BODDIYA

Note: littafina na kudine, 300 Normal Group, Special 500

by @xayyeesherthulhumaerath

LAST FREE PAGE-11

Bismillahir-Rahmanir-Rahim

Free pages na daf da karewa In Sha Allah daman na ce ba zan yi da yawa ba.

*Payment Still On Going...*

Pay Into 1453215759 Aisha Abdullahi Sani Access Bank

Evidence of Payment To *** In Kuma Kati ne ma Transfer Or Message ***

★★★

Shirin biki ya kankama an shiga gyaran gida ta ko ina yi ake Ba yadda Rowan ya iya haka ya sanar da Ammur domin ya tawo Malaysia suyi shirin bikin. Aikuwa ba ɓata lokaci ya fara shirin zuwa.

Rowan na zaune ya lallaɓo kawu mata abinci ta ce, "Na Gode Baddo." Bude baki ya yi cikin mamaki ya ce, "What? Magana kika yi? Maimaita inji."

Dariya tayi tana zare hannunta abaki ta ce, "Na gode Baddo am."

Kasa tsayuwa ya yi,ya zauna har yana kokarin faduwa ya ce, "To mene ne Baddo? Kuma ya aka yi kika fara magana maganar ma da harshen Hausa?"

"Baddo kyakkyawa, Baddo am kyakkyawawana, Hausa kuma yaren duniyar ku ne ai da kake mun na ji na fara iyawa nima."

Har yanzu dai cike yake da mamaki ya kasa rufe baki tashi ya yi yaje ya sawa kofar bangaren gaba-daya key sannan ya dawo ya zauna yana. "Ma sha Allah, Alhmdu Lillah to ki fada mun sunanki da kuma duniyar da kike."

"Sunana Ayshatou , Duniyar mu kuma ban san ya zan fadeta da taku ba,amman abu ɗaya na sani mu bama rayuwa kamar taku,bama da Tv,gado irin wannan,gida haka,komai ma ya bambanta domin mu cikin bishiyoyi muke rayuwa da jinkoki agefe wanda suke zama makwanci a garemu,kammmaninmu ma da naku ba iri ɗayane da kwai bambanci sosai musamman wannan gemun naka ban taba ganin me irinsa a duniyarmu ba." Ta karasa maganar tana taɓa masa gemu. Bige mata hannu ya yi,yana,"zan kamaki." Ya gyara zama kafin ya ci gaba da magana, "Allah mai iko niko zam so inji komai dangane da duniyarku da ma yadda akai kika shigo wannan duniyar tamu."

"Duniyarmu wata irin duniyace wacce kowa ya san kowa kuma kammanin mutanen cikinta yake kala guda illa ni ɗaya tilo da na bambanta da su." ta fada tana share hawaye.

Rowan ya kasa hakuri cikin zaƙuwa ya ce, "me yasa kika bambamta da su? Meya faru?"

"Saboda ni baƙa ce,wai ni fata ta batai kalam nasu ba,kuma bana da kyau kamar irin na su,saboda haka mahaifina ya rabu da mahaifiyata kan cewa ni ba 'Yarsa ce ba,tun daga ranar da nazo duniya ta fara fuskantar kalubale domin ko suna ba shi ya samun ba ita ta rada mun da kanta,ko su jefar dani ko kuma ya rabu da ita,bana da kawaye bana da kowa sai mahaifiyata tun ina asalin karamar yarinya ko wasa yan uwana yara suke da zaran naje wajen suke watsewa gudun kar in shafa masu fatar jikina suma su zama kamar ni,ban san meyasa Ubangiji ya yi daban cikin su ba,amman nasan cewa akwai dalili wannan furucin mahaifiyata ke fadamun a kullum aduk sanda ta riskeni ina kuka ko kunci saboda tsangwamar da nake fuskanta,har ta kai ga tana kirana da Boddi (kyakkyawa) duk Don ta kawar mun da damuwa, su sauran mutane Kulludo suke kirana da shi ma'ana mummuna,a karshe Masarautar duniyarmu muka koma nida mahaifiyata saboda Sarkin ne kawai ya iya tausaya mana ya Aureta tare da amincewar zata iya shiga dani masarautar amman duk da haka ban tsira ba domin kullum kulle nake a daki in ko na fito ba mai kulani daga masu darewa sai masu gudu, dalilin zuwana wannan duniyar kuma ban sani ba kawai dai na san akwai wata rana da Sarkin duniyarmu ya kirani kan cewa na cire madaurina zaiyi abu a jikina na ji tsoro sosai na gudu wanda har ya fara barazana ga mahaifiyata kan cewa ya sani abu mai mahimmanci naki mai zai rabu da ita yama koremu gabadaya, ban san me zaiyi dani ba amman naji yana cewa bokansa ne ya ce ya yi abun da ni don nicce mafitar da zai iya mulkar garin har karshen numfashinsa,hakan yasa wata rana yana bina ina gudu karshe yasa an kamoni an kulleni a daki mahaifiyata na kuka ni ina kuka ya yi abun da zaiyi sannan ya bada ni wa fadawansa kan cewa su fidda ni daga wannan duniyar gaba-daya domin zamana zai xubda masa da kimarsa idon jama'a."

Sai a lokacin Rowan ya fahimci cewa Ayshatou yar kasar Singa ce,fulani ne a kasar amman masu bambancin al'ada da dabi'u domin su har yanzu wadataccen addini ma bai je masu ba, rayuwa suke tamkar ta awaki amman wai duk da hakan musulmai ne, gaba-daya farare ne yan kasar maza da mata sannan basa da wani cikakken kaya sai wani madauri da suke daure ƙugu, sai kuma na kirji ma da mata ke daurawa mazan kuwa iyaka na kugun ne,A al'adarsu ranar da mace ta fara fitar da jinin al'ada aranar ake daura mata aure ga duk wanda yake da bukata domin su a ganinsu hakan alama ce ta nuna cewa mace ta isa aure zata shiga gidan miji kuma aranar ake sanar da yaran komai na dangane da rayuwar aure,Sannan fulatancinsu ba irin na kowanni Fulani bane kamar yadda al'adarsu take hatta sallahma yinta suke kawai ba tare da sanin abubuwan da ke cikinta ba sannan sam basu dauki rayuwar 'Ya mace da wani mahimmanci ba bare kuma batun darajata matan basu san ko ina ba,kuma basu san komai ba hakan yasa suke kallon cewa duniyar su daban data wasu in banda mazan da ke iya fita kasashe daban-daban babu shakka harkar tsafinsune da son zuciya yasa Sarkin su kuma mijin mahaifiyarta ya hake ma yarinyar da ko balaga batai ba "

Numfasawa Rowan ya yi yana neman mafitar da zai kawar wa da Boddi tunani ya ce, "kin ce Mun Boddo to yanzu in zan ce kyakkyawata me ake cewa?"

, "Boɗɗiya."ta fada

Share mata hawaye ya ci gaba da yi "Eheen to daga yau sunanki BODƊIYA ,ba ki san cewa ke kin fi duk matan duniyoyi gaba-daya kyau ba har ma da taku? Ai bakake sun fi kyau kuma gaskiyar Mamanki ce ,ke kyakkyawace a kyawawanma ta musamman ." Karasa maganar ya yi aransa yana kudurta cewa duk yadda za ayi sai ya kawo sauyi ga rayuwar Boddi ya sa tayi karatu boko da na addini taje kasarsu ta nuna masu cewa ya mace ba abar tozarci bace,haka kuma bakaken fata ba abun gudu da wulakantawa bane domin kowanni Dan Adam Ubangiji ne yayisa kuma ya masa kalar matar da yaso ya gansa komai da dalili.

Girgiza kai ta yi tana, "Aa in ni kyakkyawace me yasa za ana guduna to ?"

Rike mata hannu ya yi,ya ce, "kin yarda dani ?"

Girgiza kai tai alamar e

"To ke kyakkyawace , kyakkyawata kin ji ko?"

Ta kara girgiza kai.

"To yi min murmushi."

"Umm umm ." Ta ce tana shagwabe fuska.

Cakulkuli Rowan ya fara mata bata san lokacin da ta fara dariya ba karaf sai Granny suka gani gabansu ashe ta zata baya nan ne ta dauko key ta bude har ta shigo basu ganta ba.

Suman tsaye tayi kayan da ke hannunta nan take suka fadi.

Ita ko ganin yadda granny ta fante fuskarta ne ya hargitsa mata kwakwalwa nan take ta fara surfa ihu tana shishshiɗewa.

Ita ma Granny ihun ta fara tana karkarwa.

*Ma sha Allah yanzu aka fara ko ince za a fara,free pages ya kare hajiyata da 300 dinki zaki sha karatu hankali kwance ga account number cen asama zaki dauka sannan kimun magana ta WhatsApp *** domin saki a paid group ,Thank You all,Yau duk wacce comments dinta ya mun sugar nayi alkawarin sata a Payment group kyauta😘😘 urs Xayyeesherthuo*

*🤝 SDEENDTM DATA SERVICES🤝* *MTN* . *Airtel* 1GB = ₦300. 1GB = ₦300 2GB = ₦600. 2GB = ₦600 3GB = ₦900. 3GB = ₦900 4GB = ₦1200. 4GB = ₦1200 5GB = ₦1500. 5GB = ₦1500

*GLO* . *9MOBILE* 1GB = ₦350. 500Mb ₦500 2GB = ₦700. 1.5GB ₦1100 3GB = ₦1050. 2GB ₦1600 4GB = ₦1400. 3GB ₦2000 5GB = ₦1750. 4GB ₦2500

*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH* For cable subscription or sell recharge card Call this number or whatsapp 👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽 *🪀****