AZZAWAJUL-MUKADDAR

PAGE-5

by @xayyeesherthulhumaerath

____________________________________________________________________________

*A min afwan muna fama da rashin wuta ne 🙏*

_*Wannan shafin sadaukarwa ne ga yar uwata gudan jinina SUBAI'ATU SANI MUNKAILA (suby) ki yi yadda kikeso dashi😘ina kewarki a kulamin da die heart dina🤣*_

a ko wani bangare Shiryen baki suke ba na wasa ba, mussaman gidan Su Sakina dan zan iyacewa ba abinda ba suyi ba nakayan fulawa,robobi,buga stikas,kalan,sobeniyas dai nagani afada.

karfe 11:00 na safiyar asabar A ka daura Auren Sakina da Faruq kennan mahaifiyarsa labari ya zo ma ta ita tana nan ta na shirin karfe 2:00 za daura da yar kawarta Safiya.

Tana jin labarin nan bata sarara ba dibi yan koranta harda Maman Safiya suka nufi gidan su Sakina.....

*a pejin farko na sanar da ku abinda yawakana wanda sai da hajiyan faruq tasa aka saki Sakina kan taji dadi yanzu zamu cigaba da tsunduma cikin labarin ku biyoni asannu karku gaza😘😘*

*CIGABAN LABARI.......*

ba fashi kuwa karfe 2 dai-dai aka daura Auren Faruq da Safiya amman ba Ango domin tsabar zazzabi da ya addabi faruq ko daurin auren ma bai iya hallarta ba duk da cewa koda yana da lafiyar ma bai da niyyar zuwa a cewar sa *Ni na ga kaddarar aure*

A haka dai a ka gama shagalin biki adaddafe domin kuwa Ango baya ta amarya.

Ankai amarya Safiya Gidan Faruq wanda daman gidan mace biyu ya gida.

Dakyar Hajiyarsa ta tirsasa shi aka rakasa.

Sakina na zaune ta rikye wayarsa tare da kallon hotunan da sukai na pre-weeding da Faruq din ta azahiri murmushi ta ke amman cikin zuciyarta banda kuna ba abinda ta ke ji.

Misalin sha biyu na dare tana ta fama ta kalla ta kara kalla sai ga kiran Faruq ya shigo, shi kan shi kiran da taga ya shigo murmushi tayi kaman zata kama amman kuma sai ta katse tare ajiye wayar ta juya ma ta baya.

Faruq bai gaji ba yacigaba da kira kusan sau biyar bata dauka ba sai tunani ya zo ma sa ta hanyar yi ma ta text msg..

" _Sakina ta kinsan dai halin da na ke ciki ko? ko da ace kalau na ke bana iya rintsawa batare da naji muryarki ba, bare ace yau da na ke cikin tashin hankali, Sakina ina son ki ina son ki dan Allah karkicemin kin dai na so na ki dau wayata naji muryarki ko zuciyata zata bar kuna."_ kuka Faruq ya ke yana wannan rabutun.

Sakina na jin karar mssg ta mikye tare da janyo wayar ta, duban da zatayi ne yasa jikinta ya yi sanyi domin kuwa ita kan ta tana ma Faruq so ba na wasa ba, hakan yasa bata jira ya kara kira ba tuni ta kirasa tare da fadin, "Hubbynah ka yi hakuri karkasa damuwa aranka kaji wannan itace kaddarar auren mu kuma komai mai hucewa ne, ba na so kana sa damuwa aranka kaji please." murya araunane.

Tuni Faruq ya ji Zuciyarsa tai fari ya ce, "Maddalla da samun mace ta gari kamarki, insha Allah sai na mallake ki mallaka ta har abada, ina son ki Sakina, ina son kyawawan dabi'un ki, kin cika jarumar ma ta da kowani irin namiji zai yi alfahari da ita."

Murmushi Sakina tayi tare da fadin, "Nima ina son ka, byebyee aje gun Amarya."

Kan Faruq ya kara magana tuni ta katse wayar tare da rufe idanunta.

Safiya kuwa taga abin ba yi Faruq na falo kwance akan kujera tunda suka gama waya da Sakina ya zubawa fuskar wayar ido domin hoton Sakina ne akai..

Safiya na zuwa ta fusge wayar tare da fadin, "Wai wannan wani irin iskanci ne? wa ce Amarya aka tabama haka, ka bar ni kamar wata gunki ina ta zaman jiran shigowarka."

Faruq ya ce, "Ya isa haka Safiya ke kan ki kin san ba son ki nake aka aura min ke ba, ki barni naji da damuwata Aure dai gashi anyi kuma kin shigo gidana burinki da na mahaifiyarki ya cika dan haka ki bar ni please."

Mika hannu ya yi zai karbi wayarsa ta bige ma sa hannu tare da fadin, "Wai akan waccer karuwar ka ke wulakantani? da me ta fini."

Kalmar karuwar da Safiya ta kira Sakina da shi ne ya girgiza Faruq bai san lokacin da yadauketa da mari ba fusge wayarsa ya yi tare da shigewa cikin dakin ya rufo kofar.

Tsaye ya bar Safiya jim domin tayi biyu ba bu ya mareta sannan ya shige cikin daki tare da rufo kofa.

Haka kuwa ta kwana a kan kujerar falo tun tana kuka harta gaji tai shiru.

Da asuba Faruq ya fito da alwalarsa tare da nufar massallaci domin salla, Ko kallon inda ta ke bai yi ba bare magana.

Daga masallacin nan ba inda Faruq ya nufa sai kofar gidan su Sakina, tun gari bai yi haske ba har yayi haske yana cikin motarsa banda kallon kofar gidan tare da tunani kala-kala ba abinda ya ke.

Daukan wayarsa yayi tare da kiran Sakina A waya ai ko tana gani ta daga ya ce ma ta yana kofar gate.

Da sauri ta zura hijabi zata fita Maryam ta ce, "Aunty Sakina ina zaki da sassafen nan?"

Sakina ta ce, "Abu zan karba agidan su Hafsa."

Da sauri ta fice tun kan wata tambayar ta biyo baya.

Tana fita ta hango motar Faruq.

Karasawa tayi da murmushin ta.

Tana zuwa Faruq ya fara......

Urs Xayyeesherth [11/08 à 00:11] Shalelen Mamata🥳🥳: *AZZAWAJUL-MUKADDAR* *الزواج المقدر*

_(Auren kaddara)_

_A True Life Story_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

______________________________________ _We Are Here To Educate,Motivate And Entertain Our Readers_ ______________________________________

_*LABARI/RABUTAWA*_✍️ ⬇️ _*Aisha Mohammed Sani*_ _*(Xayyeesherth)*_

_Domin samun littafan mu a saukakye shiga shafukan mu kamar haka👇_

*Instagram page* _@zamani_writers_association_

*Youtube channel* _Zamani_writers_association_