AZZAWAJUL-MUKADDAR

PAGE-6

by @xayyeesherthulhumaerath

____________________________________________________________________________

*SADAUKARWA GAREKI AMINIYA MOM ANNUR😘INA YIN KI IRIN SOSE DINNAN🥰*

******

Kuka

Murmushin da ba ataba rasashi afuskar Sakina shine dai ya bayyana tare da fadin, "Haba Hubby na sai ka ce ba namiji ba karka ba ni kunya ma na."

Faruq ya ce, "Haba Sakina ya bazan yi kuka ba? kina gani fa Hajiya ta dage sai ta rabani da farincikina, na farko ta sa anfasa daurawa wannan kuma andauran ma ba ta barni ba ta sa na sakeki, ga shi ta Aurar min wadda ta ke so, haka ma yan uwanta sun aura min wadda suke so wai duk hakan bai isa ace anbar ni nima nabi zabina ba?" da kuke ya ke maganar tsabar takaici da bacin rai ne zance ko bakin ciki.

Sakina ta ce, " _Hmmm ba mu da wata manufa da ya fi mu bi umarnin iyayen mu bin na gaba bin Allah, indai Allah ya kaddara ni matar ka ce to ba makawa sai munyi aure ko da kuwa za acigaba da rusawa ne dole su gaji su barmu."_

Goge hawayen sa yayi da hankichif din da ke hannunsa tare da fadin, "Nagode Sakina, ki kulamin da kan ki, kinji kishiga gida kar azo agan mu asami matsala."

_"To hubby byebyee miss u."cewar Sakina kan ta shige gida_

Tuni ta shige da saurin ta, shi ko bai tafi alokacin ba sai da ya dan jima yana tunani.

Daga nan ba inda ya huce sai gun aikin Baban su Sakina, bai ma iso ba har sai da ya tsaya ya iso sannan ya gesheshi ba mu su ba bata rai Baba ya amsa.

Faruq na ta kame-kame ya na son yin magana amman ya rasa ta ina zai fara domin ba yau yasaba neman wannan alfarma.

Baba ya fahimta hakan ya sa shi fadin, "FARUQ ka saurareni nasan me ya kawo ka nasan bai huce maganarka da Sakina ba Wadda kuma tun jiya na fadama babu ita, kasa aranka cewa indai kaga kun yi rayuwa da Sakina to Allah ne ya kaddara amman abu mafi mahimmanci shine kawai ka sa aranka ka hakuri kaje ka bi umarnin mahaifiyarka, indai Mata ce ai gashi kana da su har biyu ma ina mai ba ka shawara da ka koyawa kan ka sansu tun kan lokaci ya kurema, ni dai ina son abin da 'ya ta ke so, amman indai ya kai ga wulakanci dole na hakura sannan ita ma na tirsasa ta, ta hakura, daga kai har Sakinan 'ya 'ya ne a guna dan Haka ina mu ku fatan alkairi."

Gaba daya jikin Faruq ya yi sanyi hakan ya Sa shi godiya ga Baba sannan ya tashi da nufin tafiya.

Tun daga ranar Faruq bai kara zuwa gidan su Sakina ba, kasancewa ba jin dadin jikin sa ya ke ba, gaba daya ma ya fita ahaiyyacin sa.

Safiya kuwa ta na nan ban da zubar masifa ba abin da ta ke ma sa duk da kasancewar bai da lafiya amman hakan bai dameta...

Sakina kuwa hakurin ta ya fara gazawa kana ganinta ka ga wadda take cikin wani hali domin duk yanayin ta ya chanja.

Mama na ta kiran ta tazo taci abinci kennan tasowar da zatayi sai ga ta akasa warwas ko motsi batayi numfashin ta ya tsaya.

Gaba daya Mama da Maryam sun rikice kasancewar Baba da Yayunta maza duk ba sa nan, Maryam ce tai saurin kiran Yaya Haidar awaya, ba adau mintina goma ba kuwa sai gashi yadau Sakina suka nufa asibiti.

A na zuwa a ka fara ma ta taimakon gaggawa, Faruq kuwa ya jin Sakina ba lafiya tuni ya ji ciwon shi ya warke kamar bai taba ciwo ba, shiryawa ya yi ya fita domin bin su asibitin, tun da ya je yaga Yaya Haidar ya ka sa karasa domin yasan za a iya samun matsala

Zagayawa ya yi ta windon dakin da take yana tsaye kamar wani mai gadi, ba kowa adakin sai ita kadai tana farfadowa kuwa yana ankare da ita ya ce, "Sakina."

Taji muryar Faruq amman ba ta ga kowa adakin ba.

Azuciyar ta take fadin, "kar fa ace son Faruq har ya fara haukatani."

Kara kiran ta yayi tare da fadin, "Gani nan ta windo."

juyowar da zatai kawai ai ko sai suka hada ido da ita ga kuma Yaya Haidar da su Mama sun shigo.

*Anya kuwa ku na jin dadin labarin nan?😘 gsky ban ga alamar hakan ba*

Urs Xayyeesherth [11/08 à 00:13] Shalelen Mamata🥳🥳: *AZZAWAJUL-MUKADDAR* *الزواج المقدر*

_(Auren kaddara)_

_A True Life Story_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

______________________________________ _We Are Here To Educate,Motivate And Entertain Our Readers_ ______________________________________

_*LABARI/RABUTAWA*_✍️ ⬇️ _*Aisha Mohammed Sani*_ _*(Xayyeesherth)*_

_Domin samun littafan mu a saukakye shiga shafukan mu kamar haka👇_

*Instagram page* _@zamani_writers_association_

*Youtube channel* _Zamani_writers_association_