CHAPTER [52
Nawaila ye tsaye yana dakon fitowansu,imbanda faɗuwa ba abinda gabanshi yakeyi.
Abby ne yaƙariso inda yake,kallo ɗaya zakaima fuskanshi ka shaida tashin hankalin dayake ciki.
"Ina yake?"
Abby yatambaya yana tsareshi da idanunshi da har sun sauya kala.
Da hannu Nawaila yemai nunida yana ciki.
Jingina bayanshi yayi dagaru,zuciyanshi na tsalle aƙirjinshi,wani irin tashin hankali yakeji aranshi,ko lokacinda yarasa mahaifanshi bai tinanin yashiga wannan halinba.
Sunanan atsaye likitan yafito tareda sauran ma'aikatan lafiyan,
dasauri suka nufeshi suna tambayanshi,
Doctor yasauke numfashi yana cewa,
"Alh.muje office mui magana"
Bamusu Abby yabishi,Nawaila yashiga ɗakin.
Akwance yake akan gadon,ahankali yake numfashi tacikin oxygen ɗin da aka samai,fuskanshi ye fayau seya ƙara haske.
Zama yayi abakin gadon yana ƙara kafeshi da ido,kallonshi yakeyi sosai,yana addu'an ubangiji yabashi sauƙi.
Sosai ye zurfi 'a tinani,har Abby yashigo besaniba,sedayaga tsayuwanshi 'a gabanshi,fuskanshi cike phall da damuwa.
"Me doctorn yace"
Nawaila yatambaya yana kallon fuskan Abby.
Abby yaɗaga kanshi sama cikin ƙoƙarin dakatarda hawayen da suke san zubomai,sedaya yatabbarda inya buɗe bakinshi baze fashe da kukaba sannan yafara magana,
"Yace jininshine yahau don ayanzu vp ɗinshi yakai 300,"
"Mekenan hakan ke nufi"?
Abby ye shiru yana kokawa da sauran kalaman,saboda ɗacinsu,yanajin lokacinda suke ƙonamai harshe asanda yafesar dasu ga Nawaila.
"Hakan na nufin yana gabda kamuwa da ci..won zu..ci..ya"
Yaƙarke maga nan ararrabe,ƙwallanda suka cikomai idanu na gangarowa saman fuskanshi.
*OMAR*
Silalewa yayi yakwanta akan carpet ɗin dake tsakar wurin,idanunshi alumshe numfashin shi nafita ahankali.
Zuwa wannan lokacin zuciyanshi taƙame,jiyakeyi kaman 'ana zaremai rai,wani abun yafi gaban faɗi ko misaltawa,
Ubangijinda ya halicce shine kaɗai yasan abinda yakeji.
Turo ƙofanda akayi be sanyashi yaɗaga kaiba,balle yakalla,yanajin yanda tazauna akusa dashi,
tukun muryanta tafito ɗaukeda yanayi maban banta,
"Don Allah kadaure kasha"
Kanshi dayemai nauyi yajuya hakan yabashi daman kallon fuskanta daye jajir na kuka da damuwan datake ciki tun lokacinda abunnan yafaru take kuka,harsu kaje babban gida,yanzuma da suka dawonan yanada tabbacin kukan tacigada yi.
Tiririnda yake dukan fuskanshi yasanyashi kallon hannunta,cup ne ɗaukeda tea,yaɗan yamutsa fuska tinanin sha kawai amai yake shirin sanyashi,
Bece komaiba yasa hannunshi yaɗauke cup ɗin dake acikin hannunta,yaɗorashi akan coffee table,yanajin kallonda takemai ajikinshi,
Aikam yanajuyowa idanunshi suka faɗa cikinnata,baki tabuɗe zatai magana,yaɗora hannunshi asaman bakinnata yana jijjigamata kanshi,dayake jinshi kaman zetar watse.
Sabbin hawayene suka gangaro saman fuskanta,
Omar yasa hannu yasharemata,da idanunshi yake roƙonta data daina kukannan haka,
Wani irin gunjin kukane yatasomata sekawai takife kanta aƙirjinshi tana sakin kuka mesauti,
kuka takeyi sosai,numfashinta har tsatstsayawa yake yalumshe idanunshi yanajin yanda jikinta ke jijjigasu suduka,
Hannayensa duka biyun yasa yariƙe ta yana bubbuga bayanta ahankali alaman lallashi.
Ahaka wani wahaltaccen bacci yaɗauketa,sekawai yagyara mata kwanciya ajikinshi,yana kallon kyakkyawan fuskanta,ahaka har gari hawaye.
@@@
Tray ɗinda ke hannunta tadire agabanshi,taname zama sosai yanda fuskokinsu ke fuskantan na juna.
Spoon tasa taɗibo tea ɗin dake cikin cup ɗin takai bakinshi,don tasan intace yasha ba shaa zeyiba,kuma tun jiya da safe rabon shida yasama cikinshi wani abu.
Hannunshi yasa yariƙe hannunta yana kallonta da rinannun idanunshi,
Zafinda taji yana ratsa fatanta yasanyata ajiye cup ɗin agefe tana kai hannunta saman fuskanshi.
"Subhanallah"!
Tafaɗi da disashshiyar muryanta dake bayyanarda damuwanta agareshi.
"Bakada lafiya,yakamata kaga likita yanzunnan."
"Bana buƙatan ganin wani likita"
Yafaɗi muryanshi can ƙasan maƙoshi,ita kanta bata jishi sosaiba,sedata kalli fuskanshi daye kaman na yaro meshirin ɓallewa da rigima.
Batasake cewa dashi komaiba tamiƙe tabar mai ɗakin,besan yanda akayiba se sallamanta dayaji taredana doctor Naim,wanda yakasance likitan gidanshi tun sanda yadawo.
Kallonta yayi amma seta ɗauke kanta,bayada yanda zeyi,hakanan yatsaya,yemai 'alluran dabesan adadinsuba.
Sannan yahau kan gado,yasamai ƙarin ruwa,beyi kyakkyawan mintina gomaba bacci yaɗukeshi.
Jameela takoma gefenshi tazauna,zuciyanta cike phall da tausayinshi,
Jitakeyi inama tanada halin ɗaukemai abinda yakeji,da tanada yanda zatayi daba abinda zehanata musanya zuciyanshi da nata don kawai yasamu sauƙi.
Doctor Naim dayagama haɗa kayan aikinshi yakalli jameela yace
"Idannaje zan aikoda magungunan sha akawomai.
Sannan daya farka abashi abinci saboda akwai allurorin cin abinci danaimai."
Jameela ta amsada
"to doctor amma wani kalan abinci za'abashi"?
"Duk kalan daya keso"
Kai tajin jinamai alaman tafahimta,
Yana fita tajawo duvet tarufeshi ganin kaman yanajin sanyi,
Sedata fara sumbatan goshinshi sannan tafice daga ɗakin,
Tanajin soyayyanshi naratsa ko wani kafa najikinta.
Kai tsaye kitchen tanufa don tagir kamai wani abu,kar yatashi bata gamaba.
Tana kammalawa tasake acikin saitin plastic masu kyau dasu,
Tajerasu akan coffee table ɗin dake bedroom dinsu,
Bathroom tashiga tawatsa ruwa,tana cikin sanya kaya taga yamotsa,dasaurin ta taƙarisa kanshi tanamai sannu.
Kallonta yayi da lumsassun idanunshi,tausayin tane yakamashi,ganin yanda duk tadamu,aranshi yakejin yakamata yaɓoye damuwanshi ko don ita.
Masu karatu kuya hakuri mutsaya anan semun hadu a chapter 53
Dafatan dai labarin yakayatar daku,wannan littafin gaba dayanshi kyautane agareku masoya,kudai kui min comnent,kununamin reaction dinku,kui min sharing a group group naku
Taku Hindatu Auwal
Se anjima.....
*ZAREN KADDARA*
*حبلاالقدر
®By Hindatu Auwal
*HIKAYA WRITERS ASSOCIATION*
ZAKUIYA SAMUN WANNAN LITTAFIN
FACE BOOK PAGE:@Hindatu Auwal Hausa Novels
WhatsApp:
AREWA PEN:Hindatu Auwal
PHONE NUMBER:***
__________________________________