AZZAWAJUL-MUKADDAR

PAGE-9

by @xayyeesherthulhumaerath

________________________________________________________

*WANNAN SHAFIN SADAUKARWA NE GA YAN GROUP DI NA XAYYEESHERTH FANS GROUP😘😘😘 INA YIN KU IRIN SOSAI DINNAN ACIGABA DA SHARHI MUTANENA*

Mota wani matsakaicin murmushi ta yi tare da kawar da kan ta gefe.

Har su ka isa garin Abuja Aunty ba ta gane Faruq na cikin motar su ba har sai da su ka sauka rikye baki kawai Aunty ta yi ganin Faruq agaban ta ya na gesheta, murmushi kawai ya yi dan ya ga mamaki tsarara afuskar Aunty kara fadi ya yi, "Ina hini Aunty? "

Murmushi ta yi tare da fadin, "Lafiya Romio dan kai kam kaci ace ma Romio ko ince Yayan sa ma. "

Murmushi kawai Faruq ya yi tare da karban jakar hannun su Anty driver ya zo ya dauke so.

Bayan sun shiga gida sun yi sallah an kawo ma Faruq abinci ya ci suma sunci sannan Anty ta ce, "Daman na so na nemaka kan mutawo dan mu yi magana amman ba lokaci to yanzu tun da dai Allah ya kawoka shikennan, Faruq ina so na nemi wannan alfarmar ce daga gareka dan Allah dan Annabi ka rabu da Sakina. "

Daga Faruq har Sakina sai da gaban su ya fadi da jin wannan kalmar da ta fito daga bakin Aunty.

Tuni Sakina ta sunkuyar da kan ta kasa shi ko Faruq ya ka sa cire idon sa daga duban na Aunty.

Ita kuwa cigaba da magana ta yi tana, "Wannan itace mafita agaremu da mu da kai, ba sai an fada ba mun san kana son sakina so kuma na gaskiya amman azahiri auren ku ba mai yuhuwa ba ne ko da anyi ma ba amfani tun da dangin ka ba son ta su ke ba, karka manta fa sau biyu kennan na farkon anzo za adaura aka fasa na biyun kuwa an daura mahaifiyarka ta sa kasake ta. To miye amfanin hakan, dan haka ina rokon ka da ka fita arayuwar Sakina kasan cewa ba dan kowa naje na dauko Sakina ba sai dan kai domin bibbiyartan ma da kake zaka iya ja mana babbar matsala.

Hawayene kawai ke zuba a idanun Faruq, ya ce, "Anty yanzu shikennan kina nufin b ni ba Sakina? Za ta je ta Auri wani ba ni ba?, ni kuma kaddarar Aure na kennan Mata biyu ba wadda nakeso aciki?, Aunty na fahimce kuma na gode, insha Allah zan fita arayuwar Sakina amman hakan ba wai yana nufin nadaina son ta bane, ina son ta kuma zan cigaba da son ta har karshen rayuwata, in dai ina nigeria ba zan iya juran rashin Sakina ba zan bar kasar nan kodan na var sakina tai rayuwa cikin walwala, amman ku sani Sakina ita ce rayuwata. "

Ta shi ya yi yaje gaban Sakina ya durkusa yana, "Ina son ki Sakina duk wanda ya sameki matsayin mata ya dace, ina alfahari da ke, karki manta dani ko da ace kinji mutuwata karkiyi kuka kimin addu'ah. "

Sakina ta kasa dagowa sun hada ido kawai wasa ta ke da yatsun hannunta.

Ta shi Faruq ya yi tare da goge hawayen da ke fuskarsa.

Sannan ya fita

XAYYEESHERTH [11/08 à 00:14] Shalelen Mamata🥳🥳: *AZZAWAJUL-MUKADDAR* *الزواج المقدر*

_(Auren kaddara)_

_A True Life Story_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

______________________________________ _We Are Here To Educate,Motivate And Entertain Our Readers_ ______________________________________

_*LABARI/RUBUTAWA*_✍️ ⬇️ _*Aisha Mohammed Sani*_ _*(Xayyeesherth)*_

_Domin samun littafan mu a saukakye shiga shafukan mu kamar haka👇_

*Instagram page* _@zamani_writers_association_

*Youtube channel* _Zamani_writers_association_