PAGE-8
________________________________________________________
*HAPPY BIRTHDAY AUNTYNA SHAXEE ALLAH YAKARA TSAWON KWANA DA BASIRAR SUBURBUDO MA NA DAD'ADAN NOVELS🥰INA YIN KI INA ALFAHARI DA KE MY MENTOR🎂🎂🎂🎂*
*WANNAN SHAFIN SADAUKARWANE GAREKI SARAUNIYAR COMMETS DIN XAYYEESHERTH FAN GROUP MAMAN USMAN KI YI YADDA KIKESO DA SHI INA YIN KI IRIN SOSE DINNAN🥰🥰*
Su Mama, Maryam, Yaya Haidar da Baba duk hankalin su y tashi hakan ya sa Yaya Haidar nufan shagon Sakina domin wayarta ma akashe ba ta shiga, ya na zuwa kuwa ya sa'a shagon abude, hakan ya sa shi karasa da sauri.
Abun mamaki Sakina gani zaune Faruq na gefenta su na ta hirarsu ban da dariya ba abinda Faruq ke yi, da ka gansu za ka fahimci cewa masoyane wanda su ke cikin shaukin So.
Wa ta tsawa da Yaya Haidar ya yi ne ya fargar da su domin ba su ma lura da zuwan sa ba.
Tuni Sakina ta mikye.
Daga hannun da Yaya Haidar zai yi aiko sai ya dallawa Faruq mari tare da fadin, "Wai kai wani irin mayye ne? Iye? Mahaifiyarka ta nuna ma ta kiyayya a fili amman ka ki rabuwa da ita? Kai ka na ganin wai akwai wani aurene tsakanin ku nan gaba? To wallahi tun huri kasan inda dare ya ma, ficemin daga shagon nan. "Ya fada tare nuna ma sa kwofa.
Ya dawo kan Sakina, "Ke kuma muje gidan za kiyi bayani, daga yau ma an rufe shagon zan ga ta inda zai na bin ki. "
Ko uffan Faruq bai iya cewa ba ya fice. Domin yasan ko miye ma ya faru Hajiyarsa ce ta ja ma sa.
Yaya Haidar daukan key yayi y rufe shagon sannan y rikye hannun Sakina su ka shiga mota, tun da su ka shiga Yaya Haidar bai kara ce ma ta komai ba har su ka isa.
Suna shiga su Mama su ka fito su na Alhamdullillahi ta rongume Sakina tare da fadin, "Haba Sakina ina ki ka je haka? Duk kin ba mu tsoro mun zata wani abu ne ya faru da ke. "
Jan ta tayi suka shige daki.
Bayan kowa ya zauna ne Yaya Haidar ya ce, "Baba ka ga dai wannan yarinyar ta karbi kaddarar auren ta hannu bibbiyu amman yanzu Faruq na neman hure ma ta kunne kuma ba za mu yarda ba dan haka ni na yanke hukunci kawai in Khadija *(Khadija Yayarsu Sakina ce da ke Aure a Abuja, daga ita sai Sakina tukun na Maryam)* ta zo zata bi ta suje chan abuja domin in ba haka ba akwai matsala."
Baba da Mama sun karbi shawarar Faruq domin kuwa sun san ba wata manufa da ta huce wannan, mussaman Baba da kullum sai Faruq ya je shago ya gallabesa kan abashi dama ta karshe.
Washe gari kuwa sai ga Aunty Khadija ta zo bayan sun gama magana da Baba ne. Ta ce to insha Allah gobe zasu huce domin tana makaranta.
**** Da Sassafi Sakina da Aunty khadija su ka fara shirin tafiya.
Misalin karfe goma dai-dai sun gama shiri tsaf.
Gaba daya jikin Sakina ya mutu domin ita kwata-kwata ba sa son tafiyar nan.
Suna fita ba jimawa suka sami mota.
Bayan sun shiga mota ta tashi daga idon da Sakina za taga Faruq a gaban mot..........
*Cmmts din ku shi ke karawa hannun mu gardin rubutu🥰*
Xayyeeshern ku ce🥰 [11/08 à 00:14] Shalelen Mamata🥳🥳: *AZZAWAJUL-MUKADDAR* *الزواج المقدر*
_(Auren kaddara)_
_A True Life Story_
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
______________________________________ _We Are Here To Educate,Motivate And Entertain Our Readers_ ______________________________________
_*LABARI/RUBUTAWA*_✍️ ⬇️ _*Aisha Mohammed Sani*_ _*(Xayyeesherth)*_
_Domin samun littafan mu a saukakye shiga shafukan mu kamar haka👇_
*Instagram page* _@zamani_writers_association_
*Youtube channel* _Zamani_writers_association_