AZZAWAJUL-MUKADDAR

PAGE 1

by @xayyeesherthulhumaerath

____________________________________________________________________________

"Wallahi sai ka saketa yanzun nan bazan yarda na fadama ni dai bana son yarinyar nan" cewar Wata Dattijo kennan tana ta kumfar baki.

Mutanen ciki agidan Fam anata shagalin biki Amman tun daga shigowar matar nan komai ya watse, Amaryar ma da suke daukan hotuna da ango sunyi sumar tsaye.

Kuka kawai Faruq ya ke domin bakin ciki ya rasa abin yi bare kuma abin fada.

Cigaba da jawabi wannan Tsohuwar tayi tana, "Na fadama wallahi sai ka saketa ko na tsine ma, haba ni na taba ganin naci irin wannan kuwa?"

Dukusawa kasa Faruq ya yi yana fadin, "Dan Allah hajiya kimin rai Wallahi ina son Sakina bazan iya rayuwa ba in babu ita, ki taimaka ki barni da ita."

Tsawa ta daka ma sa tare da fadin, "Wallahi Wallahi ba fashi sai ka saketa ai ga matar ka chan agida,wato kai bakason zabina sai zabin kanka to wallahi daga kai har wa inda suka asirce kan sunyi kadan."

Tuni gida yakaure da kuke kuke, yan uwa da abokan arziki, tun ba kanwar Sakina ba da tafi kowa zubda kwalla.

Sakina kuwa bin yan uwanta take tana basu hakuri ita da za abawa amman ita ke basu domin kuwa ita kam zuciyarta akune take kukan zuci da kuncin zuci kawai ta ke.

Yayunta maza ne suka shigo domin jin hayaniyar da suke tundaga waje.

Yah Usman na zuwa yace, "Ance ka saketa ana dolene?, mu ma fa muna sonta wannan wulakancin naku ya zo karshe ka saketa kawai kowa ya huta."

"Yaya dan Allah kuyi hakuri ina son Sakina kar ku rabani da ita."

Hajiya dai ta dage sai faruq ya saki, Sakina awannan lokacin anfi awa biyu ana abu daya har sai da Baban Sakina ya shigo.

"Haba nagaji da wannan masifa indai ina raye daga yau ba kai ba Sakina kuma kabi umarnin mahaifiyarka kowa ma ya huta."Cewar Baba.

"Faruq na fadama kasaketa ko na tsine ma."Hajiya ta fada tana karkada kai.

Faruq na kuka yana fadin, "SAKINA NA SAKEKI NA SAKEKI SAKI DAYA."

Gida ya kara kaurewa banda tashin aljanu da sume sume ba abinda ake amman abu mafi mamaki shine Sakina ko ajikinta ba ko alamar hawaye bin yan uwanta take tana basu hakuri tare da fadin Wannan Shine _Azzawajul-Mukaddar dina (Auren kaddara)_ Ku dai na kuka kunji."

Hajiya na ganin danta ya cika aikin da take bukata fuuu tabar gidan ita da yan koranta.

Faruq kuwa sai da Yayun Sakina suka fita dashi ta karfi domin ya ki barin gidan.

Gaba daya yan anguwa duk an fito.

Abangaren Sakina kuwa zaune ta ke banda tunanin duniyar nan ba abinda take, batasan me tayiwa mahaifiyar Faruq ba ta tsaneta haka.

*zan cigaba amman nuna sonku ga labarin shi zai ban karfin gwiwar cigaba ,,comments nd share pls*

*_Urs Xayyeesherth_* [11/08 à 00:10] Shalelen Mamata🥳🥳: ***

*AZZAWAJUL-MUKADDAR* *الزواج المقدر*

_(Auren kaddara)_

_A True Life Story_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

______________________________________ _We Are Here To Educate,Motivate And Entertain Our Readers_ ______________________________________

_*LABARI/RABUTAWA*_✍️ ⬇️ _*Aisha Mohammed Sani*_ _*(Xayyeesherth)*_

_Wannan labarin gaskiya ne mai cike da tausayi tare da sarkakiya,ban yarda achanjamin shi ta ko wace siga ba, domin kuwa da yarda wadda hakan ya faru da ita nake rubutun_