PAGE-12
________________________________________________________
*WANNAN SHAFIN SADAUKARWANE GAREKI FIRDAUSI NA BAKI SHI KACOKAN KIYI YADDA KIKE SO DA SHI XAYEESHER TA KI CE,,INA YIN KI IRIN SOSE DINNAN😘*
Azahiri dai Sakina ta nu na ba ta son Faruq Amman cikin zuciyar ta kam har yanzu ta na son abun ta.
Shagalin bikin da ba shiri kawai aka fara agidan, ma su zuwa kasuwa nazuwa,ma su gyara kaya na gyarawa,kasancewar duk kayan ta da man su na nan a ajiye sai yan was su kananan abun da ba arasa nema ba.
Sakina kuwa da ka ganta zakasan cewa amaryace domin kuwa ta sha lalle da gyaran jiki na bikin aminiyarta Wanda ba ta San Ashe harda na ta ba.
Sakina ta yi hakuri Amman gaba daya arikice ta ke ta rasa ma me zata fara gani ta ke kaman wasa ne ba auren ta ake ba, ko ince gani ta ke wani Abu na shirin afkuwa kamar yadda aka saba abaya. Faruq kuwa ya na chan ban da washe baki ba abin da ya ke,Safiya kuwa ta kama karamar hauka da jin wai Faruq ya yi Aure.
Ba shiri ta kira Maman ta awaya ta sanar da ita sukayi gidan su Hajiyan Faruq.
Ba sallama suka shige gidan suna huci kamar sabon biredi.
Hajiya ta ce, "Ah Aminiya ke da sirikar ta wa ce?"
Mummunan kallo Mama ta bita da shi Sannan Safiya ta ce, "To munafuka daman yadda mu kai da ke Kennan? Wa to kin yarjewa Dan ki akan ya je ya auro wannan mayyar yarinyar? To wallahi ba Ku isa ba daga ke har Dan na ki."
Hajiya ta rikye baki tana, "Safiya ni kika fadawa magana haka? Aminiya kina jin ta?"
Mama ta CE, "Ai wannan ma kadan ta mi ki dalla chan karamar munafuka kawai ashe daman da abin kika shirya to na fadamiki in sake Fada miki daga ke har Ita Sakinan zaku gayawa aya zaki."
Hajiya kuwa mutuwar tsaye ta yi domin itama yanzu taji labarin auren Faruq Abu mafi mahimmanci da ya ba ta mamaki shine yadda aminiyarta ta juya ma ta baya gashi komai da ya faru duk akam ta ne Dan kawai ta faranta ma ta Faruq ya auri yarta.
Amman yanzu ta nuna ba ta san komai ba.
Maman Safiya kuwa ba inda suka nufa sai wajen BOKA
*A na wata ga wata an gama wani case din fa ga wani sabo fil aleda.*
Hajiya kiran Faruq tai awaya kawai sai ga shi ya zo ba mu su.
Ya na zuwa Hajiya ta ce, "Faruq ka kyauta ka auri Sakina ka bi son ran ka, wannan karam dai banda bakin magana domin kuwa nagano wani babban lamari, ba abinda zan ce ma sai dai Allah ya ma albarka Allah ya sa anyi wannan aure asa'a,kamin alfarma daya a kan Safiya ka yi hakuri nasan kana da hakuurin amman ka kara hakuri nasan halin Safiya da mahaifiyarta, nayi dana sanin hadin auren kuu da tun farko na barka ka bi zabin ka
Sakina na chan tana ta neme nemen kayayyakin ta.
Karfe biyar dai-dai aka zo daukan amarya.
Sakina tayi kukan rabuwa da iyayen ta ba kadan dan da kyar ma aka fitar da ita daga gidan.
Anje kai amarya dai dai lokacin da Safiya ta koma gida.
Zama tai atsarkar gidan tanai wa mutane kallon hadarin kaji.
Su kuwa yan uwan Sakina ba mai kallonta bare shiga harkarta.
Ana kai amarya aka watse kasancewar ba kwana.
Faruq ya shiga gida ya na washe baki kawai sai ga Safiya abakin kofar Sakina.
"Miye ha ka Safiya? bani waje na huce ma na." cewar Faruq.
Safiya kowa cin cingom din ta take tana girgiza kai.
Faruq ya ga abin bq yi tuni ya fige ta ya shige abin sa.
Safiya ta tafi tana masifa domin ba yadda ta iya ya riga ya shige ya kulle kofar.
Da sallama Faruuq ya shiga dakin Sakina.
Kan Sakina durkushe agaban gado.
Ta amsa sallamar asanyaye.
Zai kara magana kennan sai sukaji bugun kofa kamar za acire.
Da huci Faruq ke fadin," wai wacece ne?"
Safiya ta ce, "Ni ce nan wallahi ka zo ka bude ko in balla kofar nan.
Rai abace Faruq ya nufa kofa Yana zuwa.....
Urs Xayyeesherth [11/08 à 00:15] Shalelen Mamata🥳🥳: *AZZAWAJUL-MUKADDAR* *الزواج المقدر*
_(Auren kaddara)_
_A True Life Story_
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
______________________________________ _We Are Here To Educate,Motivate And Entertain Our Readers_ ______________________________________
_*LABARI/RUBUTAWA*_✍️ ⬇️ _*Aisha Mohammed Sani*_ _*(Xayyeesherth)*_
_Domin samun littafan mu a saukakye shiga shafukan mu kamar haka👇_
*Instagram page* _@zamani_writers_association_
*Youtube channel* _Zamani_writers_association_