AZZAWAJUL-MUKADDAR

PAGE-13

by @xayyeesherthulhumaerath

________________________________________________________

*WANNAN FEJIN NA KU NE MASOYAN KWARAI,MMN KHAIRAT,RAHIMA ADAMU,FIRDAUSI,MAMAN USMAN,RUKAYYA FULANI,KUYI YADDA KUKESO DA SHI INA YIN KU OLL❤️* Safiya ta fara kukan munafurci,

Kawai bin ta da kallo Faruq yA yi dan ya ma kasa magana.

A shagwabe ta ce, "Sweet ni wallahi tsoro nakeji bazan iya kwana ni daya adakin ba,ko na zo nan mu kwana please." harda durkusawartA kasa ta na kuka. Faruq ya riko ma ta hannun ta na murna za su shige ciki sai ko ya yi dakin ta da ita.

Ban san me ya ce ma ta ba kawai dai naga fitowarsa ya na murmushi.

Washe gari

Da sassafe Safiya ta tashi ta dafawa su Faruq ruwan wanka tare da yi mu su breakfast.

Abin na ta ya ba Faruq mamaki sosai amman kawai ya basar.

Hajiyan Faruq kuwa da sassaafen nan ta shirya domin zuwa gidan aminiyarta.

Ta na zuwa Maman Safiya ta juya ma ta baya tare da fadin, "Wani munafurcin ne ya kawoki gida?

Murmushi Hajiya tayi tana fadin, "Aminiya ke ma dai kin san ba mai iya rabamu,Ba ma wannan ba kawo kunnanki kiji batun da na ke tafe da shi."

Ji na yi kawai suna shewa Mama na fadin, "Kai Aminiya amman kin san salon mugunta kala-kala wallahi."

Hajiya ta ce, "Ah to in anki abin da mu ke so ai ba a ki ga ni a aikace ba."

Mama ta mik'a ma ta hannu su ka tafa sannan ta ce, "Ina alfahari da ke Aminiya, yanzu zan kira Safiya in laburta ma ta komai,Kin san jiya da na fusata har na fara aikin da kai na." Hajiya ta ce, "uumm ai kawai nai shiru ne sabida nasan baku fahimci kan lamarin ba."

****************Rayuwar jin dadi mai cike da farinciki ta cigaba da wanzuwa tsakanin Faruq da Sakina sai dai kash bi ta da kullen da ake mu su na bibiyarsu ba tare da sun fahimta ba,domin kuwa Safiya faran faran ta ke da Sakina in ta gan ta kaman za ta durkusa ma ta, ta hau bayanta.

Maman Safiya da Hajiyan Faruq su na nan su na shiga da fita,su na kashe kudede amman ba chanji.

Hakan ya sa Hajiya yan ke shawarar da suje chan garin su Niger domin anan ne ta ke da tabbacin samun nasara.

Haka kuwa akayi Niger ta nufa ita da Maman Safiya.

Sai da sukai Sati fir sannan su ka dawo gida nigeria.

**********Sakina ta tashi safiyar yau jiki ba kwari gaba daya jiri ta ke ji hakan ya sa ta kiran Faruq awaya ta sanar ma sa,ya na zuwa kuwa ya dauke ta suka nufa asibiti.

Bayan likita ya yi yan gwaje-gwaje ne ya ke yi ma Faruq albishir da cewa Sakina na tare da juna biyu na wata guda.

Ba karamin farinciki Faruq yA yi ba wanda bai san lokacin da ya rungume matarsa ba.

Safiya kuwa takaici kaman ta yi, ya ya kawai dariyar yak'e ta ke, ba ta iya hakuri ba kuwa ta kira Mama ta sanar ma ta, Mama ta ce, "Karkiji komai Safiya komai da shirin maganar ciki kam kamar anyi an gama,anjima ina so kije gidan Aminiyata za mu hadu achan. Da haka su kai sallama

Shi ko Faruq ya na nan ya na lallaba abarsa kamar k'wai abin natabawa Safiya zuciya amman ta danne ba ta nunawa gudun kar shirin su ya baci.

Suna komawa kuwa Safiya tai gidan Hajiya anan ta tarar Da Mama, ba karamin bayani su Kai ma ta ba ta yadda abin na su zai tafi atsari.

Wani irin bakin abu ta bata mai sifar kunama ita kan ta sai da ta tsorata.

Mama ta ce, "ke dalla ana nema mi ki hakkin ki da mafita ke ku ma kina kawo shiririta."

Haka dai Safiya ta karba ta sa ajaka duk a tsorace.

Hajiya ta ce, "Yauwa kina ganin abun nan karkiyi wasa da shi domin bakisan mak'udan kudin da na kashe a kansa,da farko dai ki tabbatar ta yi barci sai kije dai dai kasan inda ta kwanta sai tin filon na karkashin gadon kisa Safiya karkiyi wasa in kikayi wasa wannan abn kamar rayuwarki ya ke."

Daga karshe dai atsorace Safiya ta bar gidannan.

Tana zuwa gida kuwa Faruq ya ce, "Yauwa Safiya damam kin san tun jiya ya kamata na tafi niger wajen SUBAI'ATU amman ban samuu dama ba naga jikin Sakina da sauki zan tafi Akira kanwarta ne ko ke zaki taimaka ma ta."

Da sauri Safiya ta ce, "A a ai ba komai ka bar mu kawai."

Kwata-kwata Sakina ba ta son tafiyar Faruq domin jikinta ya bata akwai abin da ke shirin Faruwa.

Ita kuuwa Safiya murna ta ke domin zatai aikin ta cikin nutsuwa.

Faruq ya ta fi.

Karfe takwas dai dai Safiya na Dakin Sakina da alama dai Sakina tai barci domin da suna yar hira ne jifa jifa.

Safiya ta tashi domin aiwatar da aikin ta.

Motsawan za tai sai ga Sakina ta......

Urs Xayyeesherth [11/08 à 00:15] Shalelen Mamata🥳🥳: *AZZAWAJUL-MUKADDAR* *الزواج المقدر*

_(Auren kaddara)_

_A True Life Story_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

______________________________________ _We Are Here To Educate,Motivate And Entertain Our Readers_ ______________________________________

_*LABARI/RUBUTAWA*_✍️ ⬇️ _*Aisha Mohammed Sani*_ _*(Xayyeesherth)*_

_Domin samun littafan mu a saukakye shiga shafukan mu kamar haka👇_

*Instagram page* _@zamani_writers_association_

*Youtube channel* _Zamani_writers_association_