FREE PAGE -3/4
_*Yayata😰 ke daya ce Yar uwa ta jini agareni, ina rokon Allah ya ba ki lafiya🙏 Allah yakareki daga sharin duk mai bin ki da sharri😰dan Allah yan uwa Ku sa min yayata a addu'ah, Allah ya ba ta lafiya, ya kareta da ma sauran musulmai da ba su da lafiya🙏🙏Dan Allah Ku sa mu addu'arku*_ __________________________________________________________
"Ayya Yaya ga abincin ka nan fa ka zo kaci."
A fusace ya juya ya na, "Ni na ce mi ki ina jin yunwa ne? Ke kam wai mayyace ko ya ya? Dan Allah ki barni na fada miki ki barni." Tsakinnan dai na fama ya yi, ya na huci ya shige daki, har ga Allah a zuciyarsa ba ya jin dadin yadda ya ke ma ta Amman bazai iya controlling tempern sa ba, Dan haka kawai wa ni lokacin ya zabi ma ta shiru ya kyaleta Amman har yanzu ta ka sa fahimtarsa.
Hannunta kawai tasa ta dafa kan ta tana fadin, "Wayyo Allah na." Sannan ta shige dakinta, ta kullo kofar kawai.
Washe gari,,
Kamar kullum da sassafe JAMEEL ya ta shi da wannan azababban ciwon kan da ya ki rabuwa da shi, bayan ya idar da sallah ya sha magani, duk da kasancewar zafi da irin radadin da kan ke yi ma sa bai fasa karatun Al'qur'ani ba, shi daya ya ke yi Amman sai ya ke ganin kamar su biyune domin zakakkiyar muryan Little Jawansa ya ke ji.
Ya na kammala karatu ya yi addu'a tare da rufe Qur'anin wanda ya dinga shafa bayan ya na murmushi.
A zuciyarsa ya ke fadin, "Allah Sarki Jawana kamar yadda ki ke fadi min a kullum a duk San da na shiga cikin wani yanayi ba abin da zai min magani illa karatun littafi mai girma, da kan ki, ki ka fanso min wannan domin faranta min, ina matukar alfahari tare da son ki.
Sai da ya dibi wajen 30minit ya na tunani kan ya tashi ya yi wanka ya Sanya Kakinsa.
Karfe bakwai dai-dai ya fito cikin shigar sa yadda ya saba ban da tashin kamshi ba abin da ke fita, indai JAMEEL ya je waje, ko da ya bar wajen indai Wanda ya San sa ya zo to sai ya tabbatar da kamshin turarensa.
Kamshin Turarensa kawai Fatima da ke kitchen ta jiyo ai ko da sauri ta fito tare da karasowa garesa.
"Morning Yaya." Cewar Fatima.
Wa ni irin bakin ciki ya ji aransa ya na fadin, "Wai wannan wace irin mayyace?"
A zahiri kuwa ya kawar da kansa tare da fadin, "Morning."
Ya cigaba da tafiyarsa ta kasaita kamar ya na tsoron ta ka kasa.
Motarsa ya nufa da sauri mai gadi ya bude ma sa get domin yasan halin mai gidan na sa ba wasa.
driving ya ke Amman kamar dole ban da kira'a ba sautin da ke tashi acikin mota, bin karatun ya ke kawai, azuciyarsa ya na jin dadi Amman da ka gansa azahiri dai kam kamar kullum fuskar nan ba fara'a.
Wani karamin gida naga ya nufa da yin Horn duk da kasancewar gidan karamine Amman ba karamin tsaruwa ya yi ba.
Wani Yarone da ba zai huce shekara shida ba ya fito da gudu ya na fadin, "Yes Na San Yaya JAMEEL ne."
Shi ko JAMEEL Da ya fito tsayawa ya yi kawai jikin motar ya na murmushi tare da jiran karasowar yaron.
Da Sauri ya rungumesa ya na fadin, "I Really Really Miss u Yaya, me ya sa kadaina zuwa?"
Shafa kan yaron ya yi ya ce, "Aiki ne yamin yawa Haneef , am really sorry, insha Allah bazan kara diban kwanaki haka ba tare da Nazo na ganka ba."
Haneef ya daga karamin Yatsansa tare da fadin, "Promise?"
JAMEEL ya ce, "Promise, Insha Allah Autan Mother."
Haneef ya yi dariya tare da fadin, "Zo mu je in kai ka gun Mother Dan nasan ita ma ta yi kewarka sosai."
Bin sa kawai JAMEEL ya yi ban da surutu ba abin da Haneef ke ma sa tin ya na tankawa har ya gaji ya yi shiru.
Suna shiga Haneef ya ce, "Ina ki ke Mother na je na daukomana Yaya JAMEEL ne a jirgina."
Mother da ke zaune a kan kujera tana chatting ta ce, "Allah Haneef ka ki yayeni wannan shirmen na ka."
Karaf sai ta ji sallamar JAMEEL.
Da sauri Ta mikye tare da fadin, "A Ashe dai da gaske ne munyi babban bako yau agidan, Welcome Son, kan ma mu gaisa barin hadama kayan breakfast Dan nasan ba ka yi ba.
Murmushi kawai JAMEEL ya bita da shi.
Ta shige kicin within 10 minit ta kammala hada ma sa komai da ya ke daman suma ba su yi break din ba, shirin yi dai suke.
Jera ma sa a kan kafet din ta yi domin tasan JAMEEL bai cika son cin abinci a daining ba.
Sinasir ne da Vegetables Soup, sai tea.
Mother ta ce, " Yauwa to Morning JAMEEL. "
JAMEEL ya fara Sosa k'yeya tare da fadin, "Morning Mother, ya kwana biyu?"
Murmushi Mother tai tare da fadin, "Lafiya lau, kullum sai Haneef ya isheni da inkiraka ka zo."
Haneef ya ce, "Mother ni yau da Yaya JAMEEL zan yi break."
" A'a Ka bari nasa Abu ta hada ma na namu a daining karka damu JAMEEL Dan nasan surutunka ma kadai ya isa ya kosar da shi."
JAMEEL ne ya mikawa Haneef hannu ya na, "Aa Mother ya zo muci ko ma na iya ci."
Tashi tai tare da fadin, "Ai kuwa ka sha surutu."
Sun fara ci kenan Haneef ya ce, "Yaya JAMEEL ka ki ka kawomin Aunty Jawana ta zo mu yi wasa."
Daga ambatan sunan Jawahir ya chanjawa JAMEEL ya na yi, ya rasa abin fadi, wani irin radadi kan sa ya fara yana kokarin juyawa, da sauri ya dafa kan ya na salati.
Da gudu Haneef ya tashi ya na , "Mother, Dady ina Ku ke Yaya JAMEEL zai yi kuka ya rikye kan sa."
Mother da Dady da ke daki da sauri su ka fito suna, "Subhannal JAMEEL what's Wrong."
Dady na ganin ya rikye kansa karasawa garesa ya yi tare da rikye kan shi ma Addu'o'i ya fara ma sa a hankali har kan ya fara Sauka, sai da JAMEEL ya dawo dai dai kan Dady ya sake shi ya na fadin, "Wai daman Har yanzu ciwon kan nan bai bar ka ba?"
Haneef da ke gefe ya na kuka ne ya ce, " Ni a kawomin Aunty Jawana, Yaya JAMEEL kadaina ciwon nan ni Aunty jawana na ke so."
Mother ce ta ma sa wata gigitacceciyar tsawa tare da fadin, "Haba Haneef ni daman nasan duk yadda a ka yi kai ne sillan ciwon kan JAMEEL, to Wallahi ka kiyayeni a hakan ne ka ke so A kawo ma Auntyn na ka, kana sa Yayanta ciwo?"
Dady ya ce, "Haneef ka yi shiru je ka yi wasa ka ji ko Auntynka na nan zuwa."
Ya na fita Dady ya ce, "Ke ma dai bai kamata kina ma sa tsawa haka ba, kin San ba Wanda ya shaku da shi sai ita, gareka kuma JAMEEL na fuskanci cewa har yanzu ka kasa daure zuciyarka, domin ya ci ace wannan ciwon kan ya rabu da kai Amman ka kasa cire tunani a zuciyarka, ka yi Hakuri ka kama aikinka hannu bibbiyu ka cigaba da Ceton al'umma domin cikawa Jawahir burinta.
Godiya JAMEEL ya wa Dady tare da fadin, " Barin je in shiga gidan Umma in gaidata kan na huce Office Dan na ga lokacin ya kusa kurewa.
Gidan Ummansa ya shiga ya gaishe zai fito Kennan ya ji sautin Raiyna ta na kuka.
Dawowa ya yi, ya shige dakin tare da ma ta wata gigitacciyar tsawa, "Wannan wani irin iskanci ne za ki cikawa mutane gida da ihu? Kina lafiya kuwa? Ki ma na shiru a wajennan." Tsaki ya ja sannan ya fice afusace, Umma da ke tsaye ta na kallonsu girgiza kai kawai ta yi sannan ta shige dakin ta.
Ya na fita ya nufi office..
*****Wata yarinya da bazata huce shekara 16 ba na hango rikye da tulin ruwa ta na tafiya a hankali, rera wakar su ta fulani kawai ta ke.
Wani matashin sauri da ya tawo da yan korarsa ne ya karaso gareta ya na fadin, "Ke Jawahir wai ban hanaki fita dibo ruwa ke daya ba ne? Iye ban ci ki na bari sai na zo mu tafi ba.
Fuska araunane ta shagwabe tare da fadin, " Umm Yo ni Goggona ta ce fa indai na kulaka ni ba ruwana da kai."
A fusace Jafaru ya wullar da tulin da ke kan Jawahir ya na , "Goggonki din banza ita har ta isa ta rabani da ke?"
Ba abin da Jawahir ta tsana irin a zagi iyayenta tuni ta fashe da kuka awajen .
JAMEEL ya ga files ya na dubawa Kennan sai gabansa ya fadi files din ya zube sautin Kukan Jawansa kawai ya ke ji.
_Shin Soyayyar da ake nunawa littafaina da gaske ko, kuwa dadin bakine? Zan gane ta hanyar siyan wannan novel mai daraja afarashi mai sauki 200 ma su tura wa ta account_ _0097524644_ _Nafisa sani Access (Diamond) bank, ko kuma katin waya ta wannan number *** sannan ayi scrinshot domin turomin da sheda sai in suburbudaki a group, karki bari abaki labari da cin haram gwanda kici gumin ki ya fi kwanciyar hankali duniya da Lahira_
Urs Xayyeesherth [9/1, 2:20 PM] Xayyeesherthul-Humaerath❤️: ***
***
••••• _*JAMEEL*_•••••
_{Nafseen}_
_PAID BOOK_
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION.*
________________________________________________
_We Are Here To Educate, Motivate And Entertain Our Readers._
________________________________________________ _A cikin kashi Dari na wannan labarin, 70% kirkirarre ne Wanda 30% ko ya kasance na gaskiya._
_*LABARI DA RUBUTAWA.*_✍️
_*Aisha Mohammed Sani (Xayyeesherth)*_