PAGE 2-3
__________________________________________________________________________
*Gaskiya naji dadin yadda littafin nan ya samu karfuwa gareku ina yin ku irin sose dinnan 😘😘*
Nasan cewa ma su karatu zasu so suji shin wacece Sakina sannan wanene Faruq
Dafarko dai Faruq 'Da ne ga Marigayi Alhaji Yusuf tare da Mahaifiyar sa Hajiya Amina wadda ta ke yar asalin Niger ce Almajiranci yakai Alhaji Yusuf Ya Auro ta sannan suka dawo mahaifarsa Bauchi inda har su ka haifi Faruq tare kannan sa guda biyu Zainab da Hamza, Azahirin Gaskiya Faruq saurayi ne kyakkyawa mai ji da kan sa domin kamanin Dangin Mamansa ya yo fari gal ga hanci, sannan yagama karatun sa yanzu yana kasuwanci ne.
Abangaren Sakina kuwa 'Ya ce ga Alhaji Sulaiman tare da Mahaifiyar ta Hajiya Maryam Tana da Yayu maza guda biyu, Auwal, Da Aliyu
Sannan kannanta Mata Maryam da Khadija, Sakina kyakkyawa ce ajin farko ba wanda zai ganta bai kyasa ba, zan iya cewa tsabar soyayya tsakaninta da Faruq har kama suke abun ka da fararen mutane.
_Soyayyace mai karfi tsakanin Faruq da Sakina dan zan iya danganasu da Majnon nd Laila, soyayyarsu ta mussamance kamar yadda suma suke na mussaman_
Abu daya ke wahalar da Faruq da Sakina , Mahaifiyar Faruq wadda batason Sa da Sakina.
*WAIWAYE______________*
Yar Budurwa na Hango tare da wani saurayi tun daga nesa zaka fahimci cewa suna cikin nishadi irin ta masoya.
Faruq ne ya ce da Sakina, "Ni fa Agaskiya bazan iya jiran har sai kin kammala karatun nan naki ba kawai ki bani dama in fito ayi Auren mun nan kowa ma ya huta."
Murmushi sakina tayi tare da fadin, "Haba Dan Allah Hubby yaushe ma na fara makarantar da har zan ce da su na zan ajiye."
Tuni Faruq ya murtuke fuska tare da fadin, "Kennan karatu ya fi mi ki ni ko sakina? Daman ni ba kowa ba ne gareki? yanzu kinfi son karatu akai na."
Tambayoyi Faruq ya cigaba da jerowa Sakina, duk hanyoyin da zai bi dan ganin ya watsar da maganar makarantar ta kawai ya ke.
Tun Sakina na basa hakuri har sai da yasa ta aminta taji maganar makaranta ta fita mata akai.
"Shikennan Hubby zan sanar da Baba yau inna koma gida insha Allah sannan ka turo." Cewar Sakina kennan.
Da Sauri Faruq ya ce, "Yauwa Hubbyna shi yasa kullum na ke kara son ki, domin ke tadabance cikin mata,in ana maganar mace ta gari aka sameki an gama."
Mumrmushi kawai Sakin tayi tare da da fadin, "Byee byeee, zan shiga gida kaga dare ya fara yi, zanyi kewarka,kasani cewa ina son ka kuma zan cigaba da son ka har bayan raina."
Faruq ya ce, "Fatana da burina a kullum bai huce ace naga ranar da zan mallakeki matsayin mata ba, nima ina son ki Hubbyna mukwana lafiya."
Tafiya yayi tare da juyowa yana ma ta byeebyee ita ma tana ma sa har sai da ya shiga motarsa sannan ta shige gida.
Sakina na shiga gida kuwa ta tarar da kowa na falo ana kallo.
Durkusawa tai akasa kowa ya ganta dai yasan da magana abakin ta.
Mama ce ta ce, "Sakina kalau dai."
wasa da hanunta tafara sannan ta fara da cewa, "Daman, daman ina so ne na ajiye karatun Diploma ma ne?"
Dasauri yayan ta ya tashi tsaye tare da fadin, ",Whatt! ki na da lafiya kuwa Sakina? .
Araunanane ta ce, "Daman Faruq ne ya ce wai zai turo."
Tsabar takaici sai da Yaya Haidar ya kusa dukan Sakina Babane ya dakatar da shi.
Baba ya ce, "Sakina kennan Dai Maganar kawai Aure ki ke so?"
kai asunkuye dai bata amsa ba amman alama ta nuna hakan.
Baba yakara da cewa, "Shikennan Allah ya kawo su, daman tun farko ai bani na nace kiyi karatun ba raa'ayin ki ne."
Yaya Haidar ya ce, "Haba Baba ya za ace wai ana biyewa yaran nan ne suna abinda suke so."
Baba ya dakatar dashi tare da fadin, "Bakomai ai Auren na ta shine ma fi alkairy."
Dakyar dai Baba ya samu damar dakatar da Yaya Haidar Amman duk da haka bai aminta da mgnr Auren ba dai.
Tun daga ranar Sakina tabar zuwa makaranta a ka koma ta hidimar biki duk da cewa dangin Faruq din ma ba su zo ba.
Acikin kwanakin nan Faruq yaje garin su Niger gun dangin Maman sa, domin Aure ne yakawo Mamarsa Nigeria.
Shirye-shiryen biki kawai ake ba wasa domin kuwa yau take ranar Auren Sakina da Faruq...
An gama shirya komai tsaf mutane sun taru amasallaci domin daurin Aure,,
Alokacin da aka gama jawabi tare da shirin daura Aure ,,, wakilan Sakina na shirin Amsa kennan ihun wata ma ta ya rikitasu wanda hakan yasa komai ya tsaya chak cewa ta ke, "Wallahi baza adaura auren nan ba, in kun ga andaura to bani aduni........
*Nasan cewa kwakwalwar mutane da yawa za ta juya amman kubini asannu za ku fahimci komai anitse🥰lamarin ne asarkakye*
✍️Urs Xayyeesherth [11/08 à 00:11] Shalelen Mamata🥳🥳: ***
*AZZAWAJUL-MUKADDAR* *الزواج المقدر*
_(Auren kaddara)_
_A True Life Story_
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
______________________________________ _We Are Here To Educate,Motivate And Entertain Our Readers_ ______________________________________
_*LABARI/RABUTAWA*_✍️ ⬇️ _*Aisha Mohammed Sani*_ _*(Xayyeesherth)*_
_Domin samun littafan mu a saukakye shiga shafukan mu kamar haka👇_
*Instagram page* _@zamani_writers_association_
*Youtube channel* _Zamani_writers_association_