting room kamar dai kowace mace tagidan, a daya gefen kuma bangaren umma ne wanda Shima kamar na mama yake dukda cewa na maman yafi girma, sai bangaren mamy kusadana daddy sai na karshe wato na ayya, sai kuma sashen azan da na mazajen gidan wanda ayanzu su sunada aure. Sashen azan wani apartment ne mai zaman kansa da daddy yagina masa tun a shekarar baya dayace bazai zo gidaba sai in yanada nashi side din kamar kowa. Yanada parlourn sama da kasa sai garden, library, gym da kuma dakunan kwana.
Parking sukayi suka fita sannan suka nufi side din mamy, shigowarsu kenan itama mamy na sauka daga stairs “a'a har kun iso” tafada tana murmushi sai suka gaisheta sai azan ya kwanta kan kujera yana cewa “oh God mamy am so tired today” mamy ta girgiza kai tana shafa kansa tace “kuje ku samu ku watsa ruwa na shirya muku fav dinku” sai Jay ya kalli azan yana murmushi yace “ I told u mamy is the best, nifa mamy kullum missing dishes dinki nake”sai tayi dariya tana nufan corridor tace “kudai je kuyi freshening up tukun”.
Bayan sun gama shirya wa suna fita daga side din azan sai Jay yake cewa “naji kayi shifting meeting in to 5, sai kuma gashi 5 dinma ya kusa kana gida” “ A S black zaiji da komai” da haka suka nufi direct parlour inda sukaga ba kowa sai suka hau parlourn sama sai suka nufi karamin parlourn ta inda sukaga mamy tareda riyya suna jera abinci akan dining, rice and stew ne sai gasassun kaza da hadin fruit salad. Jay yashafa hannayensa yace “alhamdulilla wannan shi ake kira welcome home” riyya ce tagaida su da nisha, suka amsa suna zama a kujera sai azan ya kallesa yace “kai de akullum cikin kane yake fara magana” “ kai kuma brain dinka ba"su riyya de dariya suke dan inkana neman drama to kazo wurinsu azan, mamy ma ta girgiza kai bayan tagama serving dinsu sai tace “kufara ci kar yahuce,kuma as from today henceforth zan fara sa drivers suna kaimuku abinci dan bazan yarda da cin abinci late din na da kukeba”.
Jay de anan yakwana. Washegari da safe, azan ne yake saukowa daga stairs cikin shigar casual yana gyara wrist watch din hannunsa, akasan falon kuwa Jay ne zaune yana shan coffee dinsa na alada sai yadago yana kallon azan din “ good morning sleepy head” yafada yana murmushi, zama azan yayi yana cewa “ really?nine sleepy head?” Jay yayi dariya yace “kamanta jiya wayace ‘five more minutes’?” sai azan ya girgiza kai yace “Allah yashiryeka” kafin Jay yabashi amsa sukaji takun sawu daga corridor alamun maishi yashiga taba yane.