FREE PAGE -7/8
_*AM SO SORRY DOTIE HAUWA SULAIMANš BAN GA SHARHINKI BA NE BA DA GANGAN NAKI KULAWA BA*_š„° __________________________________________________________
Karaf ya ji kiran sallar la'asar a kunnensa azatonsa inya farka da Jawan sai zai fara tozali sai ko aka sami akasin hakan wayam ya ga daki ba kowa illa shi kadai, Murmushi dole ya yi kawai ya zahiri ya ce, "Allah ya mi ki albarka Janaf a duk in da ki ke, ina matukar son ki tare da kewarki."
Wayarsa ya dago ya kalli hotonta da ke screem din ya ma ta wani hamshakin kiss Wanda ka ce dagaske ita din ce ba hoto ba, ajiye wayar yai sannan ya yi wanka ya dauro alwala sannan ya yi sallah.
Ya na idarwa ya fara dubawan wani diary me hade da hotuna wa ni gun ya yi murmushi wa ni wajen ko ji ya ke kamar zuciyarsa za ta tarwatse karaf sai ga kira ya shigo wayarsa dubawan da zai yi, ya hango Sofee ce.
Tsaki ya yi ya kawar da kansa har ya yanke ta kara kira.
Wani tsakin ya yi sannan ya dago wayar domin receiving a H-FREE ya sa ka sannan ya kara ajiye wayar.
"Hello Afternoon Sir fatan jikin dai ya yi sauki?" Cewar Sofee.
Tsaki ya yi wanda sai da sautin ya ratsa cikin wayar Sofee ta ji.
JAMEEL ya ce, "Ya yi Sauki Sosai karki da mu Am Feeling Better Now."
A bangaren Sofee murmushi tai tare da fadin, "Thank God, take care Sir."
"OWK" Kawai ya ce ya yi katse wayar batare da ya saurareta ba.
Ita kuwa SOFEE wanii irin dadi ta ji aranta wai yau OGA JAMEEL ne yadaga wayarta, rumgume wayar tai kaman mutum ta na fadin, "Ga dukkan alamu hakata ta kusa ta cinma ruwa, I really really love you Oga can't live without you, ko ma wace wannan Jawan ba ta gabana indai za ka soni to sai na kawar da ita atahirin rayuwarka, ina so na rayuwa da kai till the end of my life And I promise dole ne ka Aureni."
OGA UMAR ne ya ya zo hucewa ya katse ma ta tunani cikin tsawa , "SOFEE are u out of your sense? Wai tun yaushe na ce mi ki, ki je ki dubamin yaran chan."
Jiki na rawa ta ke Sara ma sa tare da fadin, "Am Sorry Sir."
Tsaki kawai ya yi, ya bar wajen.
Ita ko kara kalle hoton JAMEEL da ke bangon Office din tayi tai wani kayataccen murmushi sannan ta shige da sauri.
JAMEEL Ku wa gidan Ummansa ya nufa.
Ya na shigo Raiyna ta, tawo da gudu ta na rungumesa tare da fadin, "Oyoyo Yayana I really miss you oh, Na yi mafarkin Aminiyata ta ce min indaina kuka kuma na ma ta alkawarin bazan kara ba."
Dago da kan ta JAMEEL ya yi ya na shafa kan na ta ya ce, "Good girl ai ni ma haka na ke so nafison ganin ki kullum cikin farinciki kin ga nima na yi ko?"
Girgiza kai ta yi sannan ta ce, "Umn But Promise kai ma kadaina damuwa za ka dawo kamar yadda ka ke da."
Zama ya yi a kujerar da ke wajen sannan ya janyota cinyarsa ya ce, " Zan iya mi ki alkawarin komai Amman ban da maganar da ta shafi JAWAHIR kin San cewa wannan bangaren rayuwata ba na jin cewa nan gaba zan iya rayuwar farincikin da nai a baya, rayuwata ta sauya farinciki sai dai inga wa su na yi Amman ban da ni kam, domin JAWAHIR ta tafi da duk wata walwala da ke cikin rayuwata, ina ma ta so fiye da yadda na ke ma kai na, a yanzu kam ban da wani buri na duniya, yadda Allah zai yi da ni kawai na ke jira."
Kuka Raiyna ta fara ta na, "Yaya yanzu shikennan haka zamu cigaba da rayuwa cikin kunci?"
Share ma ta hawaye ya fara ya ce, "Nop My Little Sister ke da na ke jira ki samu ma na miji in mi ki Aure."
Dariya ta Fara ta na, "Umm Umm ni Gun Ummana zan zauna."
Ai ko sai ga Umma ta shigo ta na murmushi, "Ma sha Allah Ai ni haka nakeson ganin Ku cikin walwala, har kun sa zuciyata ta yi sanyi, Allah dai ya mu Ku albarka."
Zame Raiyna ya yi ajikinsa ya na, "Ina Hini Umma?
Da fara'arta ta amsa ta na, " lafiya lau, Amman ya naga kaman baka da lafiya kar dai ka CE min ciwon ne ya tashi."
Sosa kyeyarsa ya fara ya ce, "Aa Umma Dan zazzabi ne kawai."
Umma ta ce, "To dai Allah ya sa hakan, Allah kuma ya kara ba ka lafiya." Ya Amsa da Amin sannan ya tashi , "Barin Shiga masallaci Dan na ji anfara kira."
Raiyna ta ce, "Umm Yaya ka Dan rakani inga Haneef na dade ban gansa ba."
JAMEEL ya ce, "Aa yanzu fa dare ya yi Raiyna ki Bari da safe kan na huce Office sai mu je ko?"
Raiyna ta ce, "Owk Yaya Byebye zan jiraka."
Sallama ya yi ma Umma sannan ya fita.
Washe Gari
Misalin karfe 7 na safe JAMEEL ya fito cikin ka kin sa kamar yadda ya saba inya gama shiryawa tsaf a kullum sai ya dibi mintuna wajen kallon hoton kyakkyawar JAWAHIR din da kan wayar sannan ya bi ta da wani hamshakin Kiss mai tafe da sakonin soyayya na mussaman.
Fatima na jin takunsa ya na saukowa ta leko ta windownta kawai ta zuba ma sa ido.
Azuciyarta ta na fadin, "Mutum iya ka mutum, cikken namiji mai kwarji ni a ko ina Amman yanzu ya na son zama dodo ga al'umma sai ka ce a kansa aka fara, to ni kam wallahi yanzu nagaji ko kasoni ko kuwa ka sakeni na yi gaba wajen ma su kaunata, a kalla Aurenmu ya kusan kere shekaru biyu Amman ba ruwanka da ni ba ka taba shiga harkata, ba abin da ya taba shiga tsakaninmu kamar an ajiyema gunki, ko abincina ba ka taba ci ba, kai wai ni kam ko wace irin kadara na hadu da itane ko maganar cikakken minti biyar Ina ga ma ba mu taba ba, wallahi nagaji ni kam hakan ya isa bari kadawo yau za ayita ta kare Dan hakurina kam ya gaza kullum in na kai korafi daga nawa iyayen har na ka sai dai su ce min inkara hakuri in ma ka uzuri wataran sai labari, to ni dai har yanzu ban ga karshen labarin ba, bare ma a bayar."
Har JAMEEL ya fice ba ta sa ni ta na ta dogon tunani.
Sai da tagama tsara yadda yau za ta ma JAMEEL uwar watsi sannan ta koma daki ta cigaba da aikinta.
Shi ko JAMEEL ya na fita gidan Ummansa sa ya nufa domin cikawa Raiyna alkawarin kai ta gidansu Mother, duk da kasancewar layi dayane gidan ba nisa Amman Raiyna ba ta saba fita ita daya ba, ta gwammace ta jira yayanta ya kai ta.
Ai kuwa ta na jin karar motarsa ta fito da sauri ko bari ya gaida Umma ba tai ba sai ya kai ta gidansu Haneef.
Rikye Ma ta hannu ya yi suna tafiya a hankali har su ka isa Gidan.
JAMEEL ya ce, "To kingani ki shiga ni kam zan yi sauri in gaida Umma da Abba sannan intafi Office kar lokaci ya kuremin.
Shagwabe fuska ta yi ta rikyesa, " Umm Yaya indai ba zaka shigaba ni ma na fa sa mu koma kawai."
Bai kara cewa komai ba kawai riko hannunta ya yi su ka shige gidan, da gudu Haneef ya rumgume Raiyana ya na, "Oyoyo Aunty Raiyna kun dawo ina Anty JAWAHIR?"
Fara bugawa zuciyar JAMEEL ta yi hakan ya sa shi saurin fita daga gidan.
Raiyna kuwa ta ce, "Eh Ba gani ba Ai itama ta na nan Zu wa muje mu gaida Mother da Dady."
Shiga cikin falon su kai tare ai ko su ka tarar da Mother da Dady zaune su na kallon TV.
Mother na ganin Raiyna Idonta ya cika da hawaye ta ma kasa amsa gaisuwar kawai ganin Yar ta JAWAHIR ta ke a indonta, ba ta San lokacin da kuka ya kubuce ma ta ba ta shige daki da sauri.
Dady ne ya yi saurin bin ta domin nasan dalilin kukan na ta.
, "Haba Zainab a lokacin da ki ka rasata ma ki ka yi juriya ba re yanzu? Ki yi tawakkali ki mikawa Allah lamuranki domin ya na tare da mu."cewar Dady kenan
Da kyar Dady ya yi kokarin shawo kan Mother.
JAMEEL Kuwa ya ma ka sa shiga cikin gidan Ummansa kawai Jan motarsa ya yi na nufi office.
Tunda ya je Banda rawar kai ba abin da SOFEE ke ma sa hantararta ya ke Amman tana basarwa kamar ba da ita ya ke ba, kaman kara zigata ya ke Dan salon shishshige ma sa ma ta ke karawa.
Yau da huri ya tashi gashi daman ba ya jin dadin jikinsa Dan haka gida kawai ya huce.
Ya na isa Fatima ta ji alamun karar motarsa ai ko ta fito falo da mukaman yakinta ta tsaya......
_Shin Soyayyar da ake nunawa littafaina da gaske ko, kuwa dadin bakine? Zan gane ta hanyar siyan wannan novel mai daraja afarashi mai sauki 200 ma su tura wa ta account_ _0097524644_ _Nafisa sani Access (Diamond) bank, ko kuma katin waya ta wannan number *** sannan ayi scrinshot domin turomin da sheda sai in suburbudaki a group, karki bari abaki labari da cin haram gwanda kici gumin ki ya fi kwanciyar hankali duniya da Lahira_
Urs Xayyeesherth [9/5, 6:02 AM] Xayyeesherthul-Humaerathā¤ļø: ā¢ā¢ā¢ā¢ā¢ _*JAMEEL*_ā¢ā¢ā¢ā¢ā¢
_{Nafseen}_
_PAID BOOK_
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION.*
________________________________________________
_We Are Here To Educate, Motivate And Entertain Our Readers._
________________________________________________ _A cikin kashi Dari na wannan labarin, 70% kirkirarre ne Wanda 30% ko ya kasance na gaskiya._
_*LABARI DA RUBUTAWA.*_āļø
_*Aisha Mohammed Sani (Xayyeesherth)*_
*_LAST FREE PAGE -9/10_*
__________________________________________________________
Da Sallamarsa ya shigo cikin kasaita, ko Amsawa ba tai ba taja wani dogon tsaki kamar yadda shima ya sa ba ma ta.
Ko kallon inda ta ke bai yi ba zai shige abinsa, da sauri ta sha gabansa ta na, "Yau kam ba ka isa ba wallahi ai ni ba baiwarka ba ce, haba Dan Allah ai ko gunki a ka ajiye awaje ana gyara ta bare ni Mutum ku ma ma Mace, wannan wani irin rashin adalcine? Muna cikin shekara ta biyu da Aure Amman ko cikakken minti goma muna tare ba mu yi ba, rabon da naga dariyarka har na manta, ni kam wallahi nagaji nafadama nagaji ka sakeni yau ko nabar gidannan na fallasa halin da mu ke ciki kowama yasani."
Ajiyar zuciya kawai JAMEEL ya yi sannan ya kauce ya na kokarin hucewa.
Kara shan gabansa tai tare da rike ma sa wuyan Riga, "Wallahi ni na fadama ka sakeni inje in aure me sona, kai kan ka kasancewa ba wai rasa mijin aure na yi ba, kaddarace da bin iyaye tare da tausayama yasani Aurenka, ina ganin komai zai huce a kankanin lokaci Amman har yanzu shiru, to nagaji kuma bazan iya ba."
JAMEEL ya yi wani Murmushi Wanda zan iya danganta shi da na mugunta ya ce, "Fatima, Fatima,Fatima, sau nawa na kiraki? Wallahi kin fi kowa sani na a yanzu kam Dan haka ki fita sabgar rayuwata, na farko dai ba ni na auroki ba, sannan ba ni na kawoki gidan nan ba, haka kuma ni ban rikye kafarki ba kofa abude ta ke zaki iya fita." Ya karasa maganar tare da nuna ma ta hanyar fita.
Sake shi kawai tai tafara kukan takaici a wajen shi kuwa ko ajikinsa sama ya haura.
Kuka ta ke ba kakkautawa Wanda har sai da ya kai ga ta fara fita a haiyacinta, wani ihu da tayi sai da rikita JAMEEL da ke sama, da sauri ya sauko ya sameta ban da zufa ba abin da ke fita daga jikinta ga hawaye da ke kwararowa daga idanunta.
Da sauri JAMEEL ya kira Musaddam a waya ya sanar ma sa halin da Fatima ke ciki, cikin gaggawa kuwa Musaddam ya Nufo gidan.
JAMEEL ya rikice fanka ya kunna ma ta akai Amman duk da haka gumin nan dai karuwa ya ke har Allah ya sa Musaddam ya iso sannan ya fara ma ta taimakon gaggawa, cikin ikon Allah kuwa a mintina 30 Fatima ta dawo haiyacinta, kan Musaddam yaja JAMEEL waje domin yi ma sa bayani.
, "JAMEEL a Gaskiya ka kai wannan yarinyar makura hakurinta ya Gaza wai shin ka san yanzu Fatima ta kamu da hawan jini kuwa?"cewar Musaddam.
Sa ke baki tare da dafa kai kawai JAMEEL ya yi na jin wannan babban lamari.
Musaddam ya kara da, " Am serious Fatima ta Riga ta kamu da hawan jini Wanda in ba ai takatsantsan ba ina mai tabbatar ma ka da cewa za iya rasata kuma kai ma arasaka tin da ka ki cire damuwa aranka."
JAMEEL ya ce, "Hmm kai ka fi kowa sanin halin da na ke ciki, duniya ta juya min ba ya daga tafiyar JAWAHIR a cikin rayuwata komai ya sauya, a yanzu kawai ina rayuwa ne aduniyar nan ba wai ina jin dadinta ba, aiki ko da kaga ina yi Dan cikan buri tare da alkawarin da na ma JAWAHIR ne, Ni kai na nasan cewa ba na ma Fatima dai-dai to Amman Ku fahimci halin da na ke ciki mana?
Fatima ta yafemin ta gafarceni ni ina ganin sakin na ta kawai zanyi domin ba ma ita ba ba na jin cewa akwai wacce zan iya rayuwa da ita bayan JAWAHIR, farincikina ce, nishadina, tare da walwalar rayuwata."
Musaddam ya ce, "Aa JAMEEL ko kadan ba za ayi hakan ba, za ka so Fatima dole ka koyawa kan ka son fatima ka fara ma ta kallo irin Wanda ka ke ma JAWAHIR ka nuna ma ta so koda zuciyarka ba ta so ahakan zata saba har ka manta da komai, domin ba zai yu ace acikin kunci za ka kare rayuwarka ba wannan bai kamata ba ko kadan, dole ne komai ya sauya."
JAMEEL zai yi magana Kennan sai ga wani kira ya shigo wayarsa, Ogan sa ne Na Office ya ke sanar ma sa da cewa tafiya ta kamasa zuwa *RUGAR DANGI* Domin yin wani bincike game da wasu yan ta adda kuma shi kadai aka zaba.
Su na gama Wayar JAMEEL ya yi wani dogon numfashi tare da fadin, "To ka ga wani rikicin da ya bullo kuma ana wata ga wata tafiya ta kamini gobe da safe zuwa rugar dangi maganar nan ta mu dole mu Bari sai na dawo asan mafaka, yanzu babbar damuwa ita ce Fatima dole anemo mai zama da ita tunda ko da ina nan ni ba wani iya kulawa zan yi da ita ba bare kuma yanzu ni da zanyi tafiya."
Musaddam ya ce, "Wannan ai ba wata matsala ba ni gidansu za mu je adauko kanwarta ina ganin hakan shi ne mafita."
JAMEEL ya ce, "Yauwa ka kawo shawara yanzu kawai muje gidan Dan ka ga ban da ishshen lokaci dole inje office komin dare a bani kundin case din."
Haka kuwa a kayi gidansu Fatima kawai JAMEEL da Musaddam su ka nufa, ya sanar da Momy cewa zai bar gari gashi kuma Fatima ba ta jin dadi Dan haka suke Neman alfarma da Maryam ta je ta tayata zama.
Ba karamin murna Momy tai ba na jin cewa Fatima ba lafiya atunaninta cewa ai 'yarta ta samu rabone, jiki na rawa tasa Maryam ta shirya domin ta fi su JAMEEL.
Ba su wani tsaya ba ko Maryam ta kintsa sannan su ka ajiyeta wajen Auntynta Fatima sannan Musaddam ya tafi shi ko JAMEEL ya koma office.
Da shigarsa Oga ya ma sa bayanin komai game da wa innan yan ta'addan sannan ya ba sa kundin, babbar matsalar ita ce bai San takamaimai inda zai same su ba.
Washe gari kuwa da asussuba ya shirya domin nufar RUGAR DANGI ya na fito ya nufi bangaren Fatima ba karamin Mamaki tai ba ganin sa wai adakinta domin ita kam tunda tazo gidan ko kofar dankita ba ta, ta ba gani ya taka ba.
Da Sallamarsa ya shiga, ta gaishesa ya amsa da murmushi Wanda shima ya kara bata wani mamakin, Durkusa gareta ya yi ya na fadin, "Ki yafemin Fatima, Yau zan bar garin nan kuma INA ji ajikina cewa akwai wani boyayyen lamari da ke shirin faruwa da ni, Dan Allah ki yafemin duk abin da nai mi ki."
Sake ba ki kawai FATIMA tai ta na kallon sa.
Ya rikwo hannunta tare da fadin, "Please ba na so intafi kina fushi da ni ban San ko zan dawo ba ko bazan dawo ba, ki yafemin dukkan abin da na mi ki nasan ban kyauta ba Amman ke ma kinsan dalilin hakan."
Murmushi Fatima ta yi ta ce, "Alhamdulillah tun da har ka fahimci cewa ba dai-dai ka ke ba naji dadin hakan Amman ina so kamin alkawarin cewa Inka dawo komai zai sauya za ka rumgumi kadarar rayuwarka wannan shine kawai babban matsalata sannan Ina mai ba ka hakuri game da abin da nama jiya kamin afwan nima Sharrin zuciyane but I promise it can't be Happen again."
JAMEEL ya kalli agogon hannunsa ya ce, "Oh 6:40 kuma 7 ya kamata infara tafiya, karki damu insha Allah komai zai yi dai-dai ban mi ki alkawari ba Amman zan yi iyaka gwarwadon iyawata wajen sauke mi ki hakkinki da komai ma."
Ta shi ya yi zai fita itama ta mikye, zaunar da ita ya yi ya na murmushi ya ce, "JAWAHIR ke ba ki jin ma...
Kawai sai ya tuna Fatima ce fa ba JAWAHIR ba.
Kawar da kan sa kawai ya yi ya ce, " kinga ba ki da lafiya ki zauna ni na tafi."
Ya fice da sauri domin maganar da ya ke ma ta na dole Amman ba da son ransa ba.
Ya na fita ya nufi gidan Umma da Abbansa ya mu su sallama su kai ta ma sa addu'o'i sannan ya shiga gidan Mother ita ma da Daddy ba abarsu abaya ba Addu'o'i su ka dunga yi mai tare da sa ma sa albarka da fatan alkairy.
Daga nan kuwa JAMEEL ya dauki hanyar *RUGAR DANGI* gaba daya jikinsa asanyaye domin ya na ji cewa akwai wani babban boyayyen al'amari da zai iya fuskanta a wannan tafiyar.
Tafiya ya ke ban da Karatun Al'Qur'ani ba abin da ke tashi cikin motar.
Chan dai tafiya ta fara nisa ya fara isa ga RUGAR dangi.
Gabansa ne ya fara faduwa, kwakwalwarsa tafara juyawa, Birkin Motar ficewa ya yi, ya kasa controlling din ta sai da taje gaban wani dutse kan motar ta tsaya ya yin shikuma ya kifa kan sa ba motsi ba alamar motsi.
***********Farinciki ya zagaye zuciyar Fatima Fal domin gani ta ke kam a yanzu JAMEEL ya zama na ta, mokaciyarsu ce Zainab ta shigo gidan.
"Fatima yau wani irin farinciki ki ke ciki haka? Ban ta ba ganin kina dariya kamar yau ba, ke da kullum ki ke cikin tunani da kuka?" Cewar Zainab.
Fatima tai Murmushi ta ce, "Matsolinane su ka zo karshe, Wanda yau Zan ba ki labarin JAWAHIR da ta kasance hasken rayuwar mijina da ma mu baki daya, kin sha Tambaya ta ina fada mi ki cewa lokaci bai yi ba to yau lokacin ya yi Dan nasan ba ke kadai ba ce me son sanin wacece JAWAHIR, duk da kasancewar ko da zamu hini mu kwana bazan iya gama baki labarin Soyayyar JAMEEL (Nafseen) da KHADIJA (Jawahir) ba, Rayuwar su, rayuwace me cike da al'ajabi, tsantsar so, kulawa,tausayi tare da kaunar juna, A takaice dai JAWAHIR 'ya ce Wadda duk iyayen kwarai ke son kasancewa 'Diya agaresu, haka kuma ko wani namiji na fatan samun ma ta kamarta cike da alfahari, duk da kasancewar karamar yarinyace Amman ta na da baiwar da ta ninka wa su ma su shekarun."
Zainab ta ce, "Oh Ni ko Fatima na zaku mu shiga cikin labarin Dan da alama ba iyaka ji zan ba zan iya daukan darasin rayuwa, Dan Allah ki fara."
Fatima ta ce, "Ai komai ma za ki koya domin labarin ba inda ya bari mu shiga daga ciki."
*****WAIWAYE ASALIN GUNDARIN LABARIN.
Fatima ta ce, "Kan komai ya kamata in fada mi ki wacece JAWAHIR sannan wanene JAMEEL."
JAWAHIR.....
_*Yanzu a ka fara, kar ki sake a baki labari naira Dari biyun ki ta biya mi ki biya mi ki bukata cikin sauki da kwanciyar hankali*_
_Aisha Mohammed Sani (Xayyeesherth)_
_*Shin ku na Sane da marubuciyar nan da ta nishadantar da Ku game da fadakar da Ku acikin littafanta? BABU RUWAN SO, littafi mai cike da nuna da illa ga ma su daukan Soyayya ba komai ba face bata lokaci, tare da Littafin nan da yayi fice wajen mutane wato KUCHAKAR KISHIYA, Labarin ban dariya, Soyayya,tausayi tare da nadamar rayuwa, ha ka kuma ba ta Gaza ba ta kawo mu Ku WASA DA SO, littafin da ke nuni game da illar wasa da soyayya, tausayawa tare da tunatarwa,Sannan kuma AZZAWAJUL-MUKADDAR (Auren kaddara) ke daga jin sunan kin San cewa za a sha fama domin littafi ne Wanda ya kunshi fadakarwa ta mussaman game da rayuwar Aure da ma kan Aure, yanzu ma ina nan Tare mu Ku da wani kayataccen Littafin mai suna JAMEEL (Nafseen) labarine mai cike da tausayi, tsantsar so,kulawa,Rudani, fadakarwa,Sadaukarwa tare da nishadantarwa, Naira Dari biyun ki ta biya miki bukata cikin sauki, kar ki bari ayi ba ke ma za hanzarto domin fara biyan na ki.*_
_Shin Soyayyar da ake nunawa littafaina da gaske ko, kuwa dadin bakine? Zan gane ta hanyar siyan wannan novel mai daraja afarashi mai sauki 200 ma su tura wa ta account_ _0097524644_ _Nafisa sani Access (Diamond) bank, ko kuma katin waya ta wannan number *** sannan ayi scrinshot domin turomin da sheda sai in suburbudaki a group, karki bari abaki labari da cin haram gwanda kici gumin ki ya fi kwanciyar hankali duniya da Lahira_
_Urs Xayyeesherth_