Chapter 13:RDBG
RAUNIN DA BA A GANI
Meefat ink ✍️ writers
Mama tana zaune a falonta, adamu da hamis ne agabanta cikin wani yanayi, mama ta kurbi shayinta tana kallonsu sai tace “ kunsan meyasa ban taba cemuku kuyi fada da azan ba?” adamu ya girgiza kai sai tacigaba “saboda bahaka ake cin nasaraba” hamis yace “to mezamuyi mama” sai mama tadanyi murmushi tace “shi kasuwanci wani lokacin ba iya dan kudi akeyinsaba, dole saida yarda” sai adamu yace “yarda kuma” “kwarai kuwa, mahaifinku ya yarda da azan, ma'aikata sun yarda dashi, abokan aikinsa suna girmamashi” sai ta dan dakata “idan kuna son canza wannan to bata fada za'a canza ba, kukara gina sunanku” “how?” adamu ya tambaya “kununawa mahaifinku cewa yanzu kuma kun canja, kuma kununamasa zaku iya” sai hamis yace “amma bana tunanin daddy zai kara yarda damu for the second time"sai mama tace “sai kununamasa cewa yanzu ba da bane” adamu ya gyada kai yace “na fahimta” sai ta kalli hamis tana jiran shima yace wani abu, amma sai yayi shuru, azuciyarsa bai yarda da maganar kada suyi fada da azan ba yanaganin cewa akwai hanya mai sauki, mama ta lura da yanayinsa, ta san danta sosai, a ranta tace ‘hamis kada kaje ka lalata komai’.
SHAGARI LOWCOST
Ruhy ce tana danna wayarta, sai wayar tayi ringing, dauka tayi sai tace “eh inanan” shuru tayi tana sauraron nacikin wayan, can kuma sai tace “eh nagama hadawafa tuntuni, kunake jirama kuzu kudauka dan inaso naje nadauki huda a school,” sai ta danyi shuru can tace” okk sai kunzo”. Katse wayar tayi tareda cewa “ bari nayi posting wannan new design na abayannan Allah yasa ya samu karbuwa, amma nikam yamin kyau dole ma indauki biyu nawada na auta saina mayar da kudin” tana fadin hakanne tareda zaban colours datakeso tareda shiga wani daki, tasauya kayan sai tashiga page dinta na tiktok tayi hotuna tareda video tayi posting, amma duka fuskarta arufe, tana gamawa taje offline tareda shirin maida kayanta na farko, bata kaiga cire kayanba taji sallamarsu, faridace tafara shigowa sai haulart,teemah, meenat sai kuma safina “har kun karaso kenan sannunku da zuwa kuzauna” tafada tana fitowa daga dakin“da mukacemiki muna kusa ai bakiyarda ba” cewar fina, murmushi ruhy tayi tareda cewa haulart da tun shigowarsu takebin kayayyakin shagon da kallo “haulart ga kayayyaki can kusa dake miko manashi” daukowa tayi tareda cewa “wlhy ruhy kina kokari yanzu duk wadannan kayan kekikayi, murmushi ruhy tayi tace “kuntsaya surutu ko duba kayanma bakuyiba” dubawa sukafarayi sunata yaba kyan design din, dukkansu style daban daban tayi musu kuma babu na kushewa, teemah ce tace “ruhy ina naki” “ban dinka nawaba tukunnan dan naga har yanzu bikin da saura, sai next upper week fa, ai kuma kunyi hanzari” “ to ai yafi adinka da wuri sabida hankalinmu ya kwanta dukda ke kinada alkawari, inkin bawa mutum time bakya failing dinshi"cewar meenat sai ruhy tace “nikam sai ana saura two days zan dinka” haulart dake danna waya ne tace “ kai kai ruhy wlhy inason wannan abayan baima dade kikayi posting ba” ai sai dukkansu sakayi inda haulart take zaune suna kallon abayan awayarta, finace tadago ta kalli ruhy tace “to aima abayanne ajikinta” duka suka kai dubansu ga ruhy, dan kwata kwata basuma lura da kayan jikin taba “wlhy kuwa kuma yamafi kyau azahiri, gaskiya inaso” cewar meenat “wai ya ake ciremune aciki, ai muma munaso ko fina?”.