PAGE-16
________________________________________________________
*SADAUKARWA GA MY GRP XAYYEESHERTH FANS GRP🥰*
*YANZU BAKWA SON SHARHI, KUMA NI NAFARA GAJIYA GASKIYA DAGA WANNAN PAGE DIN IN BAKUYI BA NI ZAN AJIYE NOVEL DIN KAWAI TUNDA BAKWA SO🤷♀️*
Faruq ya ce, "Safiya ki zo mu je na maidaki gida kinga dare ya yi."
Marairaicewa tai tare da fadin, "Haba Honey ka na ganin yar uwata kwance ba lafiya ni Ina naga ta tafiya."
Faruq ya ce, "Eh Amman kin ga, ga Maman ta da Kanwarta su ne ma sukace in kaiki gida Dan yau anan ki ka hini."
Safiya za ta kara marairaicewa Faruq ya ce, "Mu he please Safiya ban son gardama na lura ki na matukar ji da yar uwar nan ta ki."
Wa ni Dadi Safiya ta ji aranta, ta tashi ta na fadin, "Tam Honey mu je Amman tare za mu kwana ko? Dan kasan ni dai bazan Iya kwana ni daya ba." Magana ta ke yi cike da kissa da kisisina wan da duk sai da ta sanyayarwa da Faruq jiki.
A kasale ya ke fadin, "Bakomai mu je ta ya ma zan bar My Princess ita daya."
Tun Safiya ta ga ta fara samun shiga ta tun ga kara shigewa Faruq da salo da ban da ban Wanda ya kara karkato da hankalinsa kan ta, har su ka isa gida.
A ranar Dai kam Faruq ya nunawa Safiya Soyayyar da bai taba nunawa gare ta ba, ya yin da ta dun ga kashe shi da Shagwaba.
Tuni ya manta da cewa wai fa Sakina na gadon asibiti, sai chan da Asuba ya farka afirgice tare da fadin, "Subhannallah! Na bar Sakina na jira na fa oh' oh kai Safiya ba ki kyauta min ba gaskiya.
Safiya ta fara kukan munafurci ta na fadin, "Ni ni me kuma nayi? Bayan kai ne.... Kawai sai ta kara fashewa da kuka.
Faruq bai San lokacin Da ya janyota jikin Sa ba tare da Fadin, " Am Sorry My Dear ki dai na kuka please bana so."
Araunane Safiya ta ce, "Umm to ba ka ce ban kyauya ma ba?"
Faruq ya yi murmushi tare da fadin, "Aa Farinciki na, bazan kara Fada ba ko in kama kunne na ne?"
Murmushi itama sannan ta ce, "A ko da na yi niyar hukunta Honeyna sunan ma da ya kirani da shi kadai ya isa ya kwace Sa."
Faruq ya ce, "Godiya na ke Farincikina yanzu dai muje mu yi sallah."
Bayan sun idar da Sallah ne Safiya ta shiga kicin domin yi ma su kayan karyawa.
Sai da ta gama tsaf Faruq ya ce, "To mu je a kaiwa su Sakina na su ko?"
Safiya ta shagwabe fuska sannan ta ce, "Ni sai na ciyar da mijina tukunna."
Ba gardama kuwa Faruq ya zauna sukai break shi da Safiya cikin nishadi ba tare da ya kara tunin Sakina ba.
A haka lokaci ya dunga ja sai kusan 9 kan su ka nufa asibiti domin kai wa Sakina Break.
Suna shiga tun da Sakina ta gan su tare kuma cikin nishadi jikinta ya yi sanyi gaba daya ta kasa kara kallon su illa sunkuyar da kan ta ds tai.
Faruq ne ya karasa gaban ta tare da rikwo hannun ta, "Am Sorry Matata abar so na, na yi lattin zuwa, mun tsaya ma ki girki ne."
Murmushi Sakina tai tare da fadin, "Bakomai mijina, ina kwana antashi lafiya?"
Faruq ya ce, "Matar so, matar kirki ke ta daban ce a kullum kara son ki na ke acikin rai na, ina lafiya fatan rabin rai na ma haka."
Sakina ta na gafe gabadaya ran ta ya yi baki ta kumburo baki tare da fadin, "Ni kan ina waje."
Ta tashi fuuuu ta fita.
Urs Xayyeesherth [11/08 à 00:16] Shalelen Mamata🥳🥳: *AZZAWAJUL-MUKADDAR* *الزواج المقدر*
_(Auren kaddara)_
_A True Life Story_
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
______________________________________ _We Are Here To Educate,Motivate And Entertain Our Readers_ ______________________________________
_*LABARI/RUBUTAWA*_✍️ ⬇️ _*Aisha Mohammed Sani*_ _*(Xayyeesherth)*_
_Domin samun littafan mu a saukakye shiga shafukan mu kamar haka👇_
*Instagram page* _@zamani_writers_association_
*Youtube channel* _Zamani_writers_association_