BODDIYA

FREE PAGE-5

by @xayyeesherthulhumaerath

Bismillahir-Rahmanir-Rahim

Kashi yake ji amman ya gagara tashi don yasan yana shiga toilet binsa zata yi.

Tashi ya yi tsaye yana zagaya dakin,ita kuwa idonta kur akansa tana binsa da kallo. Ganin babu sarki sai Allah kashi kara shirin fitowa yake da gudu ya nufi toilet din ya ma manta ko kulle kofar bai ba. Aikuwa binsa tai ta tsaya bakin kofar tsuru tana kallonsa yadda ya zauna kan toilet din. Irin gudawan nan mai ƙara da wari ya sake, da sauri ta toshe hancinta tana yi masa dariya. Ko kallonta bai ba sauri ya yi yaiy tsarki ya fito abunsa yana tunanin shin me zai yi ne ya yi maganin yarinyar nan?

Idea ce tazo mai ya kunna tv ,duk da cewa shi ba ma'abocin kallo bane hakan ne ma yasa ya kan mata da zaman wani tv a agidan nasa.

Kunna tv da set light ya yi , don mugunta sai da ya samo tashar Tom And Jerry tukun ya kunna mata.

Idonta idon Tv kuwa ta fara birkicewa jikinta na rawa,zata yi ihu kuwa ya fara mata nuni da hannu yana fadin, "Kina mun ihu cikin daren nan kuwa zaki sha mari,sai na miki dukan tsiya na yayyanka ki.

Haka ta takure tana toshe bakinta da hannu cikin yanayin tsoro. Har sai da ta bashi Tausayi amman ya fiske ya kwanta abinsa.

Ita kuwa a bata iya komawa barcin ba, domin sautin da take ji suna yi a Tv ma kadai kara firgitata yake bare kuma kallonsu.

A zaune ta rufe ido har asuba da ya farka ya ganta tukun ya kashe Tvn yana kara yi mata kashedi. "Kin ga inna kara shiga toilet,ko na fita wani gun kika bini har kafafunki sai na yanka,wawiya kawai ni da da yadda zanyi ma da jefar da ke zan awaje Amman na san haukarki ma kaɗai ta sa ayi zargina."

Maganar yake da baki kuma yana yi mata nuna da hannu,duk da cewa ba komai take fahimta ba,amman ta gane wasu abubuwan ciki.

Shiru kawai ta yi tana binsa d kallo idonta ya yi luɓu-luɓu. Toilet ya nufa domin dauro alwala har ya je zai shiga ya waiwaya ya ga ko ta biyosa,tana zaune abun ta yadda ya barta amman idonta na kan shi. A jiyar zuciya ya yi a zahiri yana fadin, "Alhmdu Lillah an wuce nan."

Sai da ya yi ya fito sannan ya mata nuni da ita ma taje ta yi. Haka tayi alwalan ta fito ta sa hijibi sukai sallan Bai koma barci ba kamar yadda ya saba Alqur'ani ya dauko yana karantawa har gari ya waye . Ya yi wanka sannan ya sa kayan tafiya asibiti.

Tana zaune bayan sun gama karyawa ya tashi zai tafi tana binsa da kallo cikin yanayin tsoro.

Kallonta ya yi,rai ɓace ya ce, "ki zauna a gidan nan ba inda zaki kuma kar ki taɓa komai za a kawo miki abinci anjima kiji, ki shiga toilet kiyi wanka kuma in lokacin sallah ya yi kije kiyi ka da ki fita anguwar nan ba mutane in kika fita kuma aka yankaki Shikenan ba ruwana."

Shi dai ya yi daidai gwargwadon yadda za ta fahimta ko kadan nan sannan ya fita,kuma ya tabbatarwa da mai gadin kan cewa tana ciki ya lura da ita sannan anjima za a kawo mata abinci.

Ya fice da motarsa cikin sauri.

Yana zuwa Ammur ya ce, "Ah ina take yau kuma? Ko ta daina gadin naka ne yanzu?."

Tsaki Rowan ya yi ya wuce cikin office dinsa

Binsa ciki Rowan ya yi yana, "haba aboki na ko gaisawa ba zaka tsaya mu yi ba? Ba ma wannan ba muyi maganar gaskiya kasan dai koma yane ba zan so ganinka cikin damuwa ba ko? Ya kamata mu nemawa kai mafita Dangane da yarinyar cen duk da cewa ban sani ba ko ka samu mafita." Ya karasa maganar yana zama.

Rowan ya ce, "babu wata mafita fa illa mu zubawa sarautar Allah ido,ko na ce zan je in jefar da ita zuciyata bata taɓa amincewa da hakan,a tunanina ma kamar ta samu matsala a kwakwalarta don haka zan daukota a mata scanning ko hakan ma zai taimaka mana, na san dole akwai dalilin da Ubangiji yasa na tsinceta kar ka manta fa ranar na sha na bugu Sosai ba na gane komai amman sai da na tsaya na ganta kuma na dauketa abun ya matukar bani mamaki,tabbas akwai wani boyayyen al'amari da zuwan yarinyar nan gareni kuma zan jira har bayyanar hakan."

Ammur ya numfasa kafin ya ce, "babu shakka ka gama fadin komai kuma ka bayyanar da komai fatana dai Allah ya tabbatar da alkairi kawai amman kazo da ita a dubatan dai incase a kara samun madafa kar a sakankance."

Rowan ya amsa da 'In Sha Allah kuwa."

Ci gaba da harkarsa ya yi bayan ya je ya duba halin da marasa lafiya ke ciki ya dawo office din ya zauna ya karasa sauran aikinsa.

Sai da ya yi sallar isha kafin ya dau hanyar komawa gida. Yana shiga ciki kuwa da mamakinsa ba ita babu labarinta ko alamarta ma ,a takaice babu ko motsin wani mutum a cikin gidan. Ya tambayi mai gadi ko ta fita ne,ya tabbatar masa da cewa ba wacce ta fita cikin gidan. Komawa ya yi ,ya kara dubawa amman bai gantan ba. A zahiri ya furta, "ko dai daman ba mutum ba ce wannan yarinyar? To in mugum ce Ina ta yi? Ina kuma ta je? Can kuma ya yi ya ce, "Alhmdu Lillah in ma aljanar ce dai na fi karfinta ne watakila yasa ta gudu, Allah raka taki gona."

Kitchen ya nufa ya dafa ruwan tea da kansa ya zo yana sha bayan ya gama sha ya cire kaya domin ya yi wanka ya kwanta hadda tofe dakin da addua yana murna Allah ya rabasa da alaƙaƙai. Buɗe toilet din da zaiyi ya hango mutum cikin baf din wanka kwance da alamar wani abu a hannu.

"Subhanallahi, Astagh-fi-rullah." ya furta yana karasawa a hakankali. Aiko ita ce kwance da takeaway din abincin ranan da aka kawo mata,da abincin duk ya xuzzuba a jikinta tana ta sharɓan barcin da batai jiya ba.

Ashe ita a tunaninta cewa ya yi inta ci abinci taje can ta kwanta.

Duma mata duka ya yi, yana fadin, "Kee! Kee!! Kee!!! Tashi dalla ki tashi waya ce miki nan wajen barci ne wai? Ya Allahu na gode ma ,har ina murna ashe da saura na."

Tashi ta yi tana wage baki ita adole Tana murna ya dawo ganin fuskar shi kamar ta shanu yadda ya saba ya sata saurin bata rai ita ma.

Fisgota ya yi daga cikin baf din da ya ga bata da niyar fitowa, kokarin daukan Takeaway din take da ya mata wata irin tsawa sai da ta fice aguje. Bayan gidan ya zam tamkar gidan biki ga abinci ga zarni ta ko ina ta samu fitsarin ta take sharɓawa. Haka ya zauna ya wanke na wankewa ya share na sharewa kafin ya samu ya yi wanka.

Ya gaji sosai domin ya sha aiki a asibiti hakan yasa ya kwanta da wuri ba tare da kulata ba,tunda ya nuna mata tea da bread ya yi gaba. Kan ta gama har ya yi barci tsabar gajiya. Zuwa ta yi gabansa ta zauna a hankali don ita mamakin gemunsa take,domin bata ma taba ganin gemu irin nasa ba, sa hannu ta yi tana shafawa kamar cikin mafarki ya ji ana tabasa yana bude ido kuwa wa zai gani? Ko a jikinta ya bude idon amman kara daura hannu a gemunsa take,jan fuskarsa ya yi yana bigeta sai da ta wuntsila kasa ta bige goshi yana masifa, "wai ke wacce irin jarababbiyar yarinya ce? Ki kiyayeni fa, zan ajiye tausayin da nake miki a gefe in miki duka na fitan hayyaci."

Faduwan da ta yi kuwa harta fasa goshi rikewa ta yi da hannu tana shashsheƙar kuka agefe.

Ko juyowa bai ba ya ci gaba da barcinsa.

Da asuba kuwa yana tashi bayan ya yi sallah ya zo tashinta ya ga fuskarta gaba-daya ta ɓaci da jini, ga kumburi cikin sauri ya tallafota yana, "Subhanallahi sannu." Da sauri ya dauko box din sa ya mata treating goshin sannan ya rufesa da bandeji.

Har aransa bai ji dadi ba kuma bai so ba,duk da cewa ita ta janyo.

Daga ranar ta daina binsa ko ina za shi,ko kallonsa bata yi ,suna haɗa ido ma kawar da kai take, in ko yaje asibiti inda ya barta haka zai dawo ya ganta a takure tasa hannu a baki banda tsoronsa ba abun da take ko waya yake yana daga murya take firgita, har ta zaɓi zama a gidan ita ɗaya fiye da ta ga ya dawo gabanta yata faduwa kenan, abinci kullum ko kwata bata iya ci bare rabi,ta rame fiye da yadda ya daukota gata kullum cikin zazzaɓi Kasancewar tsananin ciwo da kanta ke yi mata.

Tun abun baya damunsa har ya fara damunsa, hakan ya yasa shi yanke shawarar kaita asibiti ayi mata scanning din kawai ko za asamu mafita,don duk tsiya bai son ganin mutum a takure haka.

Haka yasata shirya tana ɗari-ɗari da jan gefe . Suna zuwa asibitin sai da ya fito da ita sannan ta fito, Ammur ya kalleta cike da mamaki ya ce, "subhanallahi me ya sameta a goshi kuma?"

Rowan ya kauda kai yana, "Manta kawai."

Murmushi kawai ya yi , domin ya san tunda ya bashi wannan amsar ba wata bayanta ya ce , "Za ayi mata scanning din kenan."

Rowan ya ce, "e gata nan ka tafi da ita."

Mika mata hannu Ammur ya yi da nufin tazo. Da sauri ta koma bayan Rowan tana buya.....

★★ Mutum ukun farko da suka fi sharhi a free pages zasu karanta har karshe kyauta In Sha Allah★★★

TALLAH

🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃 mata mutanenmu in,baku bagida amarya da uwar gida kai harma da zawarawa wadanda zaakaiwa toh kuzo ga dama tasamu Mmn Muhammad Yar mutan Sokoto tazomuku da sha hararrun kayan mata eh manya manya Hajiya gafa kayanda kun kadade kunajiranan sunzo muku har gida mata kuhita Ku gyarama oga yajidadi kunsan ance ko kanada kyau kaqara da wanka sayen nagari maida kudi gida 🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️💃💃💃 Muna Sokoto muna izakayammu ko Ina bi iznillah Ehn saudiya kuma kumaso ayi da kuwa yan Niger kuna Ina ga dama tazo muku hargida🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️ Siyan na gari mai da kudi gida💃 ***

*** Urs Xayyeesherthuo [2/20, 10:12 AM] Xayyeesherthul-Humaerath: *BOƊƊIYA*

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.``` °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

****

RUBUTAWA Aisha Sani Abdullahi *(Xayyeesherthul-humaerath)*

_Hi,Hello,Fans😍Gani na dawo da wani labari mai ɗauke da nishadantarwa, ilimantarwa ....... ba ma sai na ce komai ba,ku kun sani kuma zaku bada labari, Kafin in ci gaba da Series din Yel na ce bari mu taɓa wanan,kada ku bari a baku labari domin labarin na musamman cikin musamman dinma na daban ne_