JAMEEL

FREE PAGE -1/2

by @xayyeesherthulhumaerath

_*Fejin Farko na ki ke Antyna Real-Shaxee,Fatan Allah ya saukeki lafiya 🙏😍*_ __________________________________________________________

_*BISMILLAHIR-RAMANIR-RAHIM*_

_Kamar yadda nafara lafiya Allah ka ba ni ikon gamawa Lafiya🙏ALLAH YA SA RUBUTUNA YA AMFANAR DA AL'UMMA SANNAN YA NISHADANTAR DA SU😍_

******** kwance yake ya na bacci da kaga yanayin fuskarsa tare da kwanciyar da ya yi, za ka tabbatar da cewa ya na cikin nishadi tare da kwanciyar hankali, mafarki ya ke Wanda ke bayyanar da murmushin sa a zahiri, wata yarinyar ya hango ta na fadin, "Umm umm Yaya Jameel ka tashi Dan Allah nafadama ka tashi wai so ka ke nayi letti a zaneni ne? Ka tashi ka ji," cikin magagi ya ke fadin, "Ayya Janaf di ta barci nakeji fa kije Driver ya kai ki."

Kuka ta fara tare Da dukansa tana, "Ni dai Wallahi driver ba zai kai ni ba."

Jin sautin kunkanta ya ke har cikin ransa hakan ya sa shi farkawa arazane ya na waige-waige.

"Subhannallah jawahir ina ki ke? Ki dawo Dan Allah zan kai ki Skul din kinji ko?" A bin da ke fitowa daga bakin JAMEEL kenan ya yin da ya ke zubda kwalla.

Dafa kai kawai ya yi da hannuwansa Dan wani irin radadin zafi da kan ya fara ma sa kamar kullum a yayin da ya fi kewar JAWAHIR.

Jan yo Box din maganinsa da ke kan bedside ya yi, ya sha sannan ya tashi ya yi wanka, A cikin kakinsa na Sojoji ya fito, Wanda da ka gan sa zakasan cewa wannan cikakken jami'in tsaro ne, ba karamin kyau shigar ta ma sa ba, dauko turarensa ya yi zai faisa sai kawai ya fara jin muryar JAWAHIR A kunnensa , "Yayana a duk lokacin da za ka yi wanka ka yi kwalliya to indai ba ka sa turare ba ina mai tabbatar da ce ma ka wankan ka bai kammala ba kuma ko da mun hadu kai ba Yayana ba ne indai ba ka kamshi, domin Kamshi ba ya taba barin jikin Yayana." Wani irin Murmushi ne ya bayyana afuskarsa Wanda zan iya cewa da bai kai zuci ba, fesa turaren kawai ya yi sannan ya dauki wayarsa ya na kallon Yarinyar da ke jikin screen din wayar,black beauty Sanye da doguwar Riga murmushi ta ke Wanda ya kara baiyanar da kyan fuskarta tare dimple din ta mai dauke hankali mai kallo.

Zuba ma ta ido ya yi kawai ya na kallonta sai da ya kusa diban 30 minit kan ya kalli agogon wayarsa 8:30, Tsakin takaici ya yi kawai sannan fice daga dakin.

Da takun kasaita ya ke saukowa daga stairs din duk da ganin ya makara Amman ko ajikin sa, ya na saukowa Fatima ta karaso garesa da Murmushi ta na fadin, "Yaya ga abincin ka nan a kan daining ina ta jira ka fito Amman shiru."

Ko dagawo ya kallota bai yi ba, kawar da kan sa ya yi tare da fadin, "Nagode Amman dai kam na koshi ba na bukatan wa ni abinci a yanzu."

Bai bare ta ko kara magana ba ya cigaba da tafiyarsa.

Ita kuwa bin sa kawai ta ke da kallo, tana jin zafin abin da ya ke ma ta Amman tafijin tausayinsa fiye da komai domin duk Wanda yasan JAMEEL ya san cewa cikakken mutum ne Wanda ko wace mace ke burin samun sa, kyan hali ga kyan diri, ilimin addini da na boko.

Sai da hawaye ya fara gangaro ma ta da ga idanunta kan ta Ankare tai murmushi sannan ta goge hawayen ta haura sama da gudu.

D'akinta kawai ta shige ta kwanta a kan gado ban da zubda kwalla ba abin da ta ke.

Jameel na fita ba inda ya nufa sai office, ya na shiga da rawar kai Sofe ta, tawo garesa ta na, "Welcome Oga Ai ni nazatama bazaka sami damar zuwa yau ba ne." Durkusawa tai ta karbi files din hannunsa sannan ta daga hannu da nufin gyara ma sa butil din Riga, dakatar da ita ya yi da hannu kawai ya ja dogon Tsaki sannan ya shige cikin office din sa.

Ko ajikin Sofe domin indai wannan ne ba yau Jameel Ya fara disgata ba Amman fa ita komai zai yi birgeta ya ke sannan Kaunar shi kara shiga zuciyarta ya ke a kullum, murmushi kawai tai tare da bin sa a baya, shiga ta yi ta ajiye file's din a kan table ta Sara ma sa sannan ta ce, "Shin da wani taimakon da zan iya ma?"

Dagowa yayi ya kalleta sannan ya kawar da kai ya ce, "I need Coffee."

OK kawai Sofe ta ce domin tasan cewa tin da ya ce Coffen nan to ba makawa shi ya ke so.

Jiki na rawa taje ta kawo ma sa Dan gwaninta hadda meat-pie da hike ta San ya na so.

Ta takawo har ta ajiye bai dago kai ba sai da takusa fita ya na ganin Meat-pie, murya a sama ya ma ta wa ta tsawa ya na, "Wannan Meat pie din fa? Na ce mi ki Ina so ne? To zo ki dauke shi a wajen nan bana bukata."

Jikina na rawa Sofe ke fadin, "Am Sorry Sir, A tunani na ka na so ne."

Dakatar da ita ya yi tare da nuna ma ta kofar fita.

Tana fita ya dau coffen ya fara sha, yana duba files din da ke gabansa.

Kamar kullum indai ya je Office ba ruwansa da kowa harkar gabansa kawai ya ke yi,in lokacin sallah ya yi kam ba fashi komai mahimmancin aikin da yake barinsa ya ke domin gaida ubangiji, sai da kuma in abokin sa Mussaddam ya zo ne kawai za ki JAMEEL ya Dan sake suna hira sama-sama.

Misalin Karfe biyar JAMEEL ya tashi daga Office kasancewar bai da wani babban case a hannunsa, ba inda ya nufa sai gidan Ummansa.

Da Sallamarsa ya shiga dakin gaishe da Umma ya yi ta amsa cike da farinciki tana, "Andawo kenan."

Bai kara ce ma ta komai ba, kawai kwanciya ya yi a kan doguwar gujerar da ke fallon yana kallon sa ma.

Hawayene kawai ya fara zubowa daga idanunsa.

Umma da ke gefe ta ce, "Haba Dan Allah JAMEEL wai kai har yanzu ba za ka cire kan ka daga wannan halin ba ne? Kai kan ka kasan cewa ita kan ta wadda ka ke Dan itan bazata taba farinciki da zaman ka cikin kunci ba, ka yi hakuri ka kara hakuri ba kai kadai ba kasancewa mu ma kan mu har yanzu ba mu dawo seti ba, Amman muna kokari wajen danne zuciyarmu, da kyar a ka samu damar ceto ka Amman ka na so ka koma halin da ka shiga a baya ko? Kanaso ka rasamu mu ma ko? Ka karbi kaddarar ka hannu bibbiyu domin ubangiji ya na jarabtar mu ne domin ya ga yadda za mu amshi jarabawar."

K'okarin danne zuciyarshi ya fara Dan kar kukansa ya fito fili Amman bai San lokacin da kukan ya kara barkewa ba, da sauri Umma ta karaso gareshi tare da shafa ma sa baya ta na fadin, "Ka yi hakuri JAMEEL Dan Allah ka yi shiru in ba ka na so nima na fara ba ne."

A haka Umma ta kwantar ma sa da hankali tare kalamai ma su sanyaya zuciya, a take awajen ya fara bacci.

Karfe Shida da minti arba'in ya farka domin lokacin sallah ya doso, Alwala ya yi, ya nufi massalincin da ke cikin gidansu sai da ya jira har a ka yi isha sannan ya shiga cikin gida, Umma ta ce, "Yauwa ga abincin ka nan na ma ka na mussaman Yayan Ja... Kawai sai Umma ta Ankara tai shiru jiki a sanyaye kallonta kawai ya yi tare da sake ma ta murmushin da bai kai zuci ba.

Soyayyar doyace da kwai, tare da juice din Apple, za ma yi a kan kafet ya fara ci, ba wadda ya ke tunawa illa jawan sa ga ni ya ke kamar za ta shigo da dariyarta ta na fadin, " Kai Yaya Nafseen ni dai kar acinye a ragemin in ansami duniya sai a manta da Anty Jawa?"

A zahiri murmushi ya yi, ya na fadin, "Ban manta da ke ba kuma bazan taba mantawa da ke ba Janaf dina, kina raina har karshen numfashina."

Bai wa ni ci sosai ba kawai ya ji doyar ta ginshesa karamar kanwarsa ce ta shigo wadda kwata-kwata ba sa son haduwa da juna kullum wasan buya su ke, da sauri za ta shige dakinta ya ce, "Raiyna zo nan."

Kaman za ta yi kuka ta karaso garesa kai a kasa ta ce, "Ina hini Yaya?"

Amsawa ya yi da lafiya sannan ya ce, "Ki yi Hakuri kinji hakuri ya zame ma na dole wannan kaddarar mu ce, nasan me yasa ba kya son mu hadu."

Ta kasa ba sa amsa kawai shigewa daki tai da gudu tana kuka.

Bin ta da Kallo kawai ya yi sannan ya dauki keyn motarsa ya nufi gida.

Ya na shiga ya tarar da Fatima Zaune ta yi tagumi ta na jiransa.

"Sannu da dawowa." Cewar Fatima Kenan.

D'aga ma ta hannu kawai ya yi, ya cigaba da tafiyarsa, ta kara da cewa,"..

_Shin Soyayyar da ake nunawa littafaina da gaske ko, kuwa dadin bakine? Zan gane ta hanyar siyan wannan novel mai daraja afarashi mai sauki 200 ma su tura wa ta account_ _0097524644_ _Nafisa sani Access (Diamond) bank, ko kuma katin waya ta wannan number *** sannan ayi scrinshot domin turomin da sheda sai in suburbudaki a group, karki bari abaki labari da cin haram gwanda kici gumin ki ya fi kwanciyar hankali duniya da Lahira_

*Urs Xayyeesherth😍* [8/31, 11:41 AM] Xayyeesherthul-Humaerath❤️: ***

••••• _*JAMEEL*_•••••

_{Nafseen}_

_PAID BOOK_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION.*

________________________________________________

_We Are Here To Educate, Motivate And Entertain Our Readers._

________________________________________________ _A cikin kashi Dari na wannan labarin, 70% kirkirarre ne Wanda 30% ko ya kasance na gaskiya._

_*LABARI DA RUBUTAWA.*_✍️

_*Aisha Mohammed Sani (Xayyeesherth)*_