JAMEEL

FREE PAGE -5/6

by @xayyeesherthulhumaerath

__________________________________________________________

_*Wai kuna dariya dan na ce JAMEEL na da diri afejin farko🤣 wa ya CE mu Ku matane kadai ke da diri? To ysn duk wa ni namiji mai kwarjini ya na da diri🤨*_

A lokacin kan JAMEEL ya fara sarawa wani irin radadi ya ke ji fiye da na kullum da kyar ya samu damar zama sannan ya lalubo wayarsa Da ke kan table din ya kira Doctornsa Ku ma abokin sa Musaddam, Ya ma ka sa magana kawai sai nishi daga jin hakan Musaddam ya fahimci cewa akwai matsala ta ke ya ajiye aikin da ya ke yi ya fito domin nufar office din su JAMEEL.

Dasauri ya ke tukin domin shi kansa yanayin da ya ji Abokin na sa ya rikitasa domin abin da zai hana JAMEEL magana babbana ba karami ba.

Yanayin yadda Musaddam ya shigo ya rikita sauran sojojin mussaman ma Sofee sun San cewa akwai matsala kenan.

Bin sa suka yi dukan su ai ko suna shiga su ka tarar da JAMEEL kwance asume.

Dasauri mazan wajen su ka taimakawa Musaddam su ka daga JAMEEL a ka kwantar da shi agefe sannan ya fara ma sa taimakon gaggawa, cikin ikon Allah kuwa JAMEEL ya farka ya na fadin, "Musaddam Jawana wallahi Janaf na cikin matsala ta na bukatar taimakona, kuka fa ta ke yi Musaddam."

Maganar ya ke ya na kokarin tashi, tuni Musaddam ya ma sa allurar bacci daga nan jikinsa ya yi sanyi chan kuma bacci ya daukesa.

Gabadaya yan wajen Tambayar kan su, su ke wai shin wacece JAWAHIR? Wace irin Shakuwa su ke da Nafseen haka? To ma wai ina ta ke?.

Wannan tambayoyin da yan wajen su kewa zuciyarsu kennan ban da musaddam da shi kam yasan komai a zuciyarsa jimami ya ke tare da tausayama abokinsa na irin halin ya ke ciki.

Tun safe sai wajen Azahar kan JAMEEL ya farka.

****A bangaren Jawahir kuwa da kuka ta karasa gida.

Ta na shiga Inna ta dafa kai tare da fadin, "Handi imbomi, ni kam na shiga uku, Jauwahira yau kuma waya taboki?"

Zaman dirshem tai kasa ta fara birgima ta na, "Aradun Allah sai an biyani karamin tuluna, ni Allah bazan Yarda ba, kuma Kuma In...

Kawai sai ta kara fashewa da kuka, " Ni dai sai an min wani kuma ni Baffa ya hwadawa Jafaru ya yadaina kulani, Inna wari fa ya ke yi, ni Wallahi ba na kula kazami mai wari."

Sa ke baki kawai Inna tai ta na kallon ikon Allah, duk da ba yau ta saba ganin rigimar 'yarta ta ba Amman kullum da sabon salo ta ke zuwan ma ta.

Durkusa Inna tai tare da tallafo kan 'yarta ta, ta na , "Ki yi shiru Dadan Baffa ko kina so ni nima nai kukan ne? Ba ma ke ba ni kaina kinsan ba na son Jafaru ya kulaki, Yanzu ki tashi ki yi wanka na mi ki Dan malelenki."

Tuni JAWAHIR ta mikye ta na share hawayenta rumgume Innarta tai ta ce, "Ina Shonki Inna ta in na ki ka mutu zan yi kuka Dan haka ma ni na fiso inrigaki mutuwa, ki bari in fara mutuwa kinji?"

Murmushi kawai Inna ta yi tare da fadin, "Hmm diyar kirki ina mi ki so fiye da yadda ki ke tunani."

Da gudu JAWAHIR ta shige bandaki wanka ta yi sannan ta dauro alwala ta yi sallah ta idarwa ta kwalla innarta kira, "Inyaman hiri, zanci abinci."

Kwala ma ta kira ta ke ba ji ba gani kaman da gaske wa ni cin abincin kirki za ta yi.

Inna ta ce, "Oh ni Shatu jawahira wannan kwalla Kira ha ka? To gashinan."

Kawo ma ta tai sannan ta zauna ta na fadin, "kin ga aiki na ke yi inje kin karasa za ki ci ko?"

Shagwabe fuska JAWAHIR tayi tarw da tashi tsaye ta na, "Ni ni kam ma na koshi ba na jin yunwa."

Da sauri Inna ta janyota cinyarta ta ce, "Ai daman nasan za arina mutum ya na girma Amman bai San ya zauna ya ci abinci ba, sai dai abaki, ana bakin ma da kyar zakici, shiyasa kullum ki kenan kaman ahure ai."

Da kyar JAWAHIR ta danci sau biyar ta fara rikye ciki ta na, "Umm umm ni kam Allah cikina zai fashe Inna na koshi fa."

Inna ta ce, "Ai ko ba ki isa ba ko biyune sai kin kara."

JAWAHIR ta fara zame jikinta ta ce, "Laaa Inna kalli Samra za ta ci miki hatsi."

Samra jinjirar tinkiyace ta JAWAHIR wadda ta ke matukar kauna arayuwarta.

Inna ta fara waige-waige kawai JAWAHIR ta zura da gudu ta ce, "Yasin ni bani ci haka kawai kallan ki Fasa min ciki ya dawo irin na innatako? Anki in."

Gwalo ta ma ta, ta fice agidan ta na, "Natahi gun Baffa na."

Bin ta da kallo kawai Inna tai ta ce, "Allah dai ya Kara shiryamin ke Jawahira."

**************JAMEEL na farkawa Musaddam ya kai sa gida a falo ya kwanta ya na hutawa domin gabadaya jikinsa ya mutu ba kwari.

Saroro Fatima tai ganin JAMEEL a falo kwance da ya ke ta na daki ta ji motsi kan ta fito har Musaddam din ya fice.

Durkusawa tai garesa ta na, "Yaya JAMEEL lafiya kuwa?"

Daga ma ta kai kawai ya yi alamar Eh.

Ta kara cewa, "Ko da Abin da ka ke bukata?"

Ya kara girgiza kai.

Ba ta ga ji ba dai ta ce, "To ko in dauko ma babban filo?"

A fusace JAMEEL ya ta shi ya faskawa ma ta wani hamshakin Mari.

Sai da ta ji kan ta ya fara juyowa hazo-hazo ta Fara gani, shi ko haurawa sama ya yi ko kallonta bai kara ba bare ya ce uffan.

Jiri Fatima ta fara ji Dan haka tuni ta nemi waje ta zauna .

JAMEEL Ku wa kwanciya ya yi, barci ya fara daukansa.

Cikin baccin ya ji ana kiransa, "Yaya JAMEEL, ka zo mu yi wasa kaji."

Ya ce, "Auntyna ina zuwa bari in karasa hada file's dinnan."

JAWAHIR ta ce, "Allah fa ka ajiye ko inzo in ma chakukulo."

JAMEEL Ya yi murmushi tare da fadin, "To wai wayace mi ki jarumin maza na jin chakulkuli yasin ni bazan ji ba ko kinyi ma."

A sulale JAWAHIR ta karaso garesa sa hannunta tai ta rungumesa sannan ta fara ma sa chakulkuli ta na, "Za mu ga jarumin ai."

Dariya JAMEEL ya fara ya na, "Aunty Dan Allah ki bari."

Gabadaya ban da sautin dariyarsu ba abin da ke tashi a dakin.

A mafarki JAMEEL ya ke dariya Amman sautin ya fito fili.

_Shin Soyayyar da ake nunawa littafaina da gaske ko, kuwa dadin bakine? Zan gane ta hanyar siyan wannan novel mai daraja afarashi mai sauki 200 ma su tura wa ta account_ _0097524644_ _Nafisa sani Access (Diamond) bank, ko kuma katin waya ta wannan number *** sannan ayi scrinshot domin turomin da sheda sai in suburbudaki a group, karki bari abaki labari da cin haram gwanda kici gumin ki ya fi kwanciyar hankali duniya da Lahira_

*🤣damuwarku Kennan shin JAWAHIR din gida nawace? Amsar ta na ga ma su siyan buk din💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻*

Urs Xayyeesherth [9/3, 7:24 AM] Xayyeesherthul-Humaerath❤️: ••••• _*JAMEEL*_•••••

_{Nafseen}_

_PAID BOOK_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION.*

________________________________________________

_We Are Here To Educate, Motivate And Entertain Our Readers._

________________________________________________ _A cikin kashi Dari na wannan labarin, 70% kirkirarre ne Wanda 30% ko ya kasance na gaskiya._

_*LABARI DA RUBUTAWA.*_✍️

_*Aisha Mohammed Sani (Xayyeesherth)*_