PAGE-7
________________________________________________________
*Am back🥰ayi min afwan duk kasancewar nasanar tun kan nadakata amman wa su ba su sani ba suna ta tmby, ngd sose da nuna kulawarku gareni❤️*
Faruq na ganin su yalabe agefe ya na jin maganar su har Mama ta ce wa Yaya Haidar suje pamasi ga maganin da a ka rubuto, ai kuwa Faruq na jin fitar su ya zaga ya shige dakin.
Sakina ta ce, "Kar su Mama su shigo fa Hubby in suka gan mu za asami matsala.
Faruq ya ce, "Tun da dai naganki ai ba na gudun duk wani abun da zai faru Ynzu ko anjima. "
Murmushi Sakina tayi tare da fadin, "Ya naga kaman ba ka da lafiyane. "
Janyo kujerar robar da ke gefen sa ya yi tare fadin, "Ki na ganin zan sami lafiya ne bayan an rabani da farincikina?, Sakina ina sonki ina so na rayu da ke rayuwa ta har abada. "
Magana ya ke hawaye na zuba daga idanunsa.
Dafa karfen gadon Sakina ta yi ta dan zauna tare mikawa Faruq hanki tana, "Kai ne farincikin rayuwata a kullum ina fada ko da ba ka gareni, ka goge hawayenka masoyina ina so kasa aranka cewa indai rayuwarmu tare alkairi ne to ba makawa zan kasance mata agareka, ka sawa zuciyarka ruwan sanyi tare da neman mafita ma fi alkairi daga wajen Allah. "
Goge hawayensa ya yi shima ya na murmushi kamar yadda sahibarsa ke yi, "Maddalla da samun Mace ta gari, in na rasaki na yi babbar asara, zan cigaba da hakuri tare da mi ka komai ga Mahallincin mu, ina son ki Sakina ina Alfahari da ke. "Cewar Faruq.
Sakina ta ce, "yauwa jarumina nima ina alfahari da kai kuma ina son ka byee, byee ka tashi ka tafi kar su Mama su dawo. "
Faruq ya tashi yana, "Owk Byee, byee zan dawo amman fa. "
Murmushi kawai Sakina ta bi sa da shi.
Ai kuwa Faruq na fita sai ga Mama da Yaya Haidar.
Faruq ya gaida Mama ta amsa shiko Yaya Haidar kallon da ya ma sa ma ya hanasa iya ka ra magana bare ya geshesa wucewa kawai ya yi.
Sai da Sakina ta yi sati daya asibiti kuma a kullum sai Faruq ya je ko da bai sami shiga ba sai ya tsaya a jikin window.
Rayuwa ta cigaba Sose dai tsakanin Faruq da Sakina karuwa ta ke a kullum, duk da kasance ma su neman Aurenta kara zuwa su ke amman fir ta ki amincewa da su ita dai sai Faruq.
Kullum sai dai suyi waya ko kuma in ta fita ta kirasa su hadu.
Yau ma kamar kullum Sakina ta shirya tsaf domin tafiya shagon ta *(ta na da shagon sai da dogayen riguna na ma ta, gyalulluka hadda ma kananun kaya kasancewar fasa auren da akayi ga shi tavar skul y sa kawai a ka bude ma ta da ta zauna ba abin yi.)*
Tun safe ta fita har lokacin dawowarta ya fara kurewa ba Sakina ba labarin ta, tun yan gida ba su damu hardai a kaga dare ya yi fa shiru.
*Ko me ya faru da Sakina? Ku biyoni a shafi na gaba*
Xayyeesherthul-Humaeran ku ce😘 [11/08 à 00:13] Shalelen Mamata🥳🥳: ***
*AZZAWAJUL-MUKADDAR* *الزواج المقدر*
_(Auren kaddara)_
_A True Life Story_
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
______________________________________ _We Are Here To Educate,Motivate And Entertain Our Readers_ ______________________________________
_*LABARI/RUBUTAWA*_✍️ ⬇️ _*Aisha Mohammed Sani*_ _*(Xayyeesherth)*_
_Domin samun littafan mu a saukakye shiga shafukan mu kamar haka👇_
*Instagram page* _@zamani_writers_association_
*Youtube channel* _Zamani_writers_association_