AZZAWAJUL-MUKADDAR

PAGE-11

by @xayyeesherthulhumaerath

________________________________________________________

*AFWAN PLS BIKI MU KE WLH KUKAJINI SHIRU AMMAN YANZU TUNDA AN KAMMALA KOMAI ZAI YI DAI DAI INSHA ALLAH😘😘😘*

Suna gama wayar nan ba inda Faruq ya nufa sai gidan babban malamin da ke anguwar su Sakina.

Ita kuwa Sakina kiran Ibrahim ta yi tare da ma sa albishir cewa ta amince ya turo.

Ba karamin Farinciki Ibrahim ya yi ba da jin hakan, acikin daren kuwa ya sanar da mahaifiyar sa ita ma tai murna sose kasancewar ta san Sakina sose kuma ta na son ta itama.

Ya na zuwa ya sanarwa da malamin duk abin ke faruwa daga farko har karshe.

Faruq ya bukaci da malamin ya shiga maganar domin ma Baban Sakina magana.

Malamin kuwa ya aminshi lamarin hannu bibbiyu hakan ya sa shi kiran sauran malaman da ke anguwar su ka tattauna akan lamari sannan su ka nufi gidan su Sakina har da Faruq din.

Suna zuwa kuwa sun ci sa'a Baba ya fito kennan za shi masallaci,kasancewar lokacin sallah ya ku sa kurewa ya sa su yin maganar atsatsaye. Baba ya ji batun su kasancewar ya na ganin darajar su amatsayin su na malamai ya sa shi fadin cewa zai yi tunani su duba su gani.

Ba ason Ran Faruq ba ya bar gurin domin acewarsa ma shi bai ki adaura auren yanzu ba.

Washe gari************

Da Asuba Baba yatafi masallaci chan kawai sai ga kiran Baba nan awaya kan cewar abawa Yaya Haidar goron Auren Sakina. *kasancewar wancen goron na nan ajiye da a ka fasa auren*.

Mama ta ce, "Oh ina ga Sadaka zai bayar kuma da asubar nan."

kiran Haidar tayi ya dauuka sannan ya nufa masallacin.

Chan sai ga wani kiran ma Mama na amsawa Baba ya ce ma ta Auren Sakina fa za adaura.

"Iyeee auren Sakina kuma?."Abin da Mama ta iya furtawa kennan sai ta ajiye wayar ta nufa dakin su Sakina da Maryam.

"Sakina,Sakina,Maryam ba za ku tashi ba ne?"

Kin motsawa su kai domin barci na kan su.

Mama ta kara cewa, "Ba za Ku tashi ba? to auren Sakina za adaura."

Ai tuni Maryam ta bude kofa.

Mama ta ce, "Jeki masallacin ki jiyo ma na."

Ai ko ba takalmi Maryam ta nufa masallaci da ga zuwan ta kuwa karaf akunnan ta andaura auren Sakina Da Faruq.

Ai da gudu Maryam ta kara komawa gida. Tana zuwa ta sanar da Mama duk da cewa suma sunajin daurin Aure daga gidan.

Sakina kuwa tayi mutuwar tsaye ban da hawaye ba abin da ke fita daga idonta.

Baba na shigowa ta durkuusa gare sa ta na kuka, "Baba ba na son Auren nan, ni nadaina son sa,dan Allah ka ce min ba adaura ba."

Kawai ta fashe da kuka.

Gaba daya Sakina ta rikice ita fa adole ba ta son Faruq. Baba ya ce, "Sakina ai sai dai ki yi hakuri kawai aikin gama ya riga ya gama,ban yi tsammamin zakice Aa ba,ki yi hakuri ki karbi wannan kaddarar ma kamar yadda ki ka karba ta farko."

Ina ai Sakina ba ta san wannan zancen ba ta dage alan fur ba ta son Faruq.

Urs Xayyeesherth [11/08 à 00:14] Shalelen Mamata🥳🥳: *AZZAWAJUL-MUKADDAR* *الزواج المقدر*

_(Auren kaddara)_

_A True Life Story_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

______________________________________ _We Are Here To Educate,Motivate And Entertain Our Readers_ ______________________________________

_*LABARI/RUBUTAWA*_✍️ ⬇️ _*Aisha Mohammed Sani*_ _*(Xayyeesherth)*_

_Domin samun littafan mu a saukakye shiga shafukan mu kamar haka👇_

*Instagram page* _@zamani_writers_association_

*Youtube channel* _Zamani_writers_association_