Chapter 14:RDBG
RAUNIN DA BA A GANI
Meefat ink ✍️ writers
Fina ce ta amsa da “kwarai ma kuwa nina jikintama nakeso” murmushi ruhy tayi tace “ai nariga nadauki wannan fina” “ke wace irin y'ar kasuwace, ai sai kinbari costumers sun gama zaba tukun kidauki wanda ya rage” cewar teemah dariya ruhy tayi daidai inda take duba agogon hannunta tace “kai har 1 yayi, zanje daukan huda” “ok bari mugama zaban abayan sai muyi dropping dinki a school din nasu” “toh kuzaba da wuri” sashen sabon design na abayan suka je suka fara zaba kowacce tadauki colourn da takeso yayinda itama tasauya kayan jikinnata, bayan sun gama tasaka musu a leda suka fita, ruhy kuma tarufe shop din itama tanufi motar.
Meenat dake falfala gudu akan titine tace “ruhy nikam naturamiki kudin ankona dana abayan” “okk toh nama manta wayar a shago wlhy"cewar ruhy sai teemah tace “ai saurinda kikene” itama sai ta tura nata kudin batareda tafadaba, haulart ma tace “nima natura nawa, murmushi ruhy tayi tareda cemusu “toh nagode dayimin ciniki” safina kuma tace “nikam cash zan kawo miki school gobe” “toh Allah yakaimu” sai farida tabude jakanta tacire bounch na 500 guda biyu tamikawa ruhy, karba tayi tareda yiwa faridan murmushi, itama tamayar mata. Parking motar suka yi adaidai entrance din makarantar, sai sukayi mata sallama suka wuce. Shigowarta kenan ta hango huda goye da school bag dinta da lunch box, aiko tana ganin ruhy tazo da gudu ta rungumeta “adda kinsan me, yau ko, head masternmu yayi selecting wadanda za'a saka a competition daza ayi kuma hardani” “haba dai, toh sai kiyi kokari kizo first kinji” “toh adda”, napep suka tara sai ya saukesu a bakin shop dinta, bayan sun shiga sai taceda huda tana zuwa, sai taje fridge tadauko mata ruwa tabata tasha sannan tace “rufe idonki”bayan huda ta rufe idon sai tadauko abayan sannan tace tabude, tsalle huda tafara tana karbar kayan tareda rungumar yayartata, dan tana mugun son abaya “bara na gwada adda” “a'a kibari sai munje gida kinyi wanka tukunna ko, kazama kawai” tafada tana dungurin kanta “ai wlhy ni yar gayuce adda” cewar huda dariya ruhy tayi tana daukan bag dinta da lunch box sai tace “yanzu dai tashi muwuce gida uwar surutu dama natsaya daukan kayanki da wayatane” “adda wlhy kidaina barin wayarki a shop wataran za'a iya sacewa” sosai tabawa ruhy dariya tace “toh naji talkative ke yanzu duk abubuwanda suke shop dinnan masu tsada bazaa sace ba sai wayata” “to ai adda abunda yasa bazasu saceba indai suka ce zasu fita dasu dole sai an kamasu shiyasa zasu dauki wayar sai susa a aljihu sugudu” tsayawa ruhaina tayi tana kallon autan cikin mamakin surutunta da wayonta. Yarinyar bazata wuce 6-7 yrs ba, farace sosai irin fararen asalin fulani ga gashi masha Allah dan tafi yayartata haske sosai, batada wata rama kuma batada wani kibar azo agani.
Ammie ce zaune kamar kullum tana faman tunanin da yazame mata jiki aduk sanda yarannata basanan, tunanin yar uwarta guda daya tilo take, ina tashiga, dan yanzu tananeman 1 month kenan da batarta kuma tun bayanda taji lbr daga wajen mijinta tanemi saki wanda har abun yasoga kaisu koto, toh ba'a karajin wani labarin inda takeba. “ammie ammie” firgigit tadawu hayyacinta alokacinda ta jiyo muryar huda tana kwala mata kira tundaga kofa, share hawayenta tayi ta gyara fuskarta sabida bataso tabar wani alama da zai nunawa ruhy cewar tana cikin damuwa, sai ga huda tashigo da gudu tana cewa.