AZZAWAJUL-MUKADDAR

PAGE-14

by @xayyeesherthulhumaerath

________________________________________________________

*WANNAN SHAFIN NAKINE MARYAM ABDULLAHI KANWA A GUN ANTY SAKINA🥰 KI YI YADDA KIKESO DA SHI DOMIN DA TALLAFIN KI LABARIN NAN KE TAFIYA A TSARI*

Motsa.

Tsayawa tai chak da alama barcin bai bar jikin Sakina ba hakan ya sa ta cigaba da barcinta cikin nishadi.

Safiya kuwa tu ni ta durkusa kasan Sakina ta aiwatar da aikinta.

Ta ajiye kennan kaman an mintsini Sakina ta farka ta na, "Safiya ina jin yunwa."

Ba mu su kuwa da rawar jiki Safiya ta je kicin ta dibowa Sakina abinci.

Sai da Sakina tai nak sannan Safiya ta ce, "To Sai da Safe Sakina in kina bukatar wani abu ki kirani awaya."

Sakina ta ce, "To bakomai ma zan iya insha Allah."

Safiya ta tafi dakin ta tare da farinciki fal cikin zuciya.

Washe Gari***

Tun Asuba Sakina ta fara murkususu ciwon ciki ta rasa ma ina za ta sa kan ta, ta dau waya domin kiran Safiya amman Safiya ta ki daukam wayar kuma ta na gani, chan sai ga jini ya ballewa Sakina, tun tana iya motsi har ta fita hayyacinta, kiran Safiya ta ke amman Safiya kam ko ajikinta karshen magana ma wayar na hannuun ta daga karshe ma kiran Hajiya tai ta sanar da ita da alama aikin su fa ya yi kyau.

Sakina ta rasa ina za ta sa ranta tun ta na iya daga wayar ta kira Safiya har karfin ta ya kare ba ta iya komai.

Tun Asuba a ke abu daya har karfe sha biyu na rana, Sakina ta kasa motsi ma .

Chan karfe daya saura sai ga Maryam kanwar Sakina kamar anhankadota, ta na shiga ba ta ga Sakina ba ku ma ba ta ji motsinta ba.

, "Anty Sakina ina ki ke, wai ina ki ka shiga ne." cewar Maryam

Da ta ga alamar ba mai amsa ma ta ne ta fara dube-dube tA shige cikin Dakina, abin da Maryam ta ganine ya sa ta suman tsaye.

Sakina ce kwance cikin jini ba alamar motsi ko kadan da ka gan ta kasan ta fita a haiyyacin ta.

*Rayuwa kennan ban san yaushe Sakina za ta tsallake kaddarar rayuwarta ba😭*

Da gudu Maryam ta yi dakin Safiya tana, "Anty Safiya ki zo ki taimakeni dan Allah Anty Sakina ta mutu."

Kuka kawai Maryam ta ke yi ita kuwa Safiya ta rikyeta tana muje mu gani ki bar kuka.

Azahiri ta nuna tausayinta ga halin da ta tsinci Sakina amman azuciyarta farinciki ta ke fal harda fadin, "Allah ya sa ma mutuwar tai kowa ya huta."

Da gudu Maryam ta je ta kira mai Nafe ya zo domin kai Sakina asibiti.

Safiya ta na abu kamar ba zatai ba atunanin ta Sakina in ma ba ta karasa ba gwanda ta karasa kan su isa asibiti, hakan ya sa Maryam kiran mai nafe din ya taimaka su dau Sakina.

ban da kuka ba abin da maryam ke yi har su ka isa special hospital d Ke garin bauchi.

Su na isa aka farawa Sakina taimakon gaggawa amman ina likitoci sun rasa gane kan Sakina.

Hakan ya sa Maryam ta kira su Mama da Faruq awaya domin likitocin sun bukaci ganin su.

Tuni Faruq ya hawo jirgi domin ya na ji gaba daya ya rikice ya fita hayyacin sa burin sa kawai ya gan sa gaban sahibarsa.

Mama da Baba da su Yaya Haidar kuwa tuni sun hallara a asibiti.

Faruq na isowa ba wanda ya kula illa nufar da kin likitin in da Sakina ta ke.

Ya na shiga.......

Urs Xayyeesherth [11/08 à 00:15] Shalelen Mamata🥳🥳: *AZZAWAJUL-MUKADDAR* *الزواج المقدر*

_(Auren kaddara)_

_A True Life Story_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

______________________________________ _We Are Here To Educate,Motivate And Entertain Our Readers_ ______________________________________

_*LABARI/RUBUTAWA*_✍️ ⬇️ _*Aisha Mohammed Sani*_ _*(Xayyeesherth)*_

_Domin samun littafan mu a saukakye shiga shafukan mu kamar haka👇_

*Instagram page* _@zamani_writers_association_

*Youtube channel* _Zamani_writers_association_