His Rose

The Unkind Welcome

by @northernangel

Ƙarfe 7:30 na dare motar da ta ɗauko su daga airport ta dakata a ɗaidai ƙofar gidan Mu’azzam. Yana zaune a gaban mota, ya juya ya kalli Zara da ke kwance a ƙirjin Zafar kamar ruwa—gaba ɗaya ta yi laushe, sai sauke zazzafan numfashi take yi kamar za ta mutu. Yes, da zazzabi na gaske a jikinta, amma tsantsar raki da shagwaba ya fi yawa a ciki. Mu’azzam ya miƙa hannu yana ɗan taɓa goshinta, cike da tsokana ya yi saurin saurin janye hannunsa gaba ɗaya yana zare ido stylized, gami da cewa, "Whoa, girl, you are radiating heat! I think I just got a first-degree burn." Ko ɗaga ido ba ta yi ta kalle shi ba; sai ma ƙara narkewa da ta yi a jikin Zafar tana ƙara sauke nauyayan nishi. Wani  pointed, sharp look Zafar ya jefawa Mu’azzam yana cewa, "Leave her alone." Ya faɗa ne saboda jiyan nan da ya tsokane ta makamancin haka, sai da ta shafe sama da awa ɗaya tana risgar kuka saboda kawai ya ce tayi fresh. Ranar ma kawai fashewa ta yi da kuka out of nowhere wai saboda Imaan na kallonta! Gaba daya ta koyi wani kukan banza yanzu. Gashi idan kukan ya tashi, sai ta ja shi over an hour; duk wani lallashi da soothing words na duniyar nan Zafar zai tayi mata amma taƙi sauraron kowa, sai dai ta gaji dan kanta sannan ta sarara ta yi barci. Toh yau kam an ci sa’a sosai da ba ta bi ta kansa ba, shi yasa Zafar yayi saurin dakatar da shi don kar ya sa ta birkice musu a mota. Yar dariya Mu’azzam ya yi, yasan me Zafar ke tsoro dan ya shadai rigimar tata shima. A hankali ya ɗauki hannun Zara ya yi kissing bayan hannun softly yana cewa, "I'm sorry, I hope you feel better soon. I'll see you in the morning, alright?" Nan ma ba ta ɗago ba, kuma lumsassun idanunta na rufe ruf. Ganin ba ta da niyyar ba shi amsa ya sa ya juya yana buɗe ƙofar fita yana faɗin, "Sai da safe, Imaan!" Imaan ta sakar masa murmushi tana cewa, "Have a good night, Ya Mu’azzam..." Daga haka Mu’azzam ya fice tare da maida ƙofar motar ya rufe soundproofly. Lamidi ya ja motar a hankali saboda Zara bata son gudu tace, yayi navigating smoothly zuwa cikin manor, inda ya yi parking ɗaidai gaban entrance din private wing din Baffa. Suna shiga cikin gidan, Baffa yana tahowa zai shiga foyer ɗinsa kenan da alama masallaci za shi. Wani irin tsantsar farin ciki ne ya mamaye shi lokacin da ya yi tozali da Zara. Dama tun ranar da su Daddy suka neme ta suka rasa, Mu’azzam ya sanar da shi duk yadda ake ciki, har zuwa wayar da suka yi da Zafar da ya tabbatar masa tana tare da shi wanda hakan ba karamin dady yayi masa ba, sannan ya ƙara matsayi da kimar Zara sosai a idonsa. A gaggauce suka gaisa cikin fara’a, yana musu sannu da zuwa sannan ya tambayi Zara—da ke manne a jikin Zafar kamar ba za ta rabu da shi ba—ko ya jikin nata. Sharp-sharp suka gama gaisawa, sannan Baffa ya hau yi wa Zafar ɗan fada a kan cewa ya ɗauke Zara ya fice da ita ƙasar waje ba tare da izinin Daddy ba, tare da jaddada masa cewa dole ya tabbata ya je har Warri ya ba sa haƙuri. Daga nan ya sanar da su cewa su ƙarasa ciki wurin Yemma, shi zai wuce masallaci saboda ana kiran sallar isha ne lokacin. Ciki suka shige gaba ɗaya. Zafar na riƙe da Zara dake fama da gajiyar jiki da zazzabi, yayin da Imaan ke biye da su a baya tana riƙe da designer handbag ɗin Zara da kuma insulated bottle ɗinta mai ɗauke da cold coconut water. Ta wing ɗin Baffa suka fice zuwa ɓangaren Yemma, inda suka shiga second parlour ɗinta suka sameta a zaune. Sai dai kwata-kwata ba su yi tunanin cin karo da Rahama a zaune a parlourn ba. Cike da tsantsar murna, Imaan ta ƙarasa cikin parlourn a guje, ta ajiye kayan Zara a kan sofa sannan ta faɗa jikin Yemma. Itama Yemma ta miƙe cikin sauri ta rungume autar tata tsam a ƙirjinta, tana faɗin maganganu cikin yaren Taqbaylit cike da tsantsar kewarta. Zafar kuma ya ƙarasa da Zara gaba, ya zaunar da ita softly a kan babbar plush sofa ɗin parlourn cikin kulawa, sannan ya sunkuyo ya yi kissing temple ɗinta. Yana matsawa, Zara ta shimfide tana kwance a kan sofar ta ɗora kanta a kan throw pillow, tana sauke numfashi a hankali.  Zuwa lokacin Yemma ta sake Imaan, ta buɗe hannayenta biyu tana yi wa Zafar alamar ya ƙaraso shima. Cikin sauri ya ƙarasa ya rungomo ta a ƙirjinsa, yana kiran "Yemmaa" cikin wata kamar ƙaramin yaro. Yemma ta kasa rufe bakinta saboda farin ciki, sai zuba magana take yi cikin yarensu tana ta sa masa albarka da fadin tayi kewarsa. After a few minutes, komai ya daidaita. Zafar na zaune kusa da Yemma a kan sofa yayin da Imaan ta haura sama zuwa ɗakinta domin ta huta. A gefe guda kuwa, Rahama na zaune ta daura ƙafa ɗaya a kan ɗaya tana danna wayarta cike da shan ƙamshi da basarwa. Ta yi wani irin fari da cika na alfarma, gashi ta ci wani zafaffen gayu—sanye take da wata tight fitted red lace gown wadda ta fito da every single curve ɗinta sarai, tayi ɗaurin ture, fuskarta kuma ke ɗauke da light makeup da ya yi mata masifar kyau. Cike da salon iyayi, yanga, da wata siririyar murya mai cike da jan hankali, ta ɗago tana kallon Zafar tana cewa, "Hey babe, welcome home!" Sai a lokacin Zara da ke kwance a kan sofa ta ɗaga idanunta masu cike da gajiya ta kalli Rahama. Kure ta ta yi da kallo na few seconds, tana nazarin fari da ƙibar da taga tayi, sannan ta kawar da kanta ta kalli Zafar da ke amsa gaisuwar Rahaman a takaice tare da cewa, "Yeah, thanks." Yemma, wadda idanunta ke kan Zara tun ɗazun cike da tsananin mamaki da jin zafin halin ko-in-kula da ta nuna, ta juyo ta kalli Zafar da fuska a murtuke tana cewa, "Is your wife too big to greet anyone in this house?" Da sauri Zafar ya tare maganar Yemma don kare matarsa, yana faɗin, "Ba ta jin daɗi ne Yemma. She's running a fever, so she's completely exhausted." Daga haka ya yayiwa Zara magana softly cike da lallashi, "Princess, come on, kin manta ba ki gaida Yemma ba." Ɗan ɗaga kanta ta yi kaɗan daga kwancen da take a kan throw pillow, ta kalli inda Zafar ke zaune kusa da Yemma. Ciki-ciki ta gaida ita a takaice—wanda muryarta ba ta ma fito ba sosai dan Yemmar ba ta ji me ta ce ba, kawai dai ta ga bakinta ya motsa. Zafar, da bai fahimci yanayin da Yemman ke kallonta ba, ya kalle ta yana faɗin, "She actually just greeted you, Yemma. Ki amsa." Ko kallonsa Yemma ba ta yi ba, sai ma juyawa da ta yi ta kalli Rahama da ke zaune a gefe tana danna wayarta, ta tambaye ta, "Did you finish setting up the dinner table?" Rahama ta ɗaga mata kai cike da biyayya da shakka, "Yes Yemma, everything is all set up." Miƙewa Zafar ya yi tsaye ya kalli agogon hannunsa saboda jiyo sautin liman da ya yi an tada sallar Isha a masallaci. Fara takawa ya yi zuwa hanyar fita yana cewa, "Yemma, bari inje masallaci." Sai dai yana gaf da fita ya dakata. Ya 
juyo ya nufi tsakiyar parlourn straight zuwa inda Zara ke kwance. Ɗukawa ya yi a gabanta a hankali yana zuba mata idanu. Ita kuwa Zara idanunta na rufe ruf ta ƙi buɗewa, fuskarta a haɗe gami da turo baki, looking so cute and vulnerable. Zafar ya ɗaga kai ya kalli Yemma yana tambayarta abincin da aka dafa a gidan. Banza ta yi masa, ta maida hankalinta kan wayarta tana danna screen dinta. Juyawa ya yi ya kalli Rahama yana tambayarta, ita kuma kamar jira take ta fara jero masa nau'ikan abincin da aka shirya a dining table ɗin. Bayan ta gama lissafawa, Zafar ya sake maida kallonsa kan Zara da har lokacin ta ƙi buɗe idonta. Sam ba abunda take ci a ciki, duk algerian dishes ne daman kuma yayi tunanin hakan.  Sauke murya ya yi ƙasa-ƙasa, ya fara mata magana extremely softly and gently, "What do you feel like eating, maama?" Sai a lokacin ta buɗe idanunta a hankali ta kalle shi. Shagwabe fuskarta ta yi tamkar wata baby, muryarta na rawa tamkar za ta fashe da kuka, tace, "I just want to go home... I already told Lucy to have the chef prepare swallow for me." Gyada mata kai ya yi cike da tsantsar murna da lallabi, ya ce, "Alright. Let me run and pray, and as soon as I'm back, we'll head home." Daga haka ya miƙe tsaye, ya juyo ya kalli Rahama a nutse cikin cool voice yace, "Rahama, check the fridge and bring her a cold drink." Nan da nan fuskar Rahama ta sauya, ta kalli Zafar tana turo baki cikin wata 'yar shagwabar erin wadda ta ga Zara na yi masa—ita ma a dole shagwababbiya. Ko lura da abun da take yi bai yi ba; ya kawar da kansa ya juya ya nufi ƙofa domin tafiya masallaci. Aikuwa Rahama ba ta ma motsa ba balle ta tashi ta ɗauko wa Zara cold drink ɗin, sai ma haɗe rai da ta yi tana cika tana batsewa a kan kujera. Yemma ta ɗago daga danna wayarta tana kallon inda Zara ke kwance idon tana rufe. Calmly Yemma ta ajiye wayar gefe, sannan ta cire glasses ɗin idonta ta sake maida tsauraran idanunta kan Zara. Zara da ke kwance bata san me ke faruwa ba sai muryar Yemma kawai ta tsinta, "Ke, Zara.” Tunanin da take yi ya yanke, ta buɗe idonta ta ɗan ɗaga kai tana kallon inda Yemman take zaune. Fuskar Yemma was very serious, babu alamar wasa ko sassauci.  Ba Zara ba, hatta Rahama da ba ita aka ambata ba sai da ta sha jinin jikinta, ta sunkuyar da kanta ƙasa tana jiran ta ji me Yemma za ta ce, tana kuma fatan Allah ya sa kar a haɗa da ita koma menene. Zara kam idonta na kan Yemma tana jiran ta ji me za ta ce, sai dai tuni atmosphere ɗin ɗakin ya canza. Daga yanayin Yemman ta san ba alkhairi ba ne duk abin da zai fito daga bakinta. Cikin wata calm, icy voice Yemma ta ce, "What exactly was your reason for running back to your family and lying that your husband divorced you?" Idan sofa ɗin da Yemma ke kai ta motsa to Zara ta motsa. Sai can ta juya ta gyara kwanciyarta tana sake lumshe ido, amma sai dai ko minti ɗaya ba ta yi ba ta ɗago da ƙarfi saboda wata irin tsawa da Yemma ta daka mata, "Am I talking to a brick wall there, or did you just completely lose whatever little sanity you had left?!" A gigice Zara ta miƙe zaune tana kallon Yemma da tsantsar mamaki. Nan fa Yemma ta hau bakinta cikin bacin rai, "The nerve of you to give me the silent treatment! Ina miki magana kina kwance... Who do you think you are? Don't you dare bring your rashin tarbiyya into my house! Zan gyara miki zama ne nikam." Zara dai kallonta kawai take yi cikin muzurai, tuni ta nemi zazzabin da ciwon jikin nata ta rasa saboda mamaki. Cikin tsantsan ɓacin rai Yemma ta ci gaba da magana with a low, venomous voice, "Listen to me very carefully, you arrogant girl. Even your late mother, Maryam, would never have dared to ignore me when I spoke to her. She was nothing but a worthless, penniless nobody whom Ahmad Galado only married out of sheer pity and charity! If you think you are someone special, go and dig up the pathetic history of how your mother crawled into Galado. Ki je ki tambayi ƴan uwan uwar taki! She had no status, no name, and came with absolutely nothing. Her father lived and died a wretched beggar, scraping by as a low-class school lecturer. That miserable, low-born blood lines your veins. No matter how much money you have now, that trashy background is permanently stained in your DNA—especially you, with your ungodly, infidel bloodline that knows absolutely nothing of faith." Tunda ta fara maganar Zara ke kallonta cike da tsantsar mamaki, ta ƙasa motsawa saboda tsantsar shock. Rahama kam jinta take kamar a mafarki; like, is what she is witnessing real? In haka ne ashe har gwara ita, wulaƙancin da take sha mai sauƙi ne! Ashe haka ake ci wa iyayen Zara mutunci amma ta nace a gidan nan? Tab! Yemma dai ba ta fasa ba, sai zazzaga bala'inta take tana yi wa Zara zagin kare dangi don zuciyarta tayi sanyi, amma sai ma ƙara tafasa take duk lokacin da ta tuno da irin matsalolin da ta samu da mijinta a kan ƴaƴan Maryam. "Tashi ki fitar min a gida! Kuma ki sani aikin banza kike yi—whether you accept it or not, my son has already taken another wife. Your mother endured a co-wife and your father had two wives, yet you have the audacity to come here and lay down rules? What disrespect! Zafar has already taken a second wife, and you can either swallow that bitter pill or drop dead! If it’s too much for you to handle, then the moment you give birth, ki ajiye abin da kika haifa a ba ki takardanki. Yes! Leave the baby behind and crawl back to your village! No one is begging you to stay with my son. This is exactly what happens when a mother has zero tarbiyya to pass down to her daughter. Maryam didn't even have a mother around to raise her right, so it's no surprise you turned out completely mannerless." Cikin gajiya da maganganun da kuma zagin iyayen ta da ake, Zara ta kasa danne ɓacin ranta. Ta miƙe tsaye idanunta sun yi jawur tana cewa, "That’s enough, Yemma! Seriously, me maamanta ta yi miki ne?! What on earth did she ever do to you?! Attack me all you want, but stop disrespecting my late mother!" Ƙafin Yemma ta amsa, Rahama ta miƙe tsaye cikin masifa, "Ke, are you crazy?! How dare you speak to Yemma like that? This just proves everything she just said about you. You have zero respect for your in-laws!" Frowning, Zara ta yi tana kallon Rahama cike da takaici. Kafin ta yi magana Yemma ta ce, "Oh, did I hit a nerve? Ai ban san ki ji haushin na zagi mamanki ba sai kin rama mata! Go ahead and defend her honor if you think you can! You won't completely convince me that you are a total ƴar iska, mara tarbiyya until you match and return every single insult I just threw at you. Get out of my house this instant before I call my maids to teach you a lesson you will never forget!" Ta ƙarasa maganar daidai lokacin da Zafar yake shigowa parlourn cikin sauri, bayan ya jiyo hayaniyar da ke tashi tun daga bakin kofar shigowa parlourn. Da tsantsar mamaki ya iso wurin, yana kallon Zara da ke tsaye fuskarta ta yi jawur da kuma Yemma da ke faman huci a zaune. Normally, Yemma ba mai ɗaga murya ba ce ko da tana faɗa—she is always known for her calm, icy demeanor—unless idan a kan mutum ɗaya ne, wato matarsa. Cike da fargaba Zafar ya tambaya cikin soft, cautious voice, "What is all this shouting about?" "Why don't you ask this disrespectful, mannerless brat you chose to marry!" Yemma ta faɗa cike da masifa, tana watsa wa Zara wani irin kallon tsana da ƙasƙanci. Shiru Zafar ya yi a tsaye, yana juyar da kansa tsakanin Yemma da kuma Zara da ke ƙoƙarin maida kukan da ke son ƙwace mata ko ta yaya. Kasa  yin magana ya yi saboda tsantsar tsoron abin da zai ji, sam baya so ace Zara tayi wani laifin da zai kasa jurewa yayi maya fada. Ya barta a kwance tana rufe ido wadda ko magana da ƙyar take yi, amma ya dawo ya tarar da ita a tsaye, full of anger, energy, and raw emotion. Something seriously wrong must have clearly happened! Kafin ya buɗe baki ya sake tambaya, sai kawai ya tsinci muryar Rahama daga gefe. "All Yemma did was confront her about the lie she told her parents about being divorced. Next thing you know, she's throwing a major attitude and throwing insults, even saying—" Cikin wata calm, low, yet lethal voice, Zafar ya katse ta. "Shut. The. Fuck. Up! Did I ask for your opinion? Who the fuck do you think you are, jumping into a conversation between my mother and my wife? Get the fuck out of here before I lose my mind!" "She's not moving an inch!" Yemma ta daka masa tsawa itama. "If there is anyone who needs to get the hell out of my house, it is this insolent, useless creature you brought here as a wife!" Ta ƙarasa maganar tana nuna Zara tare da aika mata wani ƙasƙantaccen kallo. Da mamakin yadda abun ya yi zafi haka a cikin 'yan mintuna, Zafar ya dan ja tsaki kaɗan yana faɗin, "Yemma, please, stop this! I literally told you before I stepped out that Zara is really sick right now. Is all of this just because she didn't greet you? Come on, ai ta gaishe ki before I left fa!" Cikin wata irin zafaffiyar masifa Yemma ta miƙe tsaye gaba ɗaya, "Do you honestly think I care about a greeting? To hell with her and her worthless respect! Da ta gaishe ni da kar ta gaishe ni, duk uwarsu ɗaya ubansu ɗaya—it makes no difference to me! This is about her manipulative nature, and you enabling it because ba ka san ciwon kanka ba! I brought a wife into your life, and she has the nerve to demand a divorce for Rahama before stepping into your bed? And you just rolled over and took it because ba ka san darajata ba? You know what? This marriage is a total dead end. Wallahi! We are fast approaching the day where you will have to choose between her and the woman who birthed you. If you are truly my son, I dare you to divorce Rahma, and watch if Zara spends one more night as your wife. She will suck it up and live with a kishiya! Her own father had two wives, so who does she think she is? She is not made of gold!" Wani murmushin jin daɗi ne da Rahama ta ƙasa ɓoyewa yake playing a kan lips ɗinta. Tunda ta yi auren nan, ba ta taɓa tsintar kanta cikin tsantsar farin ciki da nasara irin na yau ba. Zara kam zuwa lokacin, tuni hawayen da take ta rikewa ya kubce mata, yana wanke mata fuska. Gaba ɗaya ilahirin jikinta kyarma yake yi saboda tsantsar humiliation da bacin rai. Zafar kuwa, cike da mamakin inda Yemma ta ji ainihin issue ɗinsa da Zara yake—but then, he quickly realized Daddy ya bawa Baffa information ɗin, so dole Baffa zai gaya mata yanda akayi da ya dawo. Cikin fada da ɗaga murya Yemma ta ci gaba da cewa, "Starting today, I expect absolute fairness between your wives if you truly value the womb that carried you. I don't ever want to hear another complaint about how you handle your household. You will split your nights properly, exactly how any responsible man with two wives does! For the next two days, you are staying exclusively at Rahma’s house, and wallahi, I don't want to hear a single excuse. Now, drag this shameless brat out of my house before I have my people throw her out into the street of this estate!" Daga haka ta fara tafiya cike da izza ta nufi hanyar staircase, ta bar su a nan tsaye cirko-cirko, yayin da Rahama ta saki wata 'yar karamar shewa tana faɗin, "Kare dai ya lashe zuciyar jikar malamin makaranta." Daga haka ta juya ta fice daga parlourn cike da tsantsar yauki da takama, sautin dariyarta na sake ƙarade ko'ina a cikin parlourn gaba ɗaya... Zafar na tsaye gaba ɗaya jikinsa ya yi sanyi. A yau kam Yemma ae shi tayi humiliating ba Zara ba. A hankali ya waiga ya kalli Zara—fuskar nan tata ta rigaya ta jiƙe sharkaf da hawaye, tana ta sauke ajiyar zuciya mai sauri, jikinta gaba ɗaya na kyarma out of pure humiliation and rage. A hankali ya isa kusa da ita ya kama hannunta yana mai kasa kallon fuskarta yaja hannunta suka fara tafiya…