AZZAWAJUL-MUKADDAR

PAGE-4

by @xayyeesherthulhumaerath

____________________________________________________________________________

Aduniya,, Hajiyan Faruq ce me wannan kunfar bakin tare da fadin baza adaura ba.....

Faruq ya yi kokarin shawo kan mahaifiyarsa amman ina ba dama domin kuwa kamar kara zuga ta ake.

Ba ta bar wajen ba sai da ta tabbatar komai ya watse anfasa Auren sannan taja danta su kai gida.

Baban Sakina ne ya shiga gida jiki asanyaye yana shiga bai kulawa kowa ba ya nufa dakinsa domin su kan su mutanan gidan suji abinda ya faru wanda kusan ma a idon su akai.

Sakina kuwa zaune ta ke ta rasa meke mata dadi ace wai yau daurin Aurenta amman an fasa.

banda hawaye ba abin da ke futa daga idon kanwar Sakina wadda duk ta fita ahayyacin ta wanda bai sani ba ma zai ce Maryam ce Sakina domin Sakina ta zauna ne kawai wanda azahiri ta nuna ba abinda ke damunta amman cikin zuciyarta kuwa bakin ciki ne aciki fal.

Haka taro ya watse,,,

Sakina da Faruq kullum suna cikin waya banda kuka ba abinda faruq kewa Sakina, maimakon shi ya bata hakuri ita ce ta daure tare da basa hakuri tana lallabasa...

Misalin karfe hudu na yamma Faruq ya zo kofar gate din gidan su Sakina kiranta ya yi awaya asabule ta fito ba tare da ta bari kowa ya gannta ba,, tana fita kennan sai ga ya haidar yayi kicibis da ita da kuma Faruq da gudu Sakina ta shige gida domin tasan halin Yayan na ta daman chan ba son auren ya ke ba, bare kuma an sami matsala, Yaya Haidar fin Faruq ya yi kawai da wani mummnan kallo sannan ya bi Sakina suka shige gida.

Duk da wulakancin da ake ma Faruq amman hakan bai sa ya daina zuwa gidan su Sakina ba, domin kuwa kullum yana gidan tare da roko akan akara basa damar auren Sakina Insha Allah ba matsala.

Yaya Haidar ya ki yarda fur tare da fadin, "Wannan ai rainin hankali tun yanzu uwarsa na wulakanta mu inaga anyi Auren? ni fa ban san wace irin zuciyace da Sakina ba, Shikennan Baba ayi Auren nan amman duk abinda ya biyo baya ita ta jawa kanta."

Haka dai aka cigaba da shirye-shiryen baki batare da Hajiyan Faruq ta sani ba..

Faruq ya shirya tsaf domin zuwa garin su dan ya sanar da dangin Mamansa maganar Auren sa, yana zuwa kan ma ya sanar da su aranar su ka Aura ma sa yar uwarsa domin su daman asali aka'i'dar su sai ka Aure yar kabilar su da fari koda kuwa za ka kara Aure, Haka aka ma Faruq Aure da yar uwarsa SUBAI'ATU, haka ya shirya domin dawowa gida asanyaye akan zai zo yasanar da Mahaifiyarsa kan ya zo ya tafi da amaryar sa.

Haka itama Hajiyan Faruq ta na nan tana shirin Aura ma sa yar kawarsa shirye shiryen biki kawai ta ke tana jiran Dan ta yadawo ta Aura ma sa wadda ta ke so, haka kuma dangin Baban Faruq ma suna na nan ana shirin Biki da Sakina.

*karku man ta an ma Faruq aure agarin su sannan anan Nigeria Maman sa na nan ta na shirin Aura ma sa yar kawarta haka kuma shima da dangin Babansa suna nan suna shirin Auren Sakina kuma duk arana daya za'a daura*

*KARKU BARI KWAKWALWARKU TA RIKICE DOMIN BINA ASANNU SHI ZAI SA KU FAHIMTA ASAUKAKE...*

*YAWAN CMMTS YAWAN TYPING😍*

Urs Xayyeesherth [11/08 à 00:11] Shalelen Mamata🥳🥳: ***

*AZZAWAJUL-MUKADDAR* *الزواج المقدر*

_(Auren kaddara)_

_A True Life Story_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

______________________________________ _We Are Here To Educate,Motivate And Entertain Our Readers_ ______________________________________

_*LABARI/RABUTAWA*_✍️ ⬇️ _*Aisha Mohammed Sani*_ _*(Xayyeesherth)*_

_Domin samun littafan mu a saukakye shiga shafukan mu kamar haka👇_

*Instagram page* _@zamani_writers_association_

*Youtube channel* _Zamani_writers_association_